Connect with us

Manyan Labarai

EU zata tallafawa Najeriya da fiye da Euro miliyan 150

Published

on

Kungiyar tarayyar Turai ta ware fiye da Euro miliyan dari da hamsin domin tallafawa Najeriya wajen inganta  sauyin yanayi

Jakadan kungiyar tarayyar Turai Ketil Karlsen ne ya bayyana haka yayin wani taron sauyin yanayi da aka gudanar a jami’ar Bayero ta Kano da hadin gwiwar kungiyar tarayyar Turai.

Jakadan kungiyar tarayyar Turai Ketil Karslen ya ce lokaci yayi da za’a dara daga kan turban samar da tsare-tsare zuwa ga aiwatar da su, inda yake cewa a yanzu kungiyar ta tarayyar Turai zata fi maida hankali ne wajen aiwatar da tsare-tsare da aka riga aka fito da su a aikace.

Ya ce yana da matukar muhimmanci yin hubbasa wajen inganta shirye-shiryen muhalli musammam matalolin da suka dangance sauyin yanayi da amfani da makamashi,ta hanyar amfani da wasu daga cikin abubuwa da ake amfani da su kamar su kashin shanu, shara dangogin tukkan rake,shara kamar na su takardu da sauransu wajen samar da makamashin da ba zai gurbata muhalli ba.

Ya kuma ce kungiyar tarayyar turai zata taimaka wa Najeriya wajen samar da kaidoji da hanyoyin magance matsalar sauyin yanayi, inda yake cewa Najeriya na daya daga cikin kasashen da suke fama da wannan matsala ta sauyin yanayi, tare da cewa ita ce kasar da ta fi kowacce girma a nahiyar Afrika.

Tuni kungiyar tarayyar EU ta fitar da kudi Euro miliyan 150  kan matsalolin sauyin yanayi da hanyoyin amfani da yanayi na hasken rana, da saura makamashin da muke samarwa a harkokin yau da kullum domin samar da makamashin da baya cutarwa ga yanayi mu

Tare da magance matsaloli na noma, kwarowar Hamada da samar da hasken lantarki.

Ketil ya ce a nan da sheraka ta 2030 akwai bukatar  ganin ruwan sha ya wadata a  Najeriya baki daya a wani yunkurin taimaka mata kamar yadda yake a kundin tsarin majalisar dinkin duniya na kasashen da suka cigaba su taimakawa kasashe masu tasowa wajen samar da wasu ababa more rayuwa.

Ko a nan Kano kungiyar ta EU na yunkurin samar da kudirori da tabbatar da irin wadanan matsaloli da ke adabar jihar mussamam matsala ta bahaya a bainar jama’a ,tsaftace muhalli da kawar da kwarorwar Hamada na daga cikin tsare-tsarensu.

Ya kuma ja hankali yan jihar Kano da su sani cewar babu wata al’umma da take cigaba face sai da zaman lafiya, sannan ya yaba da yadda al’ummar  jihar Kano ke kokarin tabbatar da zaman lafiya, hakan ce ma ta sa ba’a samu barkewar rikce-rikce kamar yadda ake samu a Arewa maso gabashin Najeriya.

 

 

Manyan Labarai

Ƙarin albashin da gwamnatin tarayya ta yiwa ma’aikatan ta ci gaban mai haƙan rijiya ne – Human Rights

Published

on

Ƙungiyar kare haƙƙin ɗan adam ta Universal Declaration of Human Rights, ta ce ƙarin albashin da gwamnatin tarayya ta yiwa ma’aikatan ta, ci gaban mai haƙan rijiya ne, domin ba zai magancewa ma’aikatan matsalolin su ba.

Daraktan ƙungiyar reshen jihar Kano Alhaji Umar Sani Galadanci, ne ya bayyana hakan yayin zantawar sa da wakilinmu na ƴan Zazu Hassan Mamuda Ya’u, a yau Laraba, lokacin da yake tsokaci a kan bikin ranar ma’aikata da ake gudanarwa yau a Najeriya.

