Connect with us

Addini

Kai Tsaye: Yadda zikirin shekara yake gudana a fadar sarkin Kano

Published

on

07:19pm

Wakilin mu Abba Ibrahim Lafazee da a yanzu haka yake fadar ta maimartaba sarkin Kano, ya rawaito mana cewa a jawabin Sheikh Dahiru Usman Bauchi ya maida hankali kan riko da salatin Annabi (s.a.w) domin kuwa shine mafita ga al’ummar musulmi, a don haka yayi kira ga al’ummar musulmi da su kara maida hankali wajen yiwa Annabi (s.a.w) salati.

06:45pm

Zikirin shekara dai taron addu’a ne da mabiya darikar Tijjaniyya suke gabatarwa kowace shekara, domin addu’o’in zaman lafiya da cigaba ga al’ummar musulmai, wanda ake yi a fadar maimartaba sarkin Kano.

Taron ya samo asali ne a shekarar 1999AD, lokacin da gwamnatin jihar Kano ta waccan lokacin karkashin gwamna Rabi’u Musa Kwankwaso ta shirya bikin cikar garin Kano shekaru dubu (1000) da kafuwa.

A kan haka ne masarautar Kano karkashin Maimartaba Alhaji. Dakta Ado Bayero a wancan lokaci ta shirya zikiri da addu’o’in ranar jumu’a, wanda ake gudanarwa har izuwa yanzu.

A shekarar ta 1999AD dai ta dace da shekara 100 cif da shigar darikar ta tijjaniyya masarautar Kano.

Mabiya darikar tijjaniyya daga sassa daban-daban na ciki da wajen kasar nan na halartar taron.

Tun bayan hawan maimartaba Sarkin Kano Mallam Muhammadu Sanusi II na biyu dai ya kawo sabon tsari na gabatar da addu’ar neman zaman lafiya wadda ake gabatarwa a kowacce jumu’a da safe a babban masallacin jumu’a na garin Kano.

A yau jumu’a 04 ga watan Oktoba ne dai ake gudanar da taron na bana, wanda ya samu halartar dubunnan al’umma da dama ciki harda Maimartaba Sarkin Kano Mallam Muhammadu Sanusi II, Sheikh Dahiru Usman Bauchi, Gwamna Nasir El-rufa’I na jihar Kaduna, ‘ya’yan Sheikh Ibrahim Inyass da kuma mataimakin Gwamnan jihar Kano Dakta Nasiru Yusuf Gawuna.

Ku cigaba da bibiyar wannan shafi zamu rika sabunta muku hakikanin abinda yake faruwa a wurin taron kai tsaye.

Addini

Matsin Rayuwa: Shugabanni ku sassautawa al’umma – Babban Limamin Kano

Published

on

Babban limamin Kano, kuma wanda ya jagoranci sallar idi a babban masallacin idin na Kofar Mata a nan Kano, Farfesa Muhammed Sani Zaharaddin, ya ja hankalin shugabanni da su sassautawa al’umma, sakamakon halin matsin rayuwar da ake ciki a yanzu.

Farfesa Muhammed Sani Zaharaddin, yayi jan hankalin ne yayin huɗubar da ya gabatar, bayan kammala sallar idi da ta gudana a yau Laraba, a babban masallacin idin dake unguwar Kofar Mata a Kano.

Ya kara da cewa kasancewar al’umma na cikin mawuyacin hali da kuncin rayuwa, akwai buƙatar shugabanni su yi bakin ƙoƙarin su, domin kawo sauki daga halin matsin halin rayuwar da ake fama dashi.

Yayin sallar Idin gwamnan Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf, da mataimakin sa Kwamared Aminu Abdulsalam Gwarzo, da sauran al’umma da dama ne suka halarta.

Wakilinmu na fadar gwamnatin Kano Abba Haruna Idris ya rawaito cewa, Farfesa Muhammed Sani ya kuma ja hankalin al’umma, da su koma ga Allah Subhanahu wata’ala domin samun dacewa a Duniya da gobe Ƙiyama.

Continue Reading

Addini

Ku fara duban watan Sallah daga gobe Litinin – Fadar Sarkin Musulmi

Published

on

Yanzu haka kwamitin ganin wata na Fadar mai alfarma sarkin Musulmi Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III, ya buƙaci al’ummar musulmin ƙasar nan da su fara duban jinjirin watan Shawwal, daga gobe Litinin, 8 ga watan Afrilun, 2024 da ake ciki.

Bayanin hakan na ƙunshe ne ta cikin wata sanarwa da kwamitin ya fitar a yammacin yau Lahadi a jihar Sokoto.

Sanarwar ta ce, duk wanda ya ga watan Shawwal, ya sanarwa Mai Gari ko Hakimi mafi kusa wanda kuma zai sanar har zuwa fadar Sarkin Musulmi.

Har ila yau, fadar Sarkin musulmin ta kuma bayar da lambobin waya waɗanda mutane za su yi amfani da su wajen ba da rahoton ganin watan Sallah ga fadar Sarkin musulmin, kamar yadda kafar yaɗa labarai ta BBC ta rawaito.

Continue Reading

Addini

Iyaye ku kula da tarbiyyar ƴaƴan ku – Malama Fatima Tsakuwa

Published

on

Malamar addinin musulunci dake nan Kano Malama Fatima Ahmad Tsakuwa, ta shawarci mata da su ƙara himma wajen kula da tarbiyyar ƴaƴansu, tare da kuma zaburar da su mahimmancin yin addu’a a cikin wannan wata na Ramadana, domin rabauta da rahamar Ubangiji S.W.T.

Malama Fatima Ahmad Tsakuwa, ta bayyana hakan ne yayin taron bita ta musamman da gidauniyar Bango Charity Foundation ƙarƙashin Malama Fatima Yusif Mai tama, wanda gidauniyar ta shirya wa Mata, da bitar ta shafi watan Azumin Ramadana, akan yadda iyaye matan za su kula da ƴaƴan su, da ya gudana a ofishin ƙungiyar dake unguwar Sharaɗa a Kano.

Wakiliyar tashar Dala FM Kano, ta rawaito cewa malama Fatima Tsakuwa ta ce akwai buƙatar iyayen su ƙara lura da tarbiyyar ƴaƴansu, tare da yawaita karatun Al-kur’ani mai girma domin rabauta da falala a wajen Allah S.W.T.

Continue Reading

Trending