Connect with us

Labarai

Shugaban Kasa ya jaddada goyon baya ga bande

Published

on

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kai ziyarar aiki ga zababben shugaban zauren taron majalisar dinkin duniya karo na 74 Ambasada Tijjani Muhammad Bande a ofishin sa dake majlisar dinkin duniya a birnin New York na kasar Amurka.

Ziyarar wacce jim kadan bayan da shugaban kasa Muhammadu Buhari  ya kammala jawabin sa kan sauyin yanayi  gabanin fara makon babban Zauren majalisar dinkin duniya.

Wannan na kunshe cikin sanarwar da mai Magana da yawun shugaban kasa Mr, Femi Adesina ya fitar cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari na taya Ambasada Muhammad Tijjani Bande Murna kan nasarar da ya samu na zama shugaban taron zauren majalisar dinkin duniya.

Muhammadu Buhari  ya ce akwai  nauyi mai yawa akan sabon shugaban yayin da kuma na Najeriya zata cibaga da bashi goyan bayan day a dace wajen cimma nasarorin da aka sanya  gaba .

‘’ Yace a gaskiya matsayi na na shugaban kasar Najeriya ina taya yaka murna kan wannan cigaba wanda ba kai kadai ka samu ba, har ma da Najeriya.

Da yake jawabi Tijjani Muhammad Bande y ace yayi murna matuka da ziyarar da shugaban kasar ya kai masa tare tawagar sa da suka hadar da kwararru.

Muhammad Bande wanda shi ne wakili na din-din a majalisar dinkin duniya an rantsar da shi ne a ranar  17 ga wannan watan da muke ciki wanda ya sanya shi ne mutum 3 dan Najeriya day a taba rike wannan mukamin.

A wani labarin kuma babban sakatare na majalisar dinkin duniya Antonio Guterres ya nada shahararran attajirin mia kudi Aliko Dangote da shugaban bankin raya kasashen Afrika Akinwumi Adesina da sauran mutane 25 amatsayin shugabanin duniya da za su yi yaki da rashin abinci mai gina jiki.

Labarai

NAHCON ta sanya ranar fara jigilar maniyyata aikin hajjin bana zuwa Saudiyya

Published

on

Yanzu haka hukumar Aikin Hajji ta ƙasa NAHCON, ta 15 ga watan nan na Mayun 2024, a matsayin ranar da za’a fara jigilar maniyyata aikin hajjin bana, zuwa ƙasa mai tsarki.

Bayanin hakan ya fito ne ta bakin shugaban hukumar ta NAHCON, Jalal Ahmad Arabi, a wajen taron masu ruwa da tsaki kan aikin Hajji da Umrah, da ya gudana yau Alhamis birnin tarayya Abuja.

“Maniyyata kimanin 65,500 ne za su sauke Farali daga ƙasar nan a ƙasa mai tsarki; za su shafe aƙalla kwanaki huɗu domin yin ziyara a Madina kafin fara aikin Hajji, “in ji Arabi”.

Daga bisani shugaban hukumar aikin hajjin Jalal Ahmad Arabi, ya kuma bayyana cewa za ayi jigilar maniyyata aikin hajjin ne daga cibiyoyi 10 a faɗi ƙasar nan.

Continue Reading

Labarai

Gwamnatin tarayya ta ayyana gobe Laraba a matsayin ranar hutu

Published

on

Gwamnatin tarayya ta ayyana gobe Laraba, 1 ga watan Mayun 2024, a matsayin ranar hutu, domin bikin ranar ma’aikata na wannan shekara.

Ministan harkokin cikin gida, Olubunmi Tunji-Ojo, ne ya bayyana hakan, a cikin wata sanarwa da ya fitar a yau Talata.

Olubunmi, ya kuma sake nanata buƙatar ganin ma’aikata sun jajirce da yin aiki yadda ya kamata a dukkanib matakai daban-daban.

Continue Reading

Labarai

Wahalar Fetur ta haifar mana da koma baya a sana’ar mu – Mai Motar Haya

Published

on

Wani mai sana’ar tuƙin motar Haya, da kuma lodin fasinjoji mai suna Kabiru Muhammad, mazaunin ƙaramar hukumar Munjibir, ya ce ƙarancin motocin Haya da ake samu a yanzu, yana da alaƙa da wahalar man Fetur da ake fuskanta a sassan Najeriya.

A zantawar mutumin da wakilinmu Yusuf Nadabo Isma’il, ta cikin shirin rahotanni daga ƴan Zazu na yau Talata, ya ce a baya har motoci hamsin suke yiwa lodin fasinjoji su tashi, amma a yanzu Mota ɗaya suke iya cikawa sakamakon ƙarancin Fetur da ake fama da shi.

Ya kuma ce ƙaranci tare da tsadar man fetur ɗin da ake fama da shi, sun haddasa musu koma baya a sana’ar su, baya ga batun kuma matsalar da suke fuskanta da fasinjoji wajen biyan kuɗin Mota.

Wakiliyarmu da ta bibiyi shirin na ƴan Zazu Ummi Bala Ahmad ta rawaito cewa, matuƙin motar Kabiru Muhammad, ya kuma yi kira ga gwamnatin tarayya da ta jahohi, da su yi abinda ya kamata dan ganin farashin man Fetur ɗin ya sauka, domin al’umma su samun sauƙi.

Continue Reading

Trending