Connect with us

Labarai

Kotu ta tsayar da ranar raba gardama tsakanin Ganduje da Abba

Published

on

Kotun sauraron kararrakin zaben gwamnan jihar Kano ta zabi ranar Laraba, 2 ga watan Oktoba 2019 domin yanke hukunci kan shari’ar da jam’iyyar PDP da dan takararta Abba Kabir Yusuf suka shigar kan gwamna Abdullahi Umar Ganduje na kalubalantar sakamakon zaben 9 ga Maris 2019.

Kotun ta ayyana ranar ce ta hanyar aikewa dukkanin jami’un biyu sako ta wayar salula wanda sataren kotun ya aike musu.

Jaridar Daily Nigerian ta ruwaito cewa a ranar 18 ga watan Satumba ne hukumar INEC da jam’iyyar  APC, da kuma Ganduje suka kammala muhawara da lauyoyin PDP da Abba Kabir Yusuf.

Halima S. Muhammad wacce itace take jagorantar shari’ar ta ce kotun tana sane da adadin wa’adin kwanakin da aka ware mata na kwanaki 180, kamar yadda yake a cikin kundin tsarin hukumar INEC.

Lauyan INEC, Ahmed Raji SAN, yayin fashin baki kan al’amarin inda ya ce an baiwa jam’iyyar PDP da Abba Kabir damar bayyana sahihan takardun shaida a kotu amma yawancin takardun shaidun ba sahihai bane, saboda haka, ya bukaci kotu tayi watsi da karar.

A jawabin lauyan gwamnan, Offiong Offiong (SAN), ya ce jam’iyyar PDP ta gaza gabatar da sakamakon da ta tattara da kanta amma ta dogara kan sakamakon da hukumar INEC ta sanar, saboda haka, kotu tayi watsi da karar.

A bangaren lauyan APC kuwa, Alex Izinyon SAN, ya ce jam’iyyar PDP da Abba Kabir sun yi zargin cewa an saba doka wajen soke sakamakon zaben akwatunan zabe 207 amma basu gabatar da hujjoji akai ba. Saboda haka, ya bukaci kotu tayi watsi da karar.

Amma a bangaren lauyan PDP da Abba, Kanu Agabi SAN, ya ce babbar hujjarsu itace Abba Kabir ne ya lashe zaben zagayen farko a ranar 9 ga Maris 2019.

 

Labarai

Mahukunta ku kawo mana ɗauki a masallacin garin mu – Mazauna garin Ɗan-Dalama

Published

on

Al’ummar garin Ɗan-Dalama da ke ƙaramar hukumar Dawakin Tofa a jihar Kano, sun koka tare da neman ɗaukin mahukunta kan yadda katangar masallacin Juma’a na garin ta lalace, lamarin da hakan ke barazanar faɗuwar katangar.

Shugaban kwamitin masallacin juma’ar na garin Ɗan Dalama, Mallam Muhammad Mai Nama, ne ya magantu kan al’amarin, inda ya kuma yi kira ga al’umma ciki har da Attajirin ɗan kasuwar nan Alhaji Alhassan Aminu Ɗan Tata, da su kawo musu ɗauki domin gyara katangar masallacin na Ɗan Dalama, bisa yadda take neman faɗuwa.

Ya kuma ƙara da cewa ba iya katangar ce ke barazanar faɗuwar ba, haka ma cikin masallacin ba a cewa komai, duk kuwa da ƴan kwamitin sun yi bakin ƙokarin su, amma dai kawo yanzu akwai gyare-gyaren da ya ke buƙata.

Continue Reading

Labarai

Ba za’a iya wadata mutane da Fetur ba idan gwamnati ba ta sa hannu ba – Bashir Ɗan Mallam

Published

on

Yayin da ake ci gaba da fuskantar tsadar man fetur a ƙasar nan, shugaban kungiyar Dillalan Man fetur da Iskar Gas, ta ƙasa Bashir Ahmad Ɗan malam, ya ce koda kuwa matatar Mai ta Dangote za ta yi ƙarfi ka’in da na’in, ba lallai ne a samu saukin Man fetur ba a ƙasa, matuƙar gwamnatin tarayya bata sa hannu ba.

Bashir Ɗan Malam ya bayyana hakan ne yayin ganawarsa da gidan rediyon Dala FM, da safiyar yau Juma’ar.

Ɗan Mallam ya kuma ce sakamakon yadda gwamnati take taimakawa a fagen shan man, hakan yasa idan har bata sanya hannu ba za’a rinƙa shan wahala wajen samun man fetur ɗin a ƙasa.

Wannan dai na zuwa ne yayin da al’umma ke ci gaba da fuskantar ƙalubalen tsadar man fetur, lamarin da ya sa ake siyar da kowacce lita sama da Naira 800 a jihar Kano, inda ake ci gaba da fuskantar manyan layuka a gidajen man da dama.

Continue Reading

Labarai

Zamu yi aiki kafaɗa da kafaɗa da ƴan Jarida – Hukumar Zaɓe ta Kano

Published

on

Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta jihar Kano KANSEC, ta sha alwashin aiki kafaɗa-kafaɗa da ma’aikatan Jarida, musamman ma da zaɓen ƙananan hukumomin jihar nan 44 da ke tafe.

Sabon shugaban hukumar Farfesa Sani Lawan Manumfashi, ne ya bayyana hakan, yayin ziyarar da tawagar ƙuniyar matasan ƴan Jarida, ta Kano Youth Journalist Forum, suka kai masa a ofishin sa yau Alhamis, yayin da ya shafe kwanaki huɗu da kama aiki.

Ya kuma ce, za su yi aiki da ma’aikatan Jarida musamman ma yayin gudanar da ayyukan zaɓen ƙananan hukumomin Kano 44, da ke tafe, domin wayar da kan al’umma da ma samun nasara yayin zaɓen da ma bayan sa.

Farfesa Manumfashi, ya kuma ƙar da cewa, akwai buƙatar kowa ya bayar da tasa gudummawar a harkar zaɓe, domin kuwa yanzu haka suna ci gaba da aiki wajen shirya zaɓen ƙananan hukumomin.

Da yake nasa jawabin shugaban ƙungiyar matasa ƴan Jaridar ta jihar Kano Musa Zangina Adam, ya ce sun kai ziyarar ne, domin su ƙulla alaƙar aiki a tsakanin su da hukumar, bisa yadda kowanne ɓangare yake buƙatar juna, tare kuma da bayar da gudunmawar da ya kamata.

Zangina, ya kuma ce a shirye ƙungiyar su take wajen ci gaba da bibiyar al’amuran da suka shafi al’umma, tare da nusar da mahukunta dan ganin an wadata su da kayayyakin more rayuwa.

Continue Reading

Trending