Connect with us

Manyan Labarai

Gidan abincin Naira 30 ya samu tallafi.

Published

on

Hada hadar saye da siyarwar abinci tana cigaba da kankama a sabon gidan siyar da abincin naira 30 wato Nanono restaurant kamar yadda ake masa lakabi.

Mako guda kenan da bude gidan abincin a unguwar Sani Mai Nagge dake kwaryar birnin Kano, tun bayan da kalaman ministan noma Alhaji sabo Nanono suka dauki hankali.

Ministan yayi magana ne akan cewa mutum zai iya koshi a naira talatin, musamman a birnin kano, kalaman da suka fuskanci kakkausan suka daga yan Najeriya musamman kanawa.

Sai dai komai yana da sila, domin wannan al’amari ya sanya wani mai gyaran Talabijin mai suna Haruna injiniya yayi amfani da damar sa wajen bude wani gurin abincin naira 30 a layin kuka dake unguwar Sani Mainagge.

Ganin irin tagomashi da gurin cin abincin ke samu yanzu haka wani hamshakin dan kasuwa mai suna Alhaji Abdussalam Salisu Bacha ya ziyarci dakin cin abincin, domin tabbatar da sahihancin wannan waje.

Abdussalam Bacha ya shaidawa masu dakin abincin cewar ya kai ziyarar ne bisa umarnin ministan noma Alhaji Sabo Nanono, domin tabbatar da abinda kunnuwan sa suka jiye masa.

Abdussalam Bacha ya shaidawa wakilayar mu Umma Sulema cewar zai koma da kyakkyawan sako ga minista, kan kishin kai da jajircewa da masu gidan abincin suka nuna.

Jakadan daga nan ya mikawa masu gidan abincin tallafin kashin kai na naira dubu 20, domin jan jarin da suke juyawa.

A nasa bangaren mai gidan abincin Alhaji Haruna Injiniya yace sun bude gidan abincin ne domin tabbatar da ikirarin da ministan yayi, wanda ya zamanto kariya ga rubdugun da akayi wa Sabo Nanono.

MATA TA CE TA BANI KWARIN GWIWA.

Alhaji Haruna Injiniya yace matar sa Sadiya Haruna kusan itace ta bashi kwarin gwiwar bude gidan abincin, kasancewar sanaar gidansu kenan.

Wanda kuma zan kai wannan tawaga wajenta domin ganin irin kayan da take amfani dashi”. Inji Alhaji Haruna

MUN FARA DA JARIN NAIRA 2,500.

Mamallakin dakin abincin yace sun fara da jarin naira dubu 2 da dari 5, inda cikin kwanaki 3 kacal jarin sy ya ninka zuwa naira dubu 8. Wannan kuwa ya samo asali ne sakamakon budewar cinikayya tsakanin gidan abincin da al’ummar birni da kewaye, da ba zasu iya cin abinci mai tsada ba.

MAAIKATAN MU SUN NINKA.

“Mun fara da mai dakina amma yanzu muna da maa’aikata guda 4, amma bisa dukkan alamu akwai yiwuwar sake daukar kari sakamakon budewar bukata daga al’ummar gari.”

Haruna Injiniya yace su kan dora tukunya sau 4 zuwa 5 a kullim, wanda hatta yan kasuwa daga manyan kansuwannin birnin kano kan aiko da odar abinci akai musu.

SANA’A SA’A.

Wannan dai wata yar manuniya ce da mamallaka gidan abincin suka nunawa matasa musamman wadanda ke zaman kashe wando sakmmakon rashin aaiki. ko da yake dabi’ar mazauna birni kamar Kano kan raja’a akan sana’a guda da aka ga alfanun ta akan wasu tsiraru.

A shekarun baya bayan nan anga yadda harkokin noman salwa ya bude sannan kuma ya tsuke cikin kankanin lokaci, sakamakon alamun da ake gani na gwaggwabar riba.

Haka kuma take a bangaren sanaoi irinsu sayar da ruwan sha da akafi sani da pure water, da dubban kamfanoni da baa yiwa rajista ba ke cigaba da bayyana a unguwanni.

Haka kuma wuraren sayar da abincin zamani da basu da iyaka a kwaryar birnin kadai, baya ga baburan haya masu taya uku.

Abin jira a gani shine yadda salon sabon gidan abincin naira 30 da ake yiwa lakabi da Sabo Nanono restaurant zai zo ga kanawa.

Manyan Labarai

Ɗan Bijilante ya rasa ransa bisa arangamar su da wasu ƴan Daba a Kano

Published

on

Ƙungiyar sintirin Bijilante ta ƙasa reshen jihar Kano, ƙarƙashin jagorancin kwamandan ta Ubale Barau Muhammad Badawa, ta tabbatar da rasuwar guda daga cikin jami’in ta mai suna Suraj Rabi’u mazaunin Jaba da ke ƙaramar hukumar Fagge a jihar, sakamakon arangama da ƴan Daba.

