Nishadi
Mansura Isah ta yi kaca-kaca da Sadiya Haruna

Fitacciyar jaruma kuma mai shirya fina-finai a masana’antar Kannywood Mansura Isah ta nuna takaicin ta kan abinda ya faru tsakanin Sadiya Haruna da kuma jarumi Isah A. Isah.
A kwanakin baya dai an hangi Mansura Isah tare da Sadiyar a cenima cikin raha da annashuwa.
Sai dai a wannan rigimar da ta faru tsakanin Isah da sadiya, Mansurar ta nuna rashin jin dadinta.
Har ma ta wallafa wani rubutu da turanci a shafinta na instagram cewa “Sadiya Haruna ba zan iya sanya hotonki koda a shafina ba, domin naji kunyar abin da kika aikata.
Sannan ta kara da cewa “ Subhanallahi! Sadiya ba na tausayin ki ko kadan wallahi ban damu dake ba, domin kin yankewa kanki rayuwar da kike so da halin da kike so ki tsinci kanki, damuwa ta daya ce yaranki a wadanda za ki haifa nan gaba.
Duk abinda mukayi yana nan a social media har abada ko da kuwa kin goge abinda kika wallafa
Ba zance ba zaki samu mijin aure ba domin akwai masu Imani, amma kiyi tunanin zagin da za’a yiwa yaranki idan sunyi fada ada mutane za’a tuna musu abinda mamansu tayi lokacin tana budurwa.
Na san Allah ne mai shiyarwa kuma za ki iya shiryuwa amma kiyi tunani kalubalen da iyalinki da ‘ya’yanki za su fuskanta.
Mansura Isah dai ta yi dogon bayani game da wannan rikici daya faru tsakanin jaruman biyu.
Tuni dai ‘yansanda suka bada belin Sadiya Haruna kuna suna cigaba da bincike.

Kannywood
Hukumar tace finafinai ta dage dakatarwar da ta yiwa wasu finafinai

Hukumar tace finafinai ta jihar Kano ta amince da tsawaita wa’adin dakatar da nuna wasu manyan fina-finai masu dogon zango 22.
Tun da farko hukumar ta sanar da dakatar da nuna finafinan ne sakamakon zarginsu da saɓa ƙa’idar hukumar, sannan ta ba masu finafinan mako ɗaya su cika ƙa’idojin hukumar.
Sai dai a wata sanarwa da shugaban Haɗaɗɗiyar Ƙungiyar Masu Shirya Finafinai ta Najeriya (MOPPAN) reshen jihar Kano, Ado Ahmad Gidan Dabino, ya ce an tattauna, kuma an fara samun masalaha.
“Bayan doguwar tattaunawa da shugaban hukumar, Abba Al-Mustapha da wasu ma’aikatansa da wakilan Kannywood, an samu matsaya a kan:
Hukumar ta yarda ta ƙara mako ɗaya a cigaba da sakin finafinan da suke a layin fitowa don kada masu finafinan su yi asara
Za a sake zama ranar Alhamis domin sake tattaunawa domin a ƙarƙare maganar.
Daga cikin waɗanda suka halarci taron akwai wakilan MOPPAN da Abdul Amart da Nazifi Asnanic da Abubakar Bashir Maishadda da sauransu.

Labarai
Kannywood:- MOPAN za ta fara raba ID CARD

Hadaddiyar kungiyar masu shirya fina-finai ta Mopan na sanar da dukkanin wadanda sukayi rijista cewa za ta fara bayar da shaida wato ID CARD ga masu bayar da umarni, da masu shirya fina-finai da masu daukar hoto me motsi cewa za’a fara basu ID CARD daga ranar 25 ga wannan wata.
Cikin sanarwa da shugaban kungiyar na kano Ado Ahmad Gidan Dabino ya fitar, ya ce bayar da ID CARD din ya shafi iya wadanda aka ambata ne kadai banda jarumai.
A cewar sa shaidar su ma Jarumai za’a fara bayar da nasu da zarar an kammala tantance su.
A don haka ƙungiyar ta MOPPAN ke sanar da dukkanin wadanda aka ambata da su ka tabbatar sunyi rijista da su je ofishin kungiyar domin karbar ID CARD.

Nishadi
Rayuwa ta ba ta da wata ma’ana a yanzu — Wizkid

Guda daga cikin fitattun mawakan nan na Afrobeats, Ayodeji Balogun, wanda aka fi sani da Wizkid, ya bayyana cewa rayuwa ba ta da wata ma’ana a gare shi tun bayan mutuwar mahaifiyarsa, Misis Jane Dolapo Balogun.
Mawaki Wizkid ya bayyana halin da ya ke ciki a kafafen sada zumunta tun bayan mutuwar ta ta, inda ya ce rayuwarsa sam babu dadi bayan mutuwar mahaifiyar tasa.
Ta cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na Instagram a ranar Laraba, mawakin ya bukaci masoyansa da su bi Ubangiji.
Jaridae Daily Trust ta ruwaito yadda mawakin ya rasa mahaifiyarsa a watan Agustan 2023, a lokacin da yake kan bulaguron wakokin sabon kundin wakarsa mai suna ‘More Love Less Ego’ a Turai.
Ya rubuta, “Kwanaki bayan na rasa mahaifiyata; Rayuwa ba ta da ma’ana! Amma mun ji. Wani lokaci dole ne ku bar komai ya tafi. A bi Ubangiji kawai, “A cewarsa”.
Rahotanni sun bayyana cewa a ranar Talata, Wizkid ya tayar da hankula a tsakanin magoya bayansa, bayan da ya wallafa hoton sa yana gadon asibiti a shafinsa na Instagram a cikin wani yanayi.
A cikin hoton dai mawakin ya yi nuni da cewar za’a duba shi, amma bai bayyana mai yake samunsa ba, lamarin da ya haifar da cece-kuce a shafun na sada zumunta.

-
Nishadi6 years ago
Ina neman mijin aure – Rayya
-
Labarai5 years ago
Hamisu Breaker ya kai kan sa wajen ‘yan sanda
-
Manyan Labarai5 years ago
KAROTA: An baiwa Baffa Babba wa’adin kwanaki bakwai
-
Labarai5 years ago
Auren dan Panshekara da ba Amurkiya ya samu cikas
-
Lafiya3 years ago
Rahoto: An gano wani gida da ake gini da takardun Kur’ani da Alluna
-
Manyan Labarai5 years ago
Sabuwar damfarar da ta fito a Kano
-
Nishadi6 years ago
An gano daliban da Adam Zango ya dauki nauyin karatun su
-
Manyan Labarai5 years ago
Ba’amurkiya da masoyin ta sun hada cinkoso a kasuwar Sabon Gari