Connect with us

Manyan Labarai

INA MATASAN SUKE?

Published

on

Wani matashi ne dan uwanku mai matsakaitan shekaru 20 zuwa 28 yayi tsokaci akan soyayya.

Ko da yake matsahin mai suna Bashir Sharfadi na ganin matukar aka gina soyayya akan wannan bincike nasa babu shakka za’a haigi d’a mai ido.

Ga nazatin nasa:

Abubuwa Biyar (5) da Zaka/kiyi Domin Mallake Zuciyar Budurwa/Saurayinki

Na danyi Nazari kadan inda na leka sashen su Nura Nakowa domin yau na kawo muku wasu hanyoyi da mutum zaibi a matsayinsa na wayayye domin ya sace zuciyar budurwarsa ba tare da farga ba, ko kuma shi ta sace tasa.

1. Abu na farko shine dolene masoya su mayar da junansu manyan abokai mafi kusanci, matukar baka zama babban aboki ga budurwarka ba ko ki zama babban aboki ga saurayinki to babu shakka akwai sauran aiki.
Ki dauki fadin Malam Umar M. Sharif da yake cewa “Zan Rayu dake zan mutu dake, Abadan dani dani dake zamu zauna” “Idan babu ke nima ba’a ganni ba, duk inda kike nan wurin amin marhaba…” ba wai ka daukeshi a wake ba a’a ka aikata shi a aikace, ka nuna kana matukar damuwa da ita, haka kema.

2. Ka zamo mai magana daya, kada ka/ki yiwa masa/ta karya duk abinda zaka fada ya zamo gaskiya, ya zama idan kika fada masa magana to baya shakku kada ki sake ki baiwa saurayinki damar kina fada masa magana yana yin shakku akanki, ko kana fada mata tana karyataka, matukar aka samu wannan kofar to hakika babu ranar dai-daituwa.

3. Girmama Juna, ya zama kina bashi girmansa, Namiji ko yaushe shi babbane kina ce masa Ranka ya dade, Yallabai da sunayen na Musamman na girmamawa, kaikuma namiji dolene ka dinga lallabata domin ita mace kullum ’yar shagwabace tana son ka dinga nuna mata kulawa sosai.

4. Ka Fahimceta ta Fahimceka, da yawa yanzu ana samun wannan matsalar mata basu tsayawa su fahimci dabi’un samarinsu ballantana su san ta yaya zasu mu’amalancesu, haka suma mazan basu fahimceta ba balle a samu dai-daito.

Yana da kyau ki fahimci abubuwan da yake so da wanda bayaso, shima kuma ya fahimci hakan akanki, hakan zai taimaka muku wajen kaucewa samun matsala, kuma indai kikayiwa namiji hakan to ba zai taba iya rabuwa dakeba, don wallahi ko yayi wata budurwar sai ya dawo.

5. Ki dinga bashi lokaci, ba wai ko yaushe baki da lokacinsa ba, haka shima, amman kada lokacin ya dinga wuce kima, ki dinga kiransa a waya (missed call) shima ya dinga kiranki, kar kuyi wasa da ZAFAFAN KALAMAI …

6. Ki dinga sanar dashi idan zakiyi wani abun wannan zaisa shima ya dinga kula dake akai-akai.

7. Kada ki dinga yawan rokonsa, kai kuma namiji tilasne ka dinga yi mata IHSANI wato kyautatawa tunda Hausawa sunce ai Kulawama Yabawace.

8. Ke dashi ku dinga yiwa juna Uzri, sannan ku dinga baiwa juna hakuri a duk sanda daya yayiwa day aba dai-dai ba.

A karshe manazarcin yayi fatan Soyayya mai dorewa, amma ko hangensa haka ne? Duba da cewa bai ko yi auren fari ba, kai hatta soyayyar ma ba yinta yake ba

Duk da cewa al’amari na rubutu baiwa ce, amma zamu so sanin ra’ayin matasa akan nazarin sa, da kuma saanin ko an karu da hujjoji da ya wassafo.

