Connect with us

Labarai

Likitoci na kokarin ce to rayuwar mutumin da ake zargi da kwartanci a Kano

Published

on

Shi dai wannan al’amari ya faru ne a kauyen Wutar Kara dake karamar hukumar Rano, da misalin karfe 5 na asuba, inda ake zargin wani mutum mai suna Sulaiman Saleh mai shekaru 30, ya kutsa kai gidan wani mutum mai mata biyu, inda yayi kokarin neman daya matar da mijin baya dakinta.

Sai dai bayan da matar ta kwarma ihu, mijinta ya shigo har ta kai sun fara rigima da Sulaiman Saleh da ake zargi da kwartancin, sai dai al’ummar unguwa sun kawo dauki inda suka yiwa wanda ake zargin duka har ta kai da ya galabaita.

Kakakin rundunar ‘yan sanda ta jihar Kano DSP. Abdullahi Haruna Kiyawa ya tabbatawa da wakilin mu Abba Isah Muhammad cewa tuni suka dauki wanda ake zargin zuwa babban asibitin garin Rano, inda daga nan aka tura shi zuwa asibitin kwararru na Murtala Muhammad dake nan birnin Kano.

DSP. Kiyawa ya kara da cewa tuni kwamishin ‘yan sanda na jihar Kano CP. Ahmed Iliyasu ya bada umarnin dawo da wannan korafi zuwa sashen bincikin na sakatariyar ‘yan sanda dake Bompai domin cigaba da bincike.

Rubutuka masu alaka:

YAU MA’AIKATAN LAFIYA DA BA LIKITOCI BA SUKA KOMA AIKI BAYAN SHAFE FIYE DA KWANAKI 40 SUNA YAJIN AIKI.

Zamu gurfanar da ‘yan mari a gaban Kotu –’Yan sanda

Labarai

Ƴan kasuwa ku tsaftace magudanan ruwa bisa gabatowar Damuna – Ƙungiyar Amata ta kasuwar Singa

Published

on

An buƙaci ƴan kasuwa da su rinƙa tsaftace tare da gyara magudanan ruwa a cikin kasuwannin su, bisa yadda damuna ke ƙara gabatowa.

Shugaban ƙungiyar Amata reshen kasuwar Singa Alhaji Musa Ibrahim Ɗan gaske, ne ya bukacin hakan a zantawar sa da manema labarai, yayin kaddamar da tsaftace kasuwar da kuma gyara mugudanun ruwan kasuwar.

Alhaji Musa, ya kuma ce ta hanyar tsaftace magudanan ruwan ne za a gujewa kowacce irin ambaliyar ruwa a cikin kasuwanni.

Continue Reading

Hangen Dala

Yau za’a fara Shari’ar Ganduje da gwamnatin Kano

Published

on

A yau ne babbar kotun jaha mai lamba 4 zata fara sauraron wata sharia wadda gwamnatin kano ta ahigar.

 

Gwamnatin jahar kano dai ta shigar da karar tsohon gwamnan jahar kano Dr Abdullahi Umar Ganduje da mai dakinsa Hafsat Umar Ganduje da kuma dansu Umar Abdullahi Ganduje da kuma wani kamfani mai suna Lamash da kuma Dr Jibrilla Muhammad.

 

Gwamnatin jahar kano dai tana zargin Ganduje da wadanna mutane da laifin hada baki da barnatar da dukiyoyin gwamnati.

 

 

Cikin zarge-zargen da ake yiwa su Ganduje akwai batun sun sayar da wasu filotai ba bisa ka’ida ba.

 

 

Da kuma batun zargin da akewa Ganduje na badakalar karbar dala tun a shekarar 2019.

 

 

Yanzu haka an girke jami,an tsaro a harabar sakateriyar Audu Bako inda kuma daga yanzu zuwa kowane lokaci kotun zata fara sauraron korafin kamar yadda wakilinmu Yusuf Nadabo Ismail ya rawaito

Continue Reading

Labarai

Ku tallafawa mazauna gidajen gyaran halin dan rage musu raɗaɗin rayuwa – Mallam Ibrahim Bunkure

Published

on

Limamin masallacin Salafussaleh dake unguwar Ɗorayi ƙarama a jihar Kano, Mallam Ibrahim Abdullahi Bunkure, ya shawarci al’umma da su ƙara dagewa wajen tallafawa mazauna gidajen ajiya da gyaran hali, da masu buƙata ta musamman, domin rage musu wani raɗaɗin rayuwa na yau da kullum.

Mallam Ibrahim Abdullahi Bunkure, ya bayyana hakan ne yayin da suka tallafawa mazauna gidan gyaran hali na Goron Dutse, da kayayyakin Abinci, da kuma na gidan yara, a wani ɓangare na taya su bikin ƙaramar Sallah, wajen ganin sun samu farin ciki a bukukuwan ƙaramar sallar da aka gudanar.

Ya ce matuƙar masu hali za su rinƙa tallafawa mazauna gidan gyaran halin da abubuwan da suka sawwaƙa, babu makawa za’a rage musu wata damuwa ta yau da kullum.

Wakilinmu Yakubu Ibrahim Dogarai ya rawaito cewa, Mallam Ibrahim Abdullahi Bunkure, ya ce daga cikin kayan abincin da suka kai wa mazauna gidajen akwai Tuwon Sallah, da garin Kwakwaki, da kuma sinadarin Ɗanɗano, da Sukari, domin ragewa mazaunan gidajen wani raɗaɗin rayuwa.

Continue Reading

Trending