Connect with us

Nishadi

An gano daliban da Adam Zango ya dauki nauyin karatun su

Published

on

Mahukunta a makarantar Farfesa Ango Abdullahi dake Zaria, sun tabbatar da cewa jarumin fina-finan Hausa Adam A. Zango ya dauki nauyin karatun dalibai marayu guda 101 a makarantar.

Yayin tattaunawar da Dala FM tayi da shugaban makarantar Mallam Hamza Jibril ya tabbatar mana da cewa sun samu takarda daga dauke da bayanan cewa Adam Zango yana son zai dauki nauyin karatun dalibai har guda 101, kuma bayan da suka gama tattaunawa tuni Adam Zangon ya biya kudin tun a makon da ya gabata.

Hotunan takardun shaidar biyan kudin da Adam Zango yayi.

Dangane da daliban da za’a dauki nauyin karatun nas Mallam Hamza ya bayyana cewa Adam Zango ya baiwa masarautar Zazzau gurbin mutane 50 sai jam’iyyar APC aka bata gurbin mutane 31 sai kuma jam’iyyar PDP da aka baiwa mutane 20.

Dukkan su bisa sharadin zasu kawo dalibai marayu, ko talakawa da iyayen su basu da ikon biya musu kudin makaranta.

Haka zalika Mallam Hamza ya karyata dukkan rahotonnin dake yawo a soshiyal midiya na cewa batun daukar nauyin karya ne ba gaskiya bane.

Duk kokarin da Dala FM tayi na jin ta bakin jarumin Adam A. Zango amma abin ya ci tura, sai dai wani makusancinsa ya tabbatar mana da cewa Adamun ya dauki nauyin wadannan dalibai.

Tun a yammacin jiya ne dai labaran yake ta yawo a sohiyal midiya na cewa a damun ya dauki nauyin karatun daliban inda wasu ke ta gasgata labarin wasu kuma ke karyatawa.

RUBUTU MASU ALAKA:

A saukakawa matasa lefe- inji Malama Ladi

Abinda ya sanya jaruma Barauniya rushewa da kuka

Kotu ta bada belin sadiya Haruna

Labarai

Matasa sun gudanar da bikin cin nama a Kano

Published

on

Kungiyar Teburin mai shayi na unguwar Ja’en a yankin ƙaramar hukumar Gwale, Aminu S Gandu, ta gudanar da bikin cin nama na musamman a yankin.

Taron ya wakana ne a daren Laraba a unguwar Ja’en dake jihar Kano.

Yayin bikin shugaban kungiyar, Aminu S Gandu ya gargaɗi matasa da su kaucewa sanya kan su a cikin halin shaye-shaye, domin rayuwar su ta zamo abar koyi a nan duniya dama ranar gobe alƙiyama.

Ya na mai cewar,”Mu kan shirya bikin cin naman ne a tsakanin mu matasa, domin wayar da kan matasa musamman ma dominn kaucewa faɗawa cikin halin shaye-shaye. Duk shekarar mu kan shirya taron ne, tare da taya juna nishaɗi, bisa yadda matasa ke ba mu haɗin kai a dukkanin lokacin da mu ka shirya taron”.

Wakilin mu Hassan Mamuda Ya’u ya rawaito cewa, a yayin bikin al’adar da suka saba gabatarwa, matasa da dama ne ke halarta, inda bayan kammala jawabai aka kuma shiga fagen cin naman ragon da sukan yanka kamar yadda suka saba, cikin annushuwa da jin daɗi.

Continue Reading

Duniyar Bollywood

Kannywood: Mu kaucewa yin kalaman da ba su dace ba – Ali Nuhu

Published

on

Jarumi kuma mai shirya fim a masana’antar fina-finan Hausa ta Kannywood, Ali Nuhu, ya gargadi ƴan masana’antar da su kaucewa yin amfani da kalaman da ba su dace ba.

Ali Nuhu ya yi kiran ne jim kaɗan bayan fitowa daga cikin shirin Bollywood na gidan rediyon Dala FM Kano, wanda ya mayar da hankali a kan shirin fim din sa mai suna Bana Bakwai, wanda ya gudana a safiyar yau Laraba.

Ya na mai cewa”Matuƙar ƴan masana’antar ta Kannywood za su ƙara tsaftace kalaman na su, babu shakka za a samu gyara masana’antar”.

Ali Nuhu ya kuma ce fim ɗin sa mai suna Bana Bakwai ya zo da sauye-sauye wanda za a iya dangantashi da fina-finan Bollywood na ƙasar Indiya, inda ya ce shirin yafi mayar da hankali ne wajen magance ta’addanci da garkuwa da mutane da a ke fama dashi.

“Shirin Bana Bakwai zai samar da aikin yi ga matasa da dama dake Arewacin Nijeriya, bisa yadda a ka tsarashi”. Inji Ali Nuhu.

Wakilin mu Hassan Mamuda Ya’u ya rawaito cewa, Jarumin kuma mai shirya fim, Ali Nuhu ya ce, cutar Korona bairus ta kawo tasgaro a cikin masana’antar su ta Kannywood, ba dan haka ba da tuni sun kammala shirin.

Continue Reading

Nishadi

Abinda ya sa Deezell ya maka Maryam Booth a Kotu

Published

on

Mawakin Hip Hop dinnan Ibrahim Ahmad Rufa’I wanda aka fi sani da Deezell ya maka fitacciyar jarumar fina-finan Hausar nan Maryam Booth a gaban kotu.

Cikin wata takardar shigar da kara da mawakin ya wallafa a shafin sa na Twitter ta nuna cewa ya shigar da karar Maryam Booth da wasu mutane biyar a gaban kotu bias zargin yi masa batanci.

Tunda farko dai Jaruma Maryam Booth ta zargi mawakin wanda tsohon saurayin ta ne, da cewa shi ne ya dauki wani bidiyon ta tsirara a lokacin da ta fito daga bandaki, sannan ya fitar da shi aka rika yadawa a kafafan sada zumun ta.

Sai dai mawaki Deezell ya musanta zargin inda ya ce ba shine ya saki wannan bidiyon ba, sannan ya nemi da ta janye zargin da tayi masa ko kuma ya gurfanar da ita a gaban kotu.

Cikin takardar shigar da karar dai ta nuna cewa Ibrahim Ahmad Rufa’I yana neman diyyar zunzurutun kudi har miliyan goma.

Duk da cewa har izuwa wannan lokaci Deezell bai fito ya karyata zargin Maryam na cewa shi ne ya dauki bidiyon ba, sai dai kawai ya musanta sakin bidiyon ga al’umma.

Deezell ya wallafa cewa yanzu haka kotu ta baiwa ‘yan sansa umarnin cigaba da bincike kan al’amarin kafin haduwa a gaban kotu.

(more…)

Continue Reading

Trending

error: Content is protected !!