Connect with us

Nishadi

Kanyywood: Anyi bikin jaruma Hafsat Shehu

Published

on

A ranar jumu’ar da ta gabata ne aka daura Auren fitacciyar jarumar nan wato Hafsat Shehu, a nan Kano, wadda tsohuwar matar fitaccen jarumin nan ne marigayi Ahmad S. Nuhu, wanda shi ne mijinta na farko.

Marigayi Ahmad S. Nuhu da Hafsat Shehu a shekarun baya.

Bayan rasuwar jarumin Hafsat Shehu tayi aure a birnin tarayya Abuja, sai dai auren bai jima aka samu rabuwa.

Tun bayan wancan lokacin jarumar tayi kokarin dawowa masana’antar Kannywood amma abin bai yiwu ba, saidai a baya-bayan nan daya daga manyan jaruman masana’antar Adam A. Zango ya sanya ta acikin wani Film dinsa mai suna Basaja Sabon Labari, sai dai har izuwa yanzu ba’a kai ga fara daukar film din ba.

Jaruma Hafsat Shehu dai tayi irin Auren nan da mafi yawa jarumai mata na Kannywood keyi wato a boye Ango, sannan a boye ranar Aure sai ga iya ‘yan uwa da abokanan arziki na kusa, domin kuwa kawai sai gani aka yi wasu jaruman na ta wallafa mata sakonnin Allah ya bada zaman lafiya.

Waiwaye:

An haifi jaruma Hafsat Shehu ne a ranar 28 ga watan Nuwamba shekara ta 1976 yayin da shi kuma marigayi Ahmad S. Nuhu mijinta na farko aka haife shi a ranar 15 ga watan Fabrairu na shekarar 1976.

Jarumar ta bada gudunmuwa sosai a fina-finan hausa a shekarun baya, kuma mafi yawan fina-finanta tana taka rawa ne tare da marigayin wato Ahmad S. Nuhu, inda daga bisani soyayya ta kullu har ta kai su ga yin Aure.

Manazarta fina-finan Hausa na kallon ba’a taba samun wata soyayya mai karko tsakanin jaruman masana’antar ba kamar ta marigayi Ahmad S. Nuhu da Hafsat Shehu.

Kalli wasu hotunan jaruman a kasa:

Muna fatan Allah ya gafartawa marigayin, Amarya kuma Allah ya bada zaman lafiya.

Rubutu masu alaka:

Jamila Nagudu ce ta can-canta da zama gwarzuwar Kannywood –Kamaye

Jarumi Madagwal na fama da rashin lafiya

Nishadi

Abinda ya sa Deezell ya maka Maryam Booth a Kotu

Published

on

Mawakin Hip Hop dinnan Ibrahim Ahmad Rufa’I wanda aka fi sani da Deezell ya maka fitacciyar jarumar fina-finan Hausar nan Maryam Booth a gaban kotu.

Cikin wata takardar shigar da kara da mawakin ya wallafa a shafin sa na Twitter ta nuna cewa ya shigar da karar Maryam Booth da wasu mutane biyar a gaban kotu bias zargin yi masa batanci.

Tunda farko dai Jaruma Maryam Booth ta zargi mawakin wanda tsohon saurayin ta ne, da cewa shi ne ya dauki wani bidiyon ta tsirara a lokacin da ta fito daga bandaki, sannan ya fitar da shi aka rika yadawa a kafafan sada zumun ta.

Sai dai mawaki Deezell ya musanta zargin inda ya ce ba shine ya saki wannan bidiyon ba, sannan ya nemi da ta janye zargin da tayi masa ko kuma ya gurfanar da ita a gaban kotu.

Cikin takardar shigar da karar dai ta nuna cewa Ibrahim Ahmad Rufa’I yana neman diyyar zunzurutun kudi har miliyan goma.

Duk da cewa har izuwa wannan lokaci Deezell bai fito ya karyata zargin Maryam na cewa shi ne ya dauki bidiyon ba, sai dai kawai ya musanta sakin bidiyon ga al’umma.

Deezell ya wallafa cewa yanzu haka kotu ta baiwa ‘yan sansa umarnin cigaba da bincike kan al’amarin kafin haduwa a gaban kotu.

(more…)

Continue Reading

Nishadi

Anyi shagalin bikin jaruma Maryam Ceeter

Published

on

A ranar jumu’ar da ta gabata ne aka daura auren fitacciyar Jarumar fina-finan Hausar nan Maryam Isah Ceeter, a masallacin jumu’a na Alfurkan dake nan Kano.

Jaruma Maryam Ceeter ta wallafa hotunan bikin a shafin ta na Facebook inda masoyanta suka rika yi mata sakon fatan alkhairi.


Continue Reading

Nishadi

Fadakarwa muke a fina-finan mu -Furodusa

Published

on

Shahararren mai shirya fina-finan Hausar nan Sani Ali Abubakar Indomie ya bayyana cewa wa’azi da fadakarwa sune ayyukan da suke yi a fina-finan Hausa da suke gabatarwa.

Yayin wata zantawa da jarumin yayi da Dala FM kan sabon shirin sa na “Karamin Sani” Indomie ya ce manufar yin fina-finan sa, shi ne don fadakarwa da wayar da kan al’ummar mu, a don haka ya ke maida hankali wajen ganin fina-finan sa sun dace da addinin islama.

Kazalika Indomie ya ce al’umma na nuna gamsuwarsu kan fina-finan da yake yi ba tare da waka ko kida ba, domin dai su dace dai-dai da addini.

Wasu al’umma dai na ganin cewa fina-finan Hausa na wannan zamanin ko kadan sun sha bam-bam da al’ada da addinin malam Bahaushe.

Sai dai wasu na ganin cewa wannan hobbasa da su Sani Ali Abubakar Indomie keyi zai bada gudummuwa matuka wajen kara farfadowa da martabar masana’antar shirya fina-finan Hausa.

Continue Reading

Trending

error: Content is protected !!
en_USEnglish
en_USEnglish