Ya kuma ce kasancewar ƙarin albashin ba zai ragewa ma’aikatan wata damuwa ba, sai dai ma ya tunzura ma’aikatan, bai kamata ƙungyoyin ƙwadago su amine da tsirarun ƙarin ba.

“Matukar gwamnatin tarayya za ta rinƙa tunzura ma’aikata da irin wannan tsirarun albashin babu makawa zamu gurfanar da ita a gaban kotu, “in ji Galadanci”.

Umar Sani ya kuma shawarci gwamnatin tarayya da ta lalubo sabbin hanyoyi da za’a ƙarawa ma’aikatan albashi mai tsoka wanda zai rinƙa magance musu wasu matsalolin su na yau da kullum.

Har ila yau, suma ƙungiyoyin ƙwadago a ƙasar nan, sun yi fatali da ƙarin albashin da gwamnatin tarayya ta yiwa ma’aikatan ta da kashi 25 cikin ɗari, da kuma kashi 35 a cikin ɗari.

Ƙungiyoyin ƙwadago da dama na NLC, da TUC, da sauran ƙungiyoyi ne suka gudanar da taron ranar ma’aikan a sassan jahohin ƙasar nan.

Continue Reading

Manyan Labarai

Kayan aikin ginin da ya ruftawa magina a Kuntau ba masu inganci ba ne – Cibiyar masu Taswirar Zane-zanen Muhalli

Published

on

Cibiyar masu tasawirar zane-zanen muhalli ta ƙasa reshen jihar kano, tayi Allah wa dai da kayan da akayi wani ginin Bene da shi mai hawa uku, da ya faɗo akan wasu magina a cikin unguwar Kuntau da ke yankin karamar hukumar Gwale a jihar kano.

Mataimakin shugaban ƙungiyar na kasa Arct Ali Mukhtar, ne ya bayyana hakan a lokacin da cibiyar takai ziyara wajen da al’amarin ya faru.

Ya ce dukkanin kayan da aka yi aikin ginin benen da su ba masu inganci ba ne.

A nasa jawabin shugaban cibiyar a nan nano Arct Bashir Hassan Hanga, kira ya yi ga gwamnatin jihar kano, da ta hana duk masu irin wannan gine-gine ba tare da sahalewar hukumar tsara birane ba wato Knupda, ta kuma ɗauki mataki akan mamallakin wannan gini da ya rushe a kan maginan.

Wakilin mu Shamsu Dau Abdullahi ya rawaito cewa dukkanin tawagar cibiyar tsara gine-ginen, sun ce za su ziyarci asibitin Murtala Muhammad, domin duba mutanen da gini ya fadowa da kuma zuwa ta’aziya gidan waɗanda suka rasu su uku.

Continue Reading

Manyan Labarai

Majalisa ta amince da dokar gwajin cutar Ƙanjamau da ta Sikila kafin aure a Kano

Published

on

Majalisar Dokokin jahar kano ta amince da dokar yin gwajin cutar kanjamau da ta Sikila da kuma sauran cututtuka kafin yin aure.

Da yake Jawabi akan kafa dokar, Shugaban Majalisar dokokin jahar kano Alhaji Jibril Isma’il Falgore, ya ce dokar za ta daƙile yaɗuwar cututtuka a tsakanin ma’aurata da yaɗa su ga iyali da ma al’umma baki ɗaya.

Har ila yau, dokar ta ba da damar yin gwajin cututtuka masu haɗari da wuyar magani kafin yin aure, tare da tanadin hukunci mai tsanani ga duk wanda yaƙi yin biyayya ga dokar.

Mataimakin Akawun Majalisar kuma babban Sakatare Alhaji Nasiru Magaji, ne ya gabatar da karatu na uku akan dokar kafin amincewa da ita a ranar Litinin.

Continue Reading

Trending