Connect with us

Labarai

Ana sa ran shugaban kasa zai gabatar da kasafin kudin badi

Published

on

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jagoranci majalisar zartarwa domin tattauna muhimman batutuwa da rahotanni suka nuna cewa suna da alaka da kasafin kudi da shugaban zai mikawa zauren majalisun dokokin kasar nan kudirin kasafin kudin badi, domin bayyana musu yadda kasafin kudin shekarar 2020 zai kasance.

A makon daya gabata ne dai shugaba Buhari ya aika da wasika ga majalisar dattawa, kan kasafin kudin da ake sa ran cewar zai lakume kimanin tiriliyan 10.

A jiya ne shugaba Buhari ya kaddamar da taron tallalin arziki karo na 25 wanda zai kalubalanci shugabannin hukumomin gwamnati da kuma masu zaman kansu,domin fitar da Najeriya  daga halin matsin tattalin arzikin da take ciki da kuma tabbatar da tsarin cigaba mai dorewa.

Zaman dai ya samu halartar mataimakin shugaban kasa farfesa Yemi Osibanjo da sakataren gwamnatin tarayya Boss Mustapha, sai kuma shugaban ma’aikatan fadar gwamnatin Abba Kyari da shugaban ma’aikatan gwamnatin tarayya Folasade Yemi Esan da kuma daukacin ministoci baki daya.

Rahotanni sun bayyana cewa ministan sufuri Hadi Sirika ya gabatar da jawabi na musamman a yayin zaman da shugaban kasa ya jagoranta.

 

Labarai

Zamu magance ƙalubalen da ake samu a fannin ilimi mai zurfi – Gwamnatin Kano

Published

on

Gwamnatin jahar kano ta sha alwashin mangance dukkanin wani ƙalubale a fannin ilimi mai zurfi a fadin jihar Kano.

Kwamishinan ilimi mai zurfi Dakta Ibrahim Yusif kofar mata, ne ya
bayyana hakan a yayin taron yaye daliban kwalejin ilimi ta Aminu
Kano (AKCOE), da ya gudana a ranar Alhamis.

Y kuma ce yanzu haka tattaunawa tayi nisa a hukumance akan bukatar kwalejin dan ganin ta samu wadataccenf ilin da za ta gina jami’a.

Dakta Ibrahim kofar mata ya bayyana gamsuwa da tsarin da kwalejin take bi wajen gudanar da karatu, inda ya kuma ja hankalin dalibai 40 da suka karbi shaidar kammala karatun NCE,
da su zama ababen koyi.

Da yake nasa jawabin shugaban kwalejin Dr. Ayuba Ahmad Muhammad, ya ce da zarar sun shiga sabon tsari za su fara da daukar dalibai yan asalin jahar Kano mutum dubu daya kyauta, tare da biyawa ‘yan makarantar
kudi sama da Naira miliyan 300 yan asalin jahar kano dan
karfafawa matasa gwiwa.

Wakilinmu Yusif Nadabo Isma’il ya rawaito cewa al’umma da dama ne suka samu damar halartar taron daga guraren daban-daban na jihar Kano, da ma ƙasa baki ɗaya.

Continue Reading

Labarai

Bama jin daɗin yadda wasu iyaye suke hana ƴaƴan su maza auren mu – Budurwa mai larurar Ƙafa

Published

on

Wata matashiyar budurwa mai buƙata ta musamman dake da lalurar Ƙafa Samira Ahmad Tijjani, ta nuna rashin jin daɗin ta, bisa yadda mafi yawan iyaye suke nunawa masu lalurar ƙyama, wajen hana ƴaƴan su auren masu lalurar ƙafar lamarin da yasa al’amarin ke matuƙar ɓata musu rai.

A zantawar wakilinmu na ƴan Zazu Hassan Mamuda Ya’u, da budurwar ta ce, mafi yawancin su mata masu lalurar ƙafar sun ma fi mata masu lafiya iya Girki, da sauran ayyukan yau da kullum.

Ta ci gaba da cewa, “Amma abin takaici sai a rinƙa nuna mana ƙyama, ko kuma wariya musamman ma wajen neman aure, bayan kuma ba mu muka yiwa kan mu halitta ba, “in ji Samira”.

Ta kuma ce abinda wasu daga cikin iyaye suke yi musu kan nuna ƴaƴan su ba za su aure mai lalurar Kafa ba, basa jin daɗin hakan, shi yasa ma ta fito domin ta sanarwa al’umma domin gujewa hakan.

A cewar ta, “Ko nima nayi soyayya mara misaltuwa da samari masu lafiyar Ƙafa, amma mahaifiyar ɗaya daga cikin su ta ce ita ba wai bata sona ba, amma tana jin kunyar ta tuna ni a cikin mutane cewar a zummar matar ɗan ta”.

Daga bisani dai ta yi kira ga al’umma da su dai na nuna ƙyamar ko kuma nuna wariya a gare su, bisa yadda iyayen su suke matuƙar shiga cikin damuwa a duk lokacin da aka nuna musu wariyar.

Continue Reading

Labarai

Bayan ƙaddamar da tallafi: Zamu rinƙa raba tallafin jarin Naira dubu 50,000 ga iyaye Mata duk wata – Gwamnan Kano

Published

on

Gwamnatin jihar kano ta kaddamar da rabon taffin kuɗaɗe ga iyaye mata dake kananan hukumoni 44 su 5,200 a fadin jihar nan, domin su dogara da kan su.

Gwamnan kano Injiniya Abba Kabir Yusif, ne ya jagoranci ƙaddamar da rabon tallafin kudaɗen har Naira 50,000 ga iyaye mata dake kananan hukomini 44 a yau Talata, wanda ya gudana a ɗakin taro na Coronation Hall da ke gidan gwamnatin kano.

Abba Kabir Yusif ya kuma ce hakan na daga cikin alkawarin da suka yiwa matam tun a lokacin yaƙin neman zaben shekarar 2023 da ta gabata, inda ya ce iyaye mata na da bukatar jari domin dogaro da kan su, musamman ma wajen yin sana’o’i irin su Kosai, Awara, Gurasa da Bandasho da dai sauran ƙananan sana’o’i.

Aƙalla dai Mata ɗari-ɗari ne 100, za su amfana daga kananan hukumomi 36 na Karkara, da kuma na cikin birni takwas 8, kuma iyaye mata dari biyu-biyu (200) za su amfana da tallafin duka dai domin su dogaro da kan su.

Wakilinmu Abba Haruna Idris ya rawaito cewa Gwamnan Kano Abba Kabir, ya ƙara da cewa wannan ba shine na karshe ba, za su rinƙa tallafawara duk wata-wata, domin samawa iyaye mata sana’oin dogaro da kai, ta yadda zasu rinƙa haɓɓaka tattalin arzikin jihar kano.

Continue Reading

Trending