Connect with us

Labarai

Kotu ta aike da wasu jami’an Civil Defence gidan gyaran hali

Published

on

Kotun majistret mai lamba 20 karkashin mai shari’a Muhammad Jibrin ta aike da wasu jami’an kare fararen hula Civil Defence da wasu jami’an sintiri gidan gyaran hali.

Cikin ‘yan viglanteen Sun hadar da Abdullahi Adamu da Najib Haruna da Abubakar Nura da Badaru Haruna da Mustafa Ado da kuma Yunusa Abubakar sai Umar Idris.

Tun da farko ‘yansanda ne suka gurfanar da su bisa zargin hada baki sanadin rauni da kuma laifin kisan kai laifukan da suka saba da sashi na 97,247 da sashi na 224 na kundin ACJA.

Kunshin tuhumar ya bayyana cewar yan sintirin su 7 sun kama wani matashi mai suna shu’aibu Hussaini dake unguwar Jaen inda sukayi ta jibgar sa daga karshe suka mika shi ofishin jami’an Civil Defence dan fadada bincike.

Sai dai daga karshe matashin ya rasa ransa dan haka ‘yansanda suka gurfanar da su.

Bayan karanta kunshin tuhumar, dukkansu sun musanta zarge- zargen.

Kotun ta kuma aike da su zuwa ranar 24 ga watan gobe don jiran shawarar lauyoyin gwamnati.

Wakilinmu Yusuf Nadabo ya yi yunkurin jin ta bakinsu sai dai abin ya ci tura.

Labarai

Shugabanni ku fito da sabbin dabaru domin kawo ƙarshen matsalar tsaro da ta tsadar rayuwa a ƙasa – Human Rights

Published

on

Ƙungiyar kare haƙƙin ɗan adam ta Universal Declaration of Human Rights dake jihar Kano, ta ce akwai buƙatar shugabanni suyi abinda ya dace dan ganin an kawo karshen matsalar tsaro, da kuma ta harkar tsaro dake ci gaba da addabar mutane a sassa ƙasar nan.

Daraktan ƙungiyar Kwamared Umar Sani Galadanci, ne ya bayyana hakan yayin zantwarsa da gidan rediyon Dala FM, a ranar Laraba, ya ce yadda ake ƙara samun ƴan ta’adda suna sace mutane tare da kashe su a sassan ƙasar nan, da kuma halin matsin rayuwar da ake fuskanta akwai buƙatar shugabanni suyi abinda ya kamata dan ganin an kawo ƙarshen matsalolin.

“Yawaitar kai hare-haren da ake samu daga ɓangaren ƴan bindiga a cikin al’ummar gari akan kashe su tare da sace su matuƙar ana son a kawo karshen matsalar, sai an ƙara himma wajen samar da makamai ga jami’an tsaro tare da samar da sabbin dabaru domin kawar da matsalar, “in ji Galadanci”.

Wannan dai na zuwa ne kwanaki kaɗan da sako ɗalibai aƙalla su sama da 285, na makarantar Kuriga dake ƙaramar hukumar Chikun ta jihar Kaduna, da ƴan bindiga suka sace su a baya, baya ga wasu ɗaliban da aka sace a wata makarantar Tsangaya a jihar ta Kaduna, wanda ko a jihar Borno ma aka jiyo yadda aka sace ƴan gudun hijira da dama a baya-bayan nan, inda matsalolin tsaron ke ƙara yin gaba a sassan ƙasar nan.

Continue Reading

Labarai

Gwamnan Kano ya kafa kwamitin duba yadda ake rabon tallafin abincin Azumi

Published

on

Gwamnatin Kano ta kafa kwamitin duba yadda ake ciyarwar azumin watan Ramadan, a kananan hokumomin cikin birnin jihar 8, domin sa ido da duba yadda ake gudanar da aikin dafawa da rabawa al’umma abincin.

Gwamnan Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf, ya kafa kwamitin ne ƙarƙashin kulawar mataimakin gwamnan Kano Kwamared Aminu Abdulsalam Gwarzo, da wasu ƴan kwamitin.

Hakan na zuwa ne dai bayan da gwamna Abba Kabir, ya ziyarci wasu daga cikin wuraren da ake dafa abincin, inda ya nuna rashin jin daɗin sa kan yadda ya ga aikin ke gudana a karamar hukumar kumbotso.

Bayanin hakan ya fito ne ta cikin wata sanarwar da babban mai taimakawa gwamnan Kano, na musamman akan gidajen rediyo Bashir Aminu Fanshekara, ya aikowa manema labarai, ya ce an bayyana Alhaji Danyaro Yakasai, a matsayin wanda zai jagoranci kwamitin mai mambobi 7.

Fanshekara ya ce kwamitin ya fara zagayawa wasu daga cikin mazaɓu dake karamar hukumar kumbotso, domin duba yadda ake dafawa da kuma raba abincin tallafin ga al’umma, inda suka suka fara da mazaɓar Na’ibawa a ranar Asabar 23 ga watan Maris ɗin shekarar 2024.

Continue Reading

Ilimi

Kaduna:- Daliban Kuriga sun sha ki iskar ‘yanci

Published

on

Gwamnatin jihar Kaduna ta bayar da rahoton cewa an sako duka ɗaliban makarantar Kuriga da ƴanbindiga suka sace.

 

An sace ɗaliban firamare da na sakandare su kusan 287 a makarantarsu da ke ƙauyen Kuriga a karamar hukumar Chikun ta jihar Kaduna fiye da makonni biyu da suka wuce.

 

Sanarwar da gwamnan jihar Kaduna, Sanata Uba Sani ya fitar ta ce an sako duka ɗaliban kuma suna cikin koshin lafiya.

 

Sanarwar ba tayi karin bayani ba game da irin matakan da aka bi wajen sako ɗaliban, sai dai gwamna Uba Sani ya nuna godiya ga shugaba Tinubu da mai bashi shawara kan tsaro da kuma sojojin Najeriya saboda irin rawar da suka taka wajen ganin an sako ɗaliban.

 

“Ba dare babu rana ina tattaunawa da Malam Nuhu Ribadu domin lalubo hanyoyin da za a bi wajen kubutar da daliban, kafin mu samu nasara,” in ji Uba Sani.

 

Galibinsu ɗaliban da aka sace ƴan shekaru biyar ne zuwa 18.

Continue Reading

Trending