Connect with us

Lafiya

Gwamnatin jihar Kano ta kaddamar da kasafin kudin, 2020

Published

on

Gwamnatin jihar Kano ta jaddada kudirin ta na kara habaka bangarorin ilimi da kuma lafiya.

Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje ne ya bayyana haka yayin da yake gabatar da kunshin kasafin kudin badi a gaban majalisar dokokin jihar, wanda ya haura naira biliyan 197.

Gwamnan yace duba da muhimmancin da bangarorin ke dashi ya sanya kasafin na badi zai fi mayar da hankali a kansu.

Ya kara da cewa acikin kasafin na badi gwamnatin jihar ta ware kaso 40 cikin dari na kasafin domin biyan albashi da kuma biyan bashin ‘yan fansho.

Haka kuma gwamnan yayi alkawarin yin duk mai yiyuwa wajen kara habaka tattalin arzikin jihar alabashi ta kasance abar duba ga sauran jihohin kasar nan.

A nasa bangaren shugaban majalisar dokokin jihar Kano Hon Abdulaziz Garba Gafasa cewa yayi majalisar dokokin zata yi kokarinta wajen ganin tayi aikin duba kasafin cikin lokaci.

Lafiya

Ku rinƙa ziyartar Asibiti ana muku gwaje-gwajen fitsari da Jini domin sanin halin da ƙodar ku take ciki – Likita

Published

on

An shawarci al’umma da su rinƙa ziyartar Asibiti akai akai wajen duba lafiyar su, ta hanyar yin gwaje-gwajen fitsari da jini domin sanin halin da kodar su ke ciki.

Dakta Muhajid Sunusi Rabi’u ne ya bayyyana hakan yayin ganawarsa da Dala FM, lokacin da suke aikin gwaje-gwajen fitsari da jini, kyauta a ɗaya daga cikin makarantu masu zaman kan su a nan Kano.

Dakta Mujaheed ya kuma ce sun gudanar da aikin ne a wani ɓangare na bikin ranar ƙoda ta Duniya, wadda aka ware duk ranar Alhamis ta mako na biyu na kowanne watan Maris domin gudanar da bikin ranar.

Continue Reading

Lafiya

Za’a yiwa kusan yara miliyan 3 rigakafin cutar shan Inna a Kano

Published

on

Gwamnatin jihar Kano tace kusan Yara miliyan 3 za’ayiwa rigakafin cutar shan inna a kananan hukumomin jihar nan 44, duba da samun ɓurɓushinta da kaso 65, a jihar ta Kano.

Kwamishinan lafiya na jihar Kano Dakta Abubakar Labaran Yusuf ne ya bayyana hakan yayin ƙaddamar da rigakafin cutar shan innar a yau Alhamis, wanda za’a kwashe kwanaki 4 ana gudanarwa a Kano.

Dakta Abubakar Labaran ya ce duba da shigowar zafin akwai buƙatar al’umma su kula da alamomin cutar sankarau, duk da gwamnati ta yi shirin bayar da agajin gaggawa, kamar yadda tashar Dala FM Kano ta rawaito.

Ma’aikatar lafiyar ta jihar Kano dai ta ce za’a ci gaba da gudanar da sauran rigafin, domin bai wa yaran jihar Kano kariya daga cututtuka masu yaɗuwa.

Continue Reading

Lafiya

Dokar tilasta gwajin lafiya kafin aure ta tsallake karatu na biyu a majalisar dokokin Kano

Published

on

Rahotanni na bayyana cewar majalisar dokokin jihar Kano, ta yi karatu na biyu a kan kudirin dokar tilasta wa masu niyyar yin aure yin gwajin cutar kanjamau, da na cutar hanta da kuma duba kwayoyin jini wato Sikila, gabanin daura aure.

Ɗan majalisa mai wakiltar karamar hukumar Takai, Hon.Musa Ali Kachako, shin wanda ya kawo kudirin dokar, ya bayyana cewa, jihar Kano na fama da matsalolin lafiya daban-daban da suka hada da cutar kanjamau saboda mutane kan yi aure ba tare da an duba lafiyarsu ba, hakan ne ma ya sa ya kai ƙudirin.

Kachako, ya ce, ƙudirin dokar idan har aka amince da shi, zai ceci rayuka da dama tare da dakile yaɗuwar cututtuka masu barazana ga rayuwar al’umma, kamar yadda jaridar Kadaura24 ta rawaito.

Da yake nuna goyon bayansa kan ƙudirin Ɗan majalisa Hon. Aminu Sa’ad, mamba mai wakiltar mazabar Ungogo, ya ce, jihohin Jigawa, Katsina da Kaduna sun zartar da irin wannan kudiri domin magance kalubalen kiwon lafiya da suke fuskanta.

Ya ce tilas ne Kano da ke da yawan al’umma a kasar nan ta zartar da kudirin dokar, domin kare lafiyar ‘yan jiharta ta hanyar samar da gwaje-gwaje kafin aure domin dakile yaduwar cututtuka, kamar cutar hanta, da sauran cututtuka.

Continue Reading

Trending