Connect with us

Siyasa

Nanono kaji tsoron Allah ka fadawa Buhari gaskiya –Aminu Gurgu mai fulo

Published

on

Nanono kaji tsoron Allah ka fadawa Buhari gaskiya –Audu Gurgu mai fulo

Cikin wata tattaunawa da shirin Hangen Dala yayi da Alhaji Aminu Gurgu Mai Fulu na jam’iyyar PRP ya bukaci ministan Noma Alhaji Sabo Nanono da yaji tsoron Allah ya fadawa shugaba Buhari halin da talakan Nigeria ke ciki.

Mai fulo ya roki minstan da yayi koyi da ministan wutar lantarki da ya fito ya fadawa al’ummar Nigeria gaskiya game da aikin wutar lantarki a mambila.

Shin ko yaya kuke kallon wannan batu na mai fulo?

Nanono kaji tsoron Allah ka fadawa Buhari gaskiya –Audu Gurgu mai fulo

RUBUTU MAI ALAKA:

Bana sakawa dalibai na mari –Mallam Mamman mai ‘yan mari

Dambarwa ta barke tsakanin masu lodin ababan hawa da KAROTA

Kotu ta bada belin sadiya Haruna

Siyasa

Zauren jam’iyyun haɗin kan kasa IPAC sun cire shugaban jam’iyyar LP na Kano Abdullahi Raji daga cikin tafiyar su 

Published

on

Sakataren zauren jam’iyyun haɗin kan kasar nan, IPAC na ƙasa reshen jihar Kano, kuma shugaban jam’iyyar APM na Kano Honarable Nuhu Idris, ya ce sun cire shugaban jam’iyyar LP na jihar Kano Abdullahi Raji daga cikin tafiyar su ta IPAC, baki ɗaya.

Sakataren na IPAC, Nuhu Idris ya ce sun dauki wannan mataki ne bisa yadda Rajin ke amfani da kungiyar CUPP, da rusassun jam’iyyun kasar nan suka samar a baya, a dan haka, duk wata jam’iyyar dake da rijista a yanzu na ƙarƙashin IPAC.

Ya kuma ce dokar da ta kafa IPAC, ba ta bai wa ɗan kowacce jam’iyya damar shiga hurumin wata jam’iyyar ba kamar yadda Rajin ke ƙoƙarin yi a rikicin dake faruwa a jam’iyyar APC a nan jihar Kano.

Shugaban jam’iyyar APM, ɗin Honarable Nuhu Idris, ya ce sun cire Rajin daga tafiyar ta IPAC ne, sakamakon wata sanarwa da ya fitar, ya ce, ka da hukumar zaɓe INEC, ta yi watsi da shugaban mazaɓar Ganduje, wanda hakan ba dai-dai ba ne a dokance, dan haka, suka fitar da shi daga cikin tafiyar tare da sanar da shugabancin jam’iyyar sa na kasa.

Continue Reading

Siyasa

Mun ƙudiri aniyar gyara tarbiyyar Matasa a jahar mu – Gwamnatin Kano

Published

on

Gwamnatin Kano tasha alwashin ci gaba da magance matsalar tsaro musamman wajen kawo karshen kwacen waya da harkar Daba da ake fama dashi a jihar kano.

Gwamnan Kano Injiniya Abba Kabir Yusif, ne ya bayyana hakan a yayin karɓar baƙuncin mai martaba sarkin kano Alhaji Aminu Ado Bayero, a fadar fadar gwamnatin Kano, a wani ɓangare na bikin hawan Nassarawa, da ya gudana a yau Juma’a.

Abba Kabir, ya kuma ce duk da matsalolin da gwamnatin Kano ta fuskanta a baya na harkar shari’a, amma hakan bai hana ta cika alkawarin da ta ɗauka ga al’ummar jihar kano a yakin neman zaben shekarar 2023 da ta gabata ba.

Ya ƙara da cewa gwamnatinsa ba ta tsaya ba sai da ta yi kokarin magance matsalar da harkar Ilimi ke fama dashi wajen gyara makarantu da fitar da ɗalibai kasahen waje dan karo Ilimi kyauta.

