Connect with us

Addini

Kun san menene ma’anar  Takutaha?

Published

on

An sha kai-kawo a tsakanin masana game da ma’ana ko asalin wannan kalma ta takutaha. Wannan ce ta sa aka sami mabambantan ra’ayoyi game da wannan kalma.

Daga ciki akwai Hassan (1998:94) ya nuna cewa, bayan al’ummar Kano sun rungumi wannan rana ne ta takutaha, sai Maguzawa da suke gabatar da bukukuwansu na bauta a lokacin suka damu, wasu suka bar garin zuwa qauyuka, suna cewa, “wannan sallar taku-ta ba tamu ba ce”. Daga nan sai aka sami kalmar takutaha.

Wasu kuwa suna ganin Kalmar ta samu ne daga qaulin Shehu Usmanu Danfodiyo, a lokacin da almajiransa suka yi wo bara a ranar da  shekarar da aka haifi Annabi salallahu alaihi wasallam ta kewayo, amma sai ya qi daukar komai a ciki, ya ce, “ ai wannan taku ta”. Daga nan sai aka sami kalmar “takutaha”.

Wasu kuma suna ganin ma’anar Kalmar takutaha ita ce, “Allah ya maimaita mana”, wasu kuma sun ce sunan Ma’aiki ne. Haka nan, wasu suna ganin Kalmar ta samu ne daga sunan wata baiwar Allah mai suna Taku, ‘yar Malam Usman Attuman, babban waliyin nan da ya zauna a Madabo (Hassan,1998:96).

A dunqule, za a iya cewa bikin takutaha yana daya daga cikin bukukuwan addini da ake yin sa a birnin Kano, duk ranar 19 ga watan Rabi’ul awwal, wato watan da aka haifi Annabi Muhammadu salallahu alaihi wasallam.

Rubutu masu alaka:

Al’umma na cigaba da raya daren Mauludi a Kano

Kaitsaye: Sheikh Shehu Dahiru Bauchi a Dala FM Kano -Mauludin Sheikh Ibrahim Inyass 2019

Duk wanda ya tsere maka a kaunar manzo (s.a.w) ya tsere maka da komai –Limamin Jumu’a

Marubuci: Tijjani Shehu Almajir

almajir02@yahoo.com

+234(0)8035943092

Cibiyar Nazarin Harsunan Nijeriya,

Jami’ar Bayero, Kano.

Addini

Bada taimakon Naira 10 a masallatai zai rage talauci ga musulamai- Malam Murtala

Published

on

Hukumar shari’a musulunci ta jihar Kano, ta ce da al’ummar musulmai za su rinka bada taimakon naira 10 a kowane masallacin juma’a da tuni ba a sami yaran da suke tallace-tallace a kan titi da kuma mutanen da suke neman kudin taimako na rashin lafiya a jihar Kano.

Daraktan yada addinin musulunci na hukumar, Muratala Muhammad Adam ne, ya bayyana hakan yayin taron limaman masallatan juma’a wanda ya gudana a karamar hukumar Dawakin Kudu.

Ya ce akwai bukatar al’umma da su rinka amfani da damar su wajen taimakon juna ta hanyar amfani da masallatai.

Ya kuma ce da za a rinka tattara kudaden da ake bayarwa a masallatai da an rinka tallafawa mata suna karatun aikin likita.

Shi kuwa a nasa jawabin yayin taron shugaban hukumar na karamar hukumar Dawakin Kudu,Abdulkarim Husseini Abdulkarim, cewa al’umma da su yi amfani da damar su yun a yanzu.

wakilin mu Tijjani Adamu, ya rawaito cewa taron limaman ya samu halartar limaman masallatan kananan hukumomin Warawa da na Dawakin Kudu.

 

 

 

 

 

 

Continue Reading

Addini

Mun karbi korafe-korafe sama da dubu biyu a shekarar 2019 -Hisbah

Published

on

Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta ce sashen lura da manyan laifuka na hukumar (ICD) ya karbi korafe-korafe har guda dubu biyu da dari hudu da sittin da biyu 2462 inda ta samu nasarar kammala dubu daya da dari biyar da arba’in da daya sauran kuma ta turasu zuwa inda ya dace.

Cikin wata sanarwa da hukumar Hisbah ta jihar Kano ta wallafa a shafinta na Facebook a ranar Lahadi ta bayyana cewa hukumar ta samu nasarar kwato zunzurutun kudade har sama da miliyan 76 na hakkokin jama’a, biyo bayan korafe-korafen da jama’a suka shigar a gabanta kan zargin tauye musu hakki.

Wanda hukumar Hisbar ta bibiya har aka samu karbo zunzurutun kudi har miliyan ashirin da shida da dubu dari biyar da arba’in da bakwai da dari bakwai da biyar N26,547,705.

Kazalika anyi yarjejiniya da wadanda akai korafi akansu kan zasu biya kudaden da ake binsu wanda ya kai har sama da naira miliyan talatin da tara N39,000,000, wanda izuwa yanzu tuni suka cigaba da kawo kudin lokaci zuwa lokaci ga hukumar Hisban kuma tana mikasu ga masu su.

Labarai masu alaka:

Baba Suda: Hisbah ta yanke hukuncin kan auren da aka daura ba tare da sanin iyaye ba

Hisbah ta yiwa wasu ‘yan “Good Evening” ritaya

Continue Reading

Addini

Kai tsaye: Ma’anar bikin Maukibi da akeyi yau a Kano

Published

on

Ku cigaba da bibiyar wannan shafi domin ana cigaba da sabinta shi.

(more…)

Continue Reading

Trending

error: Content is protected !!
en_USEnglish
en_USEnglish