Connect with us

Nishadi

Dalilin cafke Sadiya Haruna

Published

on

Dalilin cafke Sadiya Haruna

Rundunar ‘yansanda ta jihar Kano ta tabbatar da cafke shahararriyar jarumar nan ta soshiyal midiya wato Sadiya Haruna, biyo bayan wani sabon rikici da ya barke a masana’antar shirya fina-finan hausa ta Kannywood.

Kakakin rundunar ‘yansandan jihar Kano DSP. Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya tabbatarwa da Dala FM cewa ‘yansanda sun kama Sadiyan bayan korafin da wani jarumin fina-finan Hausa mai suna Isa I. Isa yayi, na zargin ta ci zarafinsa da kuma bata masa suna.
DSP. Kiyawa ya bayyana cewa suna cigaba da bincike akai domin gurfanar da wanda aka samu da laifi a gaban kotu.

Idan baku manta ba dai Sadiya Haruna ta fitar da wasu bidiyo ta dandalin sada zumunta na Instagram wanda take kalubalantar jarumin Isa I. Isa da aikata wasu laifuka.

Dalilin cafke Sadiya Haruna

Hoto Sadiya Haruna da jarumi Isa I. Isa

Sai dai shi ma a nasa bangaren jarumin ya fitar da wani bidiyo da ya nemi afuwar jama’a, kan wani laifi da yayi ikrarin ya aikata, amma daga bisani ya goge shi.

Haka ma dai ita ma Sadiyan izuwa yanzu ta goge bayanan da ta wallafa a shafin nata game da Isan.

Allah ya kyauta.

Rubutu mai alaka:

Mutum guda na rasa ransa  cikin sakan 40

Za mu yi amfani da kudin VAT wajen bunkasa Ilimi.

Nishadi

Abinda ya sa Deezell ya maka Maryam Booth a Kotu

Published

on

Mawakin Hip Hop dinnan Ibrahim Ahmad Rufa’I wanda aka fi sani da Deezell ya maka fitacciyar jarumar fina-finan Hausar nan Maryam Booth a gaban kotu.

Cikin wata takardar shigar da kara da mawakin ya wallafa a shafin sa na Twitter ta nuna cewa ya shigar da karar Maryam Booth da wasu mutane biyar a gaban kotu bias zargin yi masa batanci.

Tunda farko dai Jaruma Maryam Booth ta zargi mawakin wanda tsohon saurayin ta ne, da cewa shi ne ya dauki wani bidiyon ta tsirara a lokacin da ta fito daga bandaki, sannan ya fitar da shi aka rika yadawa a kafafan sada zumun ta.

Sai dai mawaki Deezell ya musanta zargin inda ya ce ba shine ya saki wannan bidiyon ba, sannan ya nemi da ta janye zargin da tayi masa ko kuma ya gurfanar da ita a gaban kotu.

Cikin takardar shigar da karar dai ta nuna cewa Ibrahim Ahmad Rufa’I yana neman diyyar zunzurutun kudi har miliyan goma.

Duk da cewa har izuwa wannan lokaci Deezell bai fito ya karyata zargin Maryam na cewa shi ne ya dauki bidiyon ba, sai dai kawai ya musanta sakin bidiyon ga al’umma.

Deezell ya wallafa cewa yanzu haka kotu ta baiwa ‘yan sansa umarnin cigaba da bincike kan al’amarin kafin haduwa a gaban kotu.

(more…)

Continue Reading

Nishadi

Anyi shagalin bikin jaruma Maryam Ceeter

Published

on

A ranar jumu’ar da ta gabata ne aka daura auren fitacciyar Jarumar fina-finan Hausar nan Maryam Isah Ceeter, a masallacin jumu’a na Alfurkan dake nan Kano.

Jaruma Maryam Ceeter ta wallafa hotunan bikin a shafin ta na Facebook inda masoyanta suka rika yi mata sakon fatan alkhairi.


Continue Reading

Nishadi

Fadakarwa muke a fina-finan mu -Furodusa

Published

on

Shahararren mai shirya fina-finan Hausar nan Sani Ali Abubakar Indomie ya bayyana cewa wa’azi da fadakarwa sune ayyukan da suke yi a fina-finan Hausa da suke gabatarwa.

Yayin wata zantawa da jarumin yayi da Dala FM kan sabon shirin sa na “Karamin Sani” Indomie ya ce manufar yin fina-finan sa, shi ne don fadakarwa da wayar da kan al’ummar mu, a don haka ya ke maida hankali wajen ganin fina-finan sa sun dace da addinin islama.

Kazalika Indomie ya ce al’umma na nuna gamsuwarsu kan fina-finan da yake yi ba tare da waka ko kida ba, domin dai su dace dai-dai da addini.

Wasu al’umma dai na ganin cewa fina-finan Hausa na wannan zamanin ko kadan sun sha bam-bam da al’ada da addinin malam Bahaushe.

Sai dai wasu na ganin cewa wannan hobbasa da su Sani Ali Abubakar Indomie keyi zai bada gudummuwa matuka wajen kara farfadowa da martabar masana’antar shirya fina-finan Hausa.

Continue Reading

Trending

error: Content is protected !!