Connect with us

Manyan Labarai

Muna zargin aikata masha’a a Kannywood. -Hisba

Published

on

Hukumar Hisba tace ta samu rahoton yadda ake cin karo da tarin kwaroron roba a wasu masana’antu na shirya fina finai ta kannywood dake kan titin gidan Zoo anan kano.

Rahoton a cewar hisbar ya gano yadda masu shara ke cin karo da robar a lunguna da taurarin masana’antar ke taruwa domin gudanar da harkokin su musamman da maraice, sai dai kuma ba’a kama sunayen wuraren ba a fili ba.

Koda yake Hisba tayi zargin wasu daga cikin yan fim din ne ke aikata masha’a da irin matan da kan baro garuruwan su domin sha’awar zamowa taurarin fina finan hausa.

Hisbbar tace tayi arba da wata matashiya data fado hannun hukumar, har take shaidawa jami’anta cewar tazo Kano ne wajen jaruma Maryam Yahaya, bayan haduwar su a facebook.

Zuwan nata kuma yana da alaka da irin sha’awar da matashiyar ta nunawa jarumar na zamowa tauraruwa.

Babban mataimaki a hukumar Muhammad Al-bukari Mika’ilu ya ce abun da wasu ‘Yan film din ake zargin suna yiwa matan da suke son shiga film din Kannywood yafi kama da karuwanci ba kasuwanci ba.

Al-bukari yace zasu gayyaci shugabannin kungiyar domin tattaunawa kan wadannan zarge zarge, da kuma tabbatar da daukar matakai da zasu kai ga dakile duk wani yunkurin aikata fasadi a masana’antar.

Dangane da batun da matashiyar tayi kan haduwar su da Maryam Yahaya a facebook, mun tuntubi Maryam Yahaya ta wayar tarho domin jin hanzarin ta, wanda kawo yanzu ba tace uffan ba.

Sai dai a nasa bangaren shugaban kungiyar Kannywood Kabiru mai kaba yace a shirye suke su baiwa hukumar hisba hadin kai da take nema, domin hukunta masu aikata badalar matukar ta tabbata cewa ana yi din kuma ‘Yan kungiyar ne.

Wakilin mu Ibrahim Abdullahi Soron-dinki ya rawaito cewa tuni aka tisa keyar budurwar da tazo gurin Maryam Yahaya zuwa Kaduna, domin danka ta a hannun mahaifanta.

Labarai

Rahoto: Mu tuba ga Allah domin fita daga tsanani – Limamin Na’ibawa

Published

on

Limamin masallacin Juma’a na Nana Aisha da ke unguwar Na’ibawa Gabas, Malam Abubakar Jibril ya ce, al’umma su tuba zuwa ga Allah, domin ya musanya tsanani zuwa yanayi na walwala.

Malam Abubakar Jibril, ya bayyana hakan ne ta cikin Huɗubar Juma’a da ya gabatar.

Mu na da cikakken rahoton a muryar da ke ƙasa.

Continue Reading

Labarai

Rahoto: Rashin wadatar zuci ke janyo zalinta a tsakanin al’umma – Limamin CBN Quarters

Published

on

Limamin masallacin Juma’a na Faruq Unguwa Uku CBN Quarters, Dr. Aminu Ismai’l, ya ce, rashin wadatar zuci ke janyo zalunci da cutar wa a tsakanin al’umma.

Dr. Aminu Isma’il, ya bayyana hakan ne, yayin da ya ke yi wa Dala FM ƙarin bayani dangane da Huɗubar Juma’a da ya gabatar.

Domin jin cikakken rahoton saurari wannan.

Continue Reading

Labarai

Rahoto: Mu guji yin ƙarya da yaɗa ta – Limamin Chiranchi

Published

on

Babban limamin masallacin Juma’a na Sheikh Aliyu Harazimi da ke unguwar Chiranchi, a ƙaramar Hukumar Kumbotso, Dr Rabi’u Tijjani Rabi’u, ya ja hankalin al’ummar Musulmi da su guji yin ƙarya da kuma yaɗa ta.

Dr. Rabi’u ya bayyana hakan ne, yayin da yake ƙarin haske dangane da abin da huɗubar sa ta ƙunsa.

Wakilin mu na ƴan Zazu, Abba Isah Muhammad na da cikakken rahoton.

Continue Reading

Trending

error: Content is protected !!