Manyan Labarai

Kayan aikin ginin da ya ruftawa magina a Kuntau ba masu inganci ba ne – Cibiyar masu Taswirar Zane-zanen Muhalli

Published

on

Cibiyar masu tasawirar zane-zanen muhalli ta ƙasa reshen jihar kano, tayi Allah wa dai da kayan da akayi wani ginin Bene da shi mai hawa uku, da ya faɗo akan wasu magina a cikin unguwar Kuntau da ke yankin karamar hukumar Gwale a jihar kano.

Mataimakin shugaban ƙungiyar na kasa Arct Ali Mukhtar, ne ya bayyana hakan a lokacin da cibiyar takai ziyara wajen da al’amarin ya faru.

Ya ce dukkanin kayan da aka yi aikin ginin benen da su ba masu inganci ba ne.

A nasa jawabin shugaban cibiyar a nan nano Arct Bashir Hassan Hanga, kira ya yi ga gwamnatin jihar kano, da ta hana duk masu irin wannan gine-gine ba tare da sahalewar hukumar tsara birane ba wato Knupda, ta kuma ɗauki mataki akan mamallakin wannan gini da ya rushe a kan maginan.

Wakilin mu Shamsu Dau Abdullahi ya rawaito cewa dukkanin tawagar cibiyar tsara gine-ginen, sun ce za su ziyarci asibitin Murtala Muhammad, domin duba mutanen da gini ya fadowa da kuma zuwa ta’aziya gidan waɗanda suka rasu su uku.

Continue Reading

Manyan Labarai

Majalisa ta amince da dokar gwajin cutar Ƙanjamau da ta Sikila kafin aure a Kano

Published

on

Majalisar Dokokin jahar kano ta amince da dokar yin gwajin cutar kanjamau da ta Sikila da kuma sauran cututtuka kafin yin aure.

Da yake Jawabi akan kafa dokar, Shugaban Majalisar dokokin jahar kano Alhaji Jibril Isma’il Falgore, ya ce dokar za ta daƙile yaɗuwar cututtuka a tsakanin ma’aurata da yaɗa su ga iyali da ma al’umma baki ɗaya.

Har ila yau, dokar ta ba da damar yin gwajin cututtuka masu haɗari da wuyar magani kafin yin aure, tare da tanadin hukunci mai tsanani ga duk wanda yaƙi yin biyayya ga dokar.

Mataimakin Akawun Majalisar kuma babban Sakatare Alhaji Nasiru Magaji, ne ya gabatar da karatu na uku akan dokar kafin amincewa da ita a ranar Litinin.

Continue Reading

Manyan Labarai

Za’a ɗauki mataki akan duk wanda yake da hannu Gini ya ruftawa mutane a Kuntau – Ƙaramar hukumar Gwale.

Published

on

Yayin da wani ginin Bene mai hawa biyu ya danne aƙalla sama da Leburori goma a unguwar Kuntau kusa da KEDCO, a safiyar yau Juma’a, Shugaban riƙo na ƙaramar hukumar Gwale Abubakar Mu’azu Mojo, ya ce za’a ɗauki mataki akan dukkan wanda aka samu da laifi har al’amarin ya faru.

Abubakar Mu’azu Mojo, ya bayyana hakan ne yayin zantawar sa da manema labarai, yayin da ya ziyarci gurin da lamarin ya faru lokacin da ake ci gaba da aikin ceto mutanen.

Mojo, ya kuma ce babu makawa za’a ɗauki matakin doka akan duk wanda aka samu da hannu akan faruwar lamarin, kama daga ɗan kwangilar da aka bai wa aikin ginin, zuwa kuma mamallakin gidan.

Rahotanni sun bayyana cewa zuwa tsakar ranar yau aƙalla mutane bakwa aka ciro daga ƙasan ginin shida daga cikin su basa iya motsa jikin su, yayin da hukumomi suka ci gaba da gudanar da aikin ceto sauran mutanen da ginin ya danne.

Continue Reading

Trending