Connect with us

Nishadi

Kannywood: Kotu ta kori shari’ar Amina Amal

Published

on

Babbar kotun tarayya mai lamba 2 dake nan Kano karkashin mai shari’ar O.A Oguata, ta kori karar da jarumar fina-finan hausar nan Amina Amal ta shigar kan fitacciyar jaruman nan Hadiza Gabon.

Tunda farko dai Amina Amal ta shigar da kara a kotun tana zargin cewa Hadiza Gabon ta ci zarafinta, tare da bata mata suna, inda ta nemi da ta biyata diyyar zunzurutin kudi har miliyan hamsin.

Jaruma Hadiza Gabon da Amina Amal lokacin ana dasawa.

Wakilin mu Abubakar Sabo ya rawaito mana cewa a zaman kotun da ya gudana a ranar larabar nan 6 ga watan Nuwamban da muke ciki, mai shari’a O.A Oguata, ya kori karar sakamakon rashin gamsar da kotun da gamsassun hujjoji kan zargin daga masu kara.

Har ila yau lauyan mai kara Barista Abdulhalim Adamu ya bayyanawa Dala FM cewa sun karbi wannan hukunci da kotu tayi, amma zasu daukaka kara zuwa gaba.

Rubutu masu alaka:

Kanyywood: Anyi bikin jaruma Hafsat Shehu

Jamila Nagudu ce ta can-canta da zama gwarzuwar Kannywood –Kamaye

Diyyar miliyan 50 nake nema daga Hadiza Gabon -Amal.

Nishadi

Abinda ya sa Deezell ya maka Maryam Booth a Kotu

Published

on

Mawakin Hip Hop dinnan Ibrahim Ahmad Rufa’I wanda aka fi sani da Deezell ya maka fitacciyar jarumar fina-finan Hausar nan Maryam Booth a gaban kotu.

Cikin wata takardar shigar da kara da mawakin ya wallafa a shafin sa na Twitter ta nuna cewa ya shigar da karar Maryam Booth da wasu mutane biyar a gaban kotu bias zargin yi masa batanci.

Tunda farko dai Jaruma Maryam Booth ta zargi mawakin wanda tsohon saurayin ta ne, da cewa shi ne ya dauki wani bidiyon ta tsirara a lokacin da ta fito daga bandaki, sannan ya fitar da shi aka rika yadawa a kafafan sada zumun ta.

Sai dai mawaki Deezell ya musanta zargin inda ya ce ba shine ya saki wannan bidiyon ba, sannan ya nemi da ta janye zargin da tayi masa ko kuma ya gurfanar da ita a gaban kotu.

Cikin takardar shigar da karar dai ta nuna cewa Ibrahim Ahmad Rufa’I yana neman diyyar zunzurutun kudi har miliyan goma.

Duk da cewa har izuwa wannan lokaci Deezell bai fito ya karyata zargin Maryam na cewa shi ne ya dauki bidiyon ba, sai dai kawai ya musanta sakin bidiyon ga al’umma.

Deezell ya wallafa cewa yanzu haka kotu ta baiwa ‘yan sansa umarnin cigaba da bincike kan al’amarin kafin haduwa a gaban kotu.

(more…)

Continue Reading

Nishadi

Anyi shagalin bikin jaruma Maryam Ceeter

Published

on

A ranar jumu’ar da ta gabata ne aka daura auren fitacciyar Jarumar fina-finan Hausar nan Maryam Isah Ceeter, a masallacin jumu’a na Alfurkan dake nan Kano.

Jaruma Maryam Ceeter ta wallafa hotunan bikin a shafin ta na Facebook inda masoyanta suka rika yi mata sakon fatan alkhairi.


Continue Reading

Nishadi

Fadakarwa muke a fina-finan mu -Furodusa

Published

on

Shahararren mai shirya fina-finan Hausar nan Sani Ali Abubakar Indomie ya bayyana cewa wa’azi da fadakarwa sune ayyukan da suke yi a fina-finan Hausa da suke gabatarwa.

Yayin wata zantawa da jarumin yayi da Dala FM kan sabon shirin sa na “Karamin Sani” Indomie ya ce manufar yin fina-finan sa, shi ne don fadakarwa da wayar da kan al’ummar mu, a don haka ya ke maida hankali wajen ganin fina-finan sa sun dace da addinin islama.

Kazalika Indomie ya ce al’umma na nuna gamsuwarsu kan fina-finan da yake yi ba tare da waka ko kida ba, domin dai su dace dai-dai da addini.

Wasu al’umma dai na ganin cewa fina-finan Hausa na wannan zamanin ko kadan sun sha bam-bam da al’ada da addinin malam Bahaushe.

Sai dai wasu na ganin cewa wannan hobbasa da su Sani Ali Abubakar Indomie keyi zai bada gudummuwa matuka wajen kara farfadowa da martabar masana’antar shirya fina-finan Hausa.

Continue Reading

Trending

error: Content is protected !!
en_USEnglish
en_USEnglish