Connect with us

Baba Suda

Maganar minista ce ta sanya na bude gidan abincin 30

Published

on

Tsohon injiniyan talabijin mai suna Haruna Sani-Mainagge, wanda a yanzu ya koma siyar da garin kwaki hadin talatin ya ce matarsa ce  ta bashi shawarar farawa.

A zantawasa da gidan radiyon Dala a yamacin asabar din da ta gabata, lokacin da ya samu karin tallafin 100,000 daga wani masoyin Buhari kuma masoyin minista Nanono wato Bashir Ibrahim Gwammaja.

Ya bayyana cewar suna hira ne da matarsa kan zancen da ministan gona Sabo Nanono ya yi na cewa za’a iya koshi da 30.

Don haka ita kuma matar ta sa a matsayinta na wadda dama a gidansu ana siyar da abinci, sai take ganin cewa ai abu ne mai yiwuwa a koshi da 30 din, don  haka ta bashi shawarar yadda zai fara da garin kwaki da kulikuli.

Ya kuma ce a ranar farko ya samu ribar 400, daga bisani itama matar ta sa ta fara wake da shinkafa zubin 30 a cikin gida.

Yanzu kuma da yake samun tallafi, wake da shinkafar ya kara fadada har zuwa shagonsa na kofar gida ya zama garin kwaki da kuma wake da shinkafar.

Ya kuma kara da cewa karin tallafin na 100,000 da ya samu nan take aka bashi.

Sannan ya ce zai yi amfani da kudin wajen bude karin wasu rassan gidan abincin na 30 din tunda dai a yanzu ya daina gyaran talabijin din.

Baba Suda

Matashi ya shiga hannu bisa zargin sa da yin baɗala da Akuya

Published

on

Jami’an tsaron jihar Ogun na Amotekun, ta kama wani matashi mai suna Ibrahim Ismaila, bisa zargin laifin yin lalata da wata Akuya.

An kama Ismaila mai shekaru 18 a garin Ilu-Tuntun Olorunsogo, Ajowa, cikin karamar hukumar Ifo ta jihar.

Kwamandan Amotekun na jihar, David Akinremi, wanda ya bayyana hakan a ranar Talata ya ce, kama matashin ya biyo bayan karar da wani Jimoh Opeyemi ne ya yi, wanda ya ga Ismaila a lokacin da yake yin lalata da Akuyar.

Jimoh Opeyemi, ya je wajen wani gini sai ya hangi wanda ake zargin ya na amfani Akuyar.

Akinremi ya ce, Opeyemi ya ƙwarma ihu, inda ya jawo hankalin jama’a a yankin ciki har da wani jami’in Amotekun Corps, wanda ya samu nasarar cafke wanda ake zargin.

Continue Reading

Baba Suda

Toro: Namijin Agwagwa ya shafe tsawon shekaru 13 a raye – Umaru Tunkuli

Published

on

Wani matashi mai suna Umaru Yahaya mazaunin layin Kuka Sani Mai Nage (A), a jihar Kano, ya tabbatar mana da cewa Namijin Agwagwar (Toro) da ya ke kiwao ya shafe tsawon shekaru 13 ya na raye a wajen shi ba tare da ya gudu ba.

Matashin Umaru Tunkuli, ya ce a yanzu haka bay a sha’awar ya yanka wannan Toro, hasali ma ya kai shekaru 20 ya na kiwon Agwagi.

Ga tattaunawar su da wakilin mu Tijjani Alfindiki.

Continue Reading

Baba Suda

Rahoto: Zan bayar da kudin fansa domin a dawo da Kyanwa ta – Matashi

Published

on

Wani matashi a yankin unguwar Farawa dake karamar hukumar Kumbotso, Kawu Rufa’I, ya ce a kan Magen da ya ke zargin an yi masa garkuwa da an raba shi da abar kaunar shi, sakamakon yadda suka shaku da juna.

Kawu Rufa’I yacce zai dauki matakin shari’a mudum ya yi artabu da mutum da ya yi garkuwa da Magen, wanda ya bayyana cewa tun a baya sai da a ka dauke ta duk da furucin da a ka yi masa cewa za a dauke ta.

Wakilin mu Tijjani Adamu wanda ya tattauna da matashin ya aiko mana rahoto.

Continue Reading

Trending