Mai magana da yawun ƙungiyar Bijilante na jihar Kano, kuma Kwamandan ta na ƙaramar hukumar Fagge, Usman Muhammad Ɗan Daji, shi ne ya bayyana hakan ta cikin wani saƙon murya da ya aikowa Dala FM Kano a ranar Lahadi.a

“Jami’in Bijilanten namu ya rasa ran nasa ne sakamakon arangama da suka yi da wasu Ƴan Daba yayin gudanar aikinsu a ranar Idin ƙaramar Sallah, inda ƴan dabar suka soke shi da Ɗanbida a Ƙirji da bayansa, wanda ya yi sanadiyar rasuwarsa, “in ji Usman”.

Ya kuma ce, an kama ɗaya daga cikin waɗanda ake zargi mai suna Usman Sharif mazaunin ƙaramar hukumar Dala, kuma tuni aka miƙa shi hannun jami’an tsaro.

Usman Ɗan daji, ya kuma yi addu’ar Allah ya jiƙan jami’in nasu ya gafarta masa.

Continue Reading

Manyan Labarai

An ga watan ƙaramar Sallah a Najeriya – Sarkin Musulmi

Published

on

Mai Alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar na uku ya tabbatar da ganin jinjirin watan Shawwal a Najeriya, inda za a yi karamar Sallah gobe Lahadi.

Sarkin Musulmin ya bayyana hakan ne a yayin jawabin da ya gabatar a cikin daren Asabar ɗin nan, ya ce sun samu rahotannin ganin watan ne daga sassa daban-daban na ƙasar nan.

Alhaji Sa’ad Abubakar ya ce daga cikin guraren da aiko musu da ganin jinjirin watan na Shawwal akwai Zazzau, da kuma daga Sarkin Dutse, da Arugungu, da kuma Shehun Borno, da dai sauran gurare daban-daban na Najeriya.

Ya kuma yi kira ga al’ummar Musulmi da su gabatar da bikin sallar cikin kwanciyar hankali, tare da taimaka wa mabuƙata.

Tashar Dala FM Kano ta ruwaito cewa, biyo bayan sanarwar fadar mai alfarma Sarkin Musulmi, ya kasance ranar Lahadi take 1 ga watan Shawwal na shekarar 1446, wato ranar ƙaramar Sallah.

Continue Reading

Manyan Labarai

Shugaba Tinubu da Sifeton Ƴan Sanda ku bi wa mutanen mu da aka yi wa kisan gilla hakƙin su – Rt. Hon. Rurum

Published

on

Ɗan majalisar tarayya mai wakiltar ƙananan hukumomin Rabo, Kibiya da Bunkure, Kabiru Alhassan Rurum, ya bayyana kaɗuwar sa bisa kisan gillan da aka yi wa wasu Mafarauta su kusan 16, a garin Uromi da ke jihar Edo, a lokacin da suke hanyar su ta komawa Kano daga jihar Rivers.

Honarable Kabiru Rurum, ya bayyana hakan ne ta cikin wata sanarwa da aka aikowa Dala FM Kano a ranar Asabar, ya ce daga cikin mutanen da aka ƙona akwai mutum 11 da suka fito daga mazaɓun yankin sa na Kibiya da Bunkure, inda wasu 6 suka samu muggan raunuka suna karɓar Magani yanzu haka a jihar Edo.

A cewar Ɗan Majalisar, “Wannan abu da matasan garin Uromi a jihar Edo, suka yi ya saɓa da dokar kasa, kuma mummunan laifi ne, a don haka za mu bi kadin hakƙin mutanen mu da aka kashe a kuma waɗanda aka jikkata, “in ji shi“.

Kabiru Rurum, ya ce a matsayinsa na wakilin mutanen da aka kashe a majalisar Wakilai ta ƙasa, yana kira ga shugaban Najeriya Bola Tinubu, da babban Sifeton ƴan sanda, da su yi duk mai yiyuwa wajen ganin an kamo waɗanda suka yi wannan aika-aikar tare da hukunta su, da kuma biyan diyya ga iyalan waɗanda suka rasu da kula da waɗanda suka jikkata.

“Kasancewar wannan bashi ne na farko da ake samun wasu ɓata gari na tare matafiya akan hanya da basu ji ba basu gani ba su kashe su, a don haka muna fatan wannan karon gwamnati da sauran hukumomin tsaro za su ƙaddamar da ƙwaƙƙwaran bincike don ɗaukae mataki kamar yadda dokar kasa ta tanada, “in ji Rurum”.

Ɗan majalisar ya kuma jajantawa dukkanin al’ummar jihar Kano musamman Iyalan waɗanda suka rasu, tare da addu’ar Allah ya gafarta musu yasa Jannatul Firdausi makomar su, su kuma waɗanda suka jikkata Allah ya basu lafiya.

Continue Reading

Trending