Connect with us

Labarai

Dattawan Kano: Za mu samarwa masana’antu mafita

Published

on

Kungiyar bibiyar muhimman al’amuran da su ka shafi jihar Kano wato Kano Concern ta ce za ta yi dukannin mai yiwuwa wurin ganin kungiyar ta samar wa masana’antun jihar Kano mafita a wurin gwamnati.

Shugaban kungiyar Alhaji Bashir Usman Tofa ne ya tabbatar da hakan a yayin wata ziyara ta musamman da kungiyar ta kai kamfanin hada buhu na BBY dake rukunin masana’antu a unguwar Sharada.

Ya ce sun kawo ziyara ne domin duba koken da masana’antun jihar Kano ke fama dashi a wanna lokaci wajen samar masu da mafita a wurin gwamnatin domin ganin an farfado da masana’antun jihar Kano.

A nasa jawabin shugaban kamfanin hada  buhunhuna na BBY, Ibrahim Haruna Yakasai, ya ce babban korafin da masana’antu ke fuskanta a halin yanzu shi ne karancin wutar lantarki da tsadar sinadaren sarrafa buhu.

Ya kuma ce kayayyakin da su ke amfani da su a masana’antun na su sun fi sauki a jihar Lagas maimakon jihar Kano.

Shi kuwa Manajan kamfanin, Kabiru Musa Adamu, ya ce babban matsalar da suke fuskanta a yanzu maganar haraji ne da kuma tsare-tsaren da gwamnatin tarayya ke yi a kan masana’antu.

Wakilin mu Tijjani Adamu ya rawaito cewa a yayin ziyarar tawagar Kungiyar bibiyar muhimman al’amuran da su ka shafi jihar Kano wato Kano Concern karkashin jagoranta Alh Bashir Usman Tofa sun gudanar da rangadi a cikin ma, harma ta yabawa ma’aikatan ta yadda su ke aiki tukuru wajen ganin an samar da kayayyaki hadin a Nijeriya.

Labarai

Ku guji zubar da Shara barkatai a muhallan ku – Gwamnatin Kano

Published

on

Gwamnatin jihar Kano ta gargadi al’umma da su kaucewa zubar da shara a wuraren da ba’a tanade su ba, domin kaucewa yawaitar samun cutuka a tsakanin al’umma, duba da yadda ake ci gaba da tunkarar lokacin Damuna.

Shugaban hukumar kwashe shara da tsaftar muhalli ta jihar Kano Ambasada Ahmadu Haruna Zago, ne ya bayyana hakan a lokacin da yake sanya ido kan aikin kwashe sharar da ke unguwar Zango hauran gadagi bayan Festival.

Ya ce duba da yadda Damuna ke ci gaba da tunkarowa, akwai bukatar al’umma su fahimci cewa zubar da shara barkatai ka iya haifar da cututtuka daban-daban ga iyalan su, musamman ma kasancewar sharar da ke unguwar ta Zango bayan Festival, tana tsakiyar gidajen al’umma ne da kasuwa da kuma makaranta.

Nazifi Mohammed Usman mai Duniya, da Mohammed Ibrahim wato Halifa mai Gas mazauna unguwar ta Zango ne, sun ce tarin sharar a cikin unguwar su babban ƙalubale ne a gare su, domin kuwa taruwar da tayi har ta kan shiga cikin makarantar yankin su.

Shugaban hukumar kwashe sharar Ahmadu Zago, ya kuma sha alwashin yin duk mai yiwuwa wajen tsafta ce birnin Kano, wajen kwashe shara daga kowane yankin, domin gudun faruwar ambaliyar ruwa sanadin sharar da ka toshe magunan ruwa a jihar Kano.

Continue Reading

Labarai

NAHCON ta sanya ranar fara jigilar maniyyata aikin hajjin bana zuwa Saudiyya

Published

on

Yanzu haka hukumar Aikin Hajji ta ƙasa NAHCON, ta 15 ga watan nan na Mayun 2024, a matsayin ranar da za’a fara jigilar maniyyata aikin hajjin bana, zuwa ƙasa mai tsarki.

Bayanin hakan ya fito ne ta bakin shugaban hukumar ta NAHCON, Jalal Ahmad Arabi, a wajen taron masu ruwa da tsaki kan aikin Hajji da Umrah, da ya gudana yau Alhamis birnin tarayya Abuja.

“Maniyyata kimanin 65,500 ne za su sauke Farali daga ƙasar nan a ƙasa mai tsarki; za su shafe aƙalla kwanaki huɗu domin yin ziyara a Madina kafin fara aikin Hajji, “in ji Arabi”.

Daga bisani shugaban hukumar aikin hajjin Jalal Ahmad Arabi, ya kuma bayyana cewa za ayi jigilar maniyyata aikin hajjin ne daga cibiyoyi 10 a faɗi ƙasar nan.

Continue Reading

Labarai

Gwamnatin tarayya ta ayyana gobe Laraba a matsayin ranar hutu

Published

on

Gwamnatin tarayya ta ayyana gobe Laraba, 1 ga watan Mayun 2024, a matsayin ranar hutu, domin bikin ranar ma’aikata na wannan shekara.

Ministan harkokin cikin gida, Olubunmi Tunji-Ojo, ne ya bayyana hakan, a cikin wata sanarwa da ya fitar a yau Talata.

Olubunmi, ya kuma sake nanata buƙatar ganin ma’aikata sun jajirce da yin aiki yadda ya kamata a dukkanib matakai daban-daban.

Continue Reading

Trending