Connect with us

Labarai

Matasa ku nemi ilimi domin dogaro da kai – KANGALA

Published

on

Kungiyar wayar da kan al’umma tare da kyautata musu jindadi da walwala ta Kangala dake Kano, ta yi kira ga al’umma musamman ma matasa da su nemi ilimin da za su dogara da kan su.

Shugaban kungiyar, Abdullahi Lawan Kangala ne ya bayyana hakan yayin wani taro daya gudana a dakin karatu na jikar kano.

Kungiyar ta shiryawa matasan ne kan amfani da shafukan sada zumunta na facebook da watsapp a matsayin wajen neman kudi a shafukan.

Ya ce kungiyar su tana shiga cikin kauyuka domin fadakar da matasa ta yadda za su yi sana’o’in dogarro da kai, maimakon shan miyagun kwayoyi suna aikata manyan laifuka.

Ya kuma shawarci matasa da su ta shi tsaye wajen neman ilimi a duk inda yake wajen ganin sun amfani rayuwar su a nan gaba.

Guda daga cikin wadanda suka gudanar da mukala a yayin taron, Jarma Hamza Malafa wanda  Alkalin kotun shari’ar musulunci a Kano, ya bukaci matasa da su mayar da hankalin su tare da karfafa zuciyar su sannan su rinka yin biyayya ga iyayen su.

Ya kuma ja hankalin iyaye da su rinka bibiyar yadda ‘ya’yansu su ke tafiyar da rayuwar su.

A nata jawabin shugabar kungiyar tallafawa matan Arewa ta kasa, Hajiya Lami Bako Yakasai, ta ce har idan za’a cigaba ta gudanar da taro irin wannan na fadakar da matasa da iyaye don cigaba mai dorewa.

Sannan ta kuma yabawa Sarkin Kano Mallam Muhammadu Sunusi na II, bisa yadda ya ke nuna jajircewar sa wajen ganin an baiwa mata ‘ya ‘ya ilimi domin cigaban rayuwar su.

Wakilin mu Tijjani Adamu ya rawaito cewa yayin taron kungiyar ta karrama Sheikh Abbas Umar Sanda, ASP Ibrahim Umar Faruq, Alhaji Umar Ka’ida da Kuma Hajiya Fatima Yusuf Mammadi bisa irin jajircewar da suke wajen hidimtawa al’umma.

 

Labarai

NAHCON ta sanya ranar fara jigilar maniyyata aikin hajjin bana zuwa Saudiyya

Published

on

Yanzu haka hukumar Aikin Hajji ta ƙasa NAHCON, ta 15 ga watan nan na Mayun 2024, a matsayin ranar da za’a fara jigilar maniyyata aikin hajjin bana, zuwa ƙasa mai tsarki.

Bayanin hakan ya fito ne ta bakin shugaban hukumar ta NAHCON, Jalal Ahmad Arabi, a wajen taron masu ruwa da tsaki kan aikin Hajji da Umrah, da ya gudana yau Alhamis birnin tarayya Abuja.

“Maniyyata kimanin 65,500 ne za su sauke Farali daga ƙasar nan a ƙasa mai tsarki; za su shafe aƙalla kwanaki huɗu domin yin ziyara a Madina kafin fara aikin Hajji, “in ji Arabi”.

Daga bisani shugaban hukumar aikin hajjin Jalal Ahmad Arabi, ya kuma bayyana cewa za ayi jigilar maniyyata aikin hajjin ne daga cibiyoyi 10 a faɗi ƙasar nan.

Continue Reading

Labarai

Gwamnatin tarayya ta ayyana gobe Laraba a matsayin ranar hutu

Published

on

Gwamnatin tarayya ta ayyana gobe Laraba, 1 ga watan Mayun 2024, a matsayin ranar hutu, domin bikin ranar ma’aikata na wannan shekara.

Ministan harkokin cikin gida, Olubunmi Tunji-Ojo, ne ya bayyana hakan, a cikin wata sanarwa da ya fitar a yau Talata.

Olubunmi, ya kuma sake nanata buƙatar ganin ma’aikata sun jajirce da yin aiki yadda ya kamata a dukkanib matakai daban-daban.

Continue Reading

Labarai

Wahalar Fetur ta haifar mana da koma baya a sana’ar mu – Mai Motar Haya

Published

on

Wani mai sana’ar tuƙin motar Haya, da kuma lodin fasinjoji mai suna Kabiru Muhammad, mazaunin ƙaramar hukumar Munjibir, ya ce ƙarancin motocin Haya da ake samu a yanzu, yana da alaƙa da wahalar man Fetur da ake fuskanta a sassan Najeriya.

A zantawar mutumin da wakilinmu Yusuf Nadabo Isma’il, ta cikin shirin rahotanni daga ƴan Zazu na yau Talata, ya ce a baya har motoci hamsin suke yiwa lodin fasinjoji su tashi, amma a yanzu Mota ɗaya suke iya cikawa sakamakon ƙarancin Fetur da ake fama da shi.

Ya kuma ce ƙaranci tare da tsadar man fetur ɗin da ake fama da shi, sun haddasa musu koma baya a sana’ar su, baya ga batun kuma matsalar da suke fuskanta da fasinjoji wajen biyan kuɗin Mota.

Wakiliyarmu da ta bibiyi shirin na ƴan Zazu Ummi Bala Ahmad ta rawaito cewa, matuƙin motar Kabiru Muhammad, ya kuma yi kira ga gwamnatin tarayya da ta jahohi, da su yi abinda ya kamata dan ganin farashin man Fetur ɗin ya sauka, domin al’umma su samun sauƙi.

Continue Reading

Trending