“Gwamnatin mu ta bijiro da tsarin tallafawa masu harkar shaye-shayen miyagun ƙwayoyi da harkar Daba, da sana’oin dogaro da kai domin kawo karshen Daba a jihar kano, “in ji Gwamna Abba Kabir”.

Hawan Nasarawa dai hawa ne da ake sada zumunci a tsakanin masarautar Kano da gwamnatin Jihar Kano, da kuma al’ummar jihar, wanda da aka saba gudanar da shi a duk rana ta uku, na bikin ƙaramar Sallah, da Babba.

Da yake jawabi tunda farko mai martaba sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero, ya yabawa gwamnatin Kano akan tsarin da ta fito dashi na ciyar da al’ummar jihar kano gaba, musamman ma tsarin ciyarwar azumi da tayi ga mabukata a watan Ramadan da ya gabata.

Ya ci gaba da cewa, “Wannan ciyarwar ga al’umma tsari ne da ya kamata ya ɗore domin rage raɗaɗi da yunwa da ake fama da ita; muna shawartar Gwamnatin Kano, da ta saka ido sosai wajen kawo ƙarshen Daba da ƙwacen waya da hawa doki ana sukuwa ba bisa ka’ida ba, “in ji Sarkin”.

Wakilinmu na fadar gwamnatin Kano Abba Haruna Idris ya rawaito mana cewa, Sarkin ya kumashawarci gwamnatin Kano, da ta ƙara dagewa wajen ci gaba da tallafawa Ilimin ɗalibai da ke fadin jihar kano, da sauran ayyuka da za su kawo wa jihar kano ci gaba.

Continue Reading

Siyasa

Gwamnan Kano ya sake naɗa Ogan ɓoye muƙami da wasu mutane takwas

Published

on

A ƙoƙarin sa na ci gaba da kawo cigaba a jihar sa Gwamnan Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf, ya sake naɗa Ambasada Yusuf Imam Ogan Ɓoye, a matsayin mai bashi shawara a kan harkokin matasa da wasanni, tare da naɗa wasu mutane takwas waɗanda za su taimaka masa a fannoni daban-daban.

Babban daraktan yaɗa labaran gwamnan Kano Sanusi Bature Dawakin Tofa, ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya fitar a jiya Litinin, ya ce Gwamnan ya amince da naɗa mutanen ne kamar haka;

An naɗa Farfesa Ibrahim Magaji Barde, a matsayin mai bai wa gwamnan shawara na musamman a kan harkokin tattara kuɗaɗen shiga (IGR).

Sai kuma Dr. Abdulhamid Danladi, da aka naɗa shi a matsayin mai bai wa gwamna shawara na musamman kan harkokin kasashen waje na II.

An kuma naɗa Engr. Bello Muhammad Kiru, mai bashi shawara na musamman kan albarkatun ruwa.

Yayin da aka sake naɗa Ambasada Yusuf Shuaibu Imam (Ogan Boye) a matsayin mai bai wa gwamna shawara na musamman a kan harkokin matasa da wasanni a jihar.

Har ila yau, Dr. Nura Jafar Shanono, shi kuma an ɗauke shi daga mai ba da shawara na musamman kan albarkatun ruwa zuwa Manajan Darakta, a ma’aikatar Ruwa da Gine-gine (WRECA) ta jihar Kano.

Shi kuwa Baba Abubakar Umar, ya samu sauyi daga mai bai wa gwamna Kano shawara na musamman ga harkokin makarantu masu zaman kansu, zuwa ma’aikatar dake kula da ma’aikatan wucin gadi.

An kuma nada Hon. Nasir Mansur Muhammad, a matsayin shugaban hukumar , ƙanana da Matsakaitan Masana’antu (SMEs).

Yayin da Aminu Hamidu Bako Kofar Na’isa ya zama mataimakin shugaban Hukumar kula da Albarkatun Noma da Raya Karkara ta Kano (KNARDA).

Shi kuwa Engr. Mukhtar Yusuf, an naɗa shi a matsayin mataimakin shugaban hukumar kula Albakatun ruwa Ruwa da Gine Gine (WRECA).

Sanusi Bature ya kuma ce, naɗin ya fara aiki ne nan take, inda Gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf, ya kuma taya su murna tare da fatan alkhairi.

Continue Reading

Trending