Connect with us

Manyan Labarai

Yadda Manhajar Whatsapp ta hada kan Sha’arai- Yan Biyun Ma’aiki

Published

on

Hassana da Usaina da akafi sani da ‘yan biyun ma’aiki’ sunyi shura a fannin yabon ma’aiki a kano, inda wakokin su suka shiga sahun wakoki na yabo da matasa ke sauraro a kasashe da harshen hausa ya yadu.Cikin shirin Gari na masoya Manzon Allah da Sayyadi Bashir Dandago ke gabatar wa a wannan tasha, matasan sun ce babu wani abu daya kawo su waje guda kamar manhajar whatsapp.Mawakan sunyi magana akan taron karawa juna sani da suke shiryawa duk shekara mai taken Da’irar Sha’iran Annabi, wanda suka shirya gudanarwa ranar lahadi 8 watan Muharram shekara ta 1441a.h, wannan dai itace shekara ta biyu da fara wannan taro da ya tattaro kan sha’irai daga sassa duniya inki ciki har da jamhuriyar Nijar.KOWANNE CIGABA SUKA SAMU A YABON ANNABI?Sun samu nasarori da suka hadar da hadin kan sha’irai, da ya haifar da karin fahimtar juna tsakanin sha’irai maza da mata.Sai wakar da suka yi yadda ta hado sha’irai sama da 100 a bangarorin biyu, mai tasiri ga kafafen yada labarai da aka yiwa lakabi da “Ga sha’iran annabi.”Wannan sune kadan daga cikin nasarori da muka samu inji yan biyun ma’aiki.Sayyadi Bashir Dandago dai ya kasance yana zakulo fitattun Sha’irai afagen yabon ma’aiki dukkanin ranakun juma’a, domin ganawa da masu sauraro har su amsa tambayoyi kan wakokin su.

Babban burin shirin na Kano Gari Na Msoya Mazon Allah a cewar mai gabatrwaar bai wuce fito da hikimomi dake kunshe cikin masana’antar yabo ba.

Manyan Labarai

Ƙarin albashin da gwamnatin tarayya ta yiwa ma’aikatan ta ci gaban mai haƙan rijiya ne – Human Rights

Published

on

Ƙungiyar kare haƙƙin ɗan adam ta Universal Declaration of Human Rights, ta ce ƙarin albashin da gwamnatin tarayya ta yiwa ma’aikatan ta, ci gaban mai haƙan rijiya ne, domin ba zai magancewa ma’aikatan matsalolin su ba.

Daraktan ƙungiyar reshen jihar Kano Alhaji Umar Sani Galadanci, ne ya bayyana hakan yayin zantawar sa da wakilinmu na ƴan Zazu Hassan Mamuda Ya’u, a yau Laraba, lokacin da yake tsokaci a kan bikin ranar ma’aikata da ake gudanarwa yau a Najeriya.

Ya kuma ce kasancewar ƙarin albashin ba zai ragewa ma’aikatan wata damuwa ba, sai dai ma ya tunzura ma’aikatan, bai kamata ƙungyoyin ƙwadago su amine da tsirarun ƙarin ba.

“Matukar gwamnatin tarayya za ta rinƙa tunzura ma’aikata da irin wannan tsirarun albashin babu makawa zamu gurfanar da ita a gaban kotu, “in ji Galadanci”.

Umar Sani ya kuma shawarci gwamnatin tarayya da ta lalubo sabbin hanyoyi da za’a ƙarawa ma’aikatan albashi mai tsoka wanda zai rinƙa magance musu wasu matsalolin su na yau da kullum.

Har ila yau, suma ƙungiyoyin ƙwadago a ƙasar nan, sun yi fatali da ƙarin albashin da gwamnatin tarayya ta yiwa ma’aikatan ta da kashi 25 cikin ɗari, da kuma kashi 35 a cikin ɗari.

Ƙungiyoyin ƙwadago da dama na NLC, da TUC, da sauran ƙungiyoyi ne suka gudanar da taron ranar ma’aikan a sassan jahohin ƙasar nan.

Continue Reading

Manyan Labarai

Kayan aikin ginin da ya ruftawa magina a Kuntau ba masu inganci ba ne – Cibiyar masu Taswirar Zane-zanen Muhalli

Published

on

Cibiyar masu tasawirar zane-zanen muhalli ta ƙasa reshen jihar kano, tayi Allah wa dai da kayan da akayi wani ginin Bene da shi mai hawa uku, da ya faɗo akan wasu magina a cikin unguwar Kuntau da ke yankin karamar hukumar Gwale a jihar kano.

Mataimakin shugaban ƙungiyar na kasa Arct Ali Mukhtar, ne ya bayyana hakan a lokacin da cibiyar takai ziyara wajen da al’amarin ya faru.

Ya ce dukkanin kayan da aka yi aikin ginin benen da su ba masu inganci ba ne.

A nasa jawabin shugaban cibiyar a nan nano Arct Bashir Hassan Hanga, kira ya yi ga gwamnatin jihar kano, da ta hana duk masu irin wannan gine-gine ba tare da sahalewar hukumar tsara birane ba wato Knupda, ta kuma ɗauki mataki akan mamallakin wannan gini da ya rushe a kan maginan.

Wakilin mu Shamsu Dau Abdullahi ya rawaito cewa dukkanin tawagar cibiyar tsara gine-ginen, sun ce za su ziyarci asibitin Murtala Muhammad, domin duba mutanen da gini ya fadowa da kuma zuwa ta’aziya gidan waɗanda suka rasu su uku.

Continue Reading

Manyan Labarai

Majalisa ta amince da dokar gwajin cutar Ƙanjamau da ta Sikila kafin aure a Kano

Published

on

Majalisar Dokokin jahar kano ta amince da dokar yin gwajin cutar kanjamau da ta Sikila da kuma sauran cututtuka kafin yin aure.

Da yake Jawabi akan kafa dokar, Shugaban Majalisar dokokin jahar kano Alhaji Jibril Isma’il Falgore, ya ce dokar za ta daƙile yaɗuwar cututtuka a tsakanin ma’aurata da yaɗa su ga iyali da ma al’umma baki ɗaya.

Har ila yau, dokar ta ba da damar yin gwajin cututtuka masu haɗari da wuyar magani kafin yin aure, tare da tanadin hukunci mai tsanani ga duk wanda yaƙi yin biyayya ga dokar.

Mataimakin Akawun Majalisar kuma babban Sakatare Alhaji Nasiru Magaji, ne ya gabatar da karatu na uku akan dokar kafin amincewa da ita a ranar Litinin.

Continue Reading

Trending