Manyan Labarai
Zaman da majalisar dokokin Kano ta yi a yau laraba.

Majalisar dokokin jihar Kano ta ce za ta yi iya bakin kokarinta wajen tabbatar da gyaran dokar kafa hukumar bunkasawa da Kuma samar da tallafi ga bangaren ilimi ta jihar Kano ta shekarar dubu biyu da goma sha Tara Wanda gwamnan Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje ya aike mata.
Mataimakin shugaban majalisar dokokin jihar Kano Honarabul Hamisu Ibrahim Chidari ne ya bayyana haka yayin karanta wasikar da gwamnan Kano ya turowa majalisar game da gyaran kudirin dokar hukumar mai taken Kano state education development establishment support bill 2019.
Ya ce matukar aka amince da gyare-gyaren da aka yi ga hukumar aka Kuma amince da shi akan lokaci zai bai wa jihar Kano daman fara cin gajiyar tallafi kan harkokin ilimi daga kungiyoyin ba da tallafi kan harkar ilimi a duniya.
Wakiliyar mu ta majalisar dokokin jihar Kano Khadija Ishaq muhammad ta rawaito cewa, majalisar ta bukaci sanya batun gyaran dokar cikin ayyukan da za ta gudanar a zamanta na gaba.
A bangare guda kuma hukumomin gwamnati na cigaba da bayyana gaban kwamatocin zauren majalisar domin kare kasafin kudin su.
Inda Ma’aikatar kananan hukumomin ta jihar Kano ta gabatar da naira biliyan dari biyu da goma sha shida da miliyan sittin da biyu da dubu dari tara da saba’in da uku da dari daya da talatin da shida da Kwabo arbain da hudu a matsayin kunshin kasafin kudin kananan hukumomin jihar arbain da hudu.
Hakan ya biyo bayan karanta wata wasikar da ma’aikatar kananan hukumomi ta aikewa majalisar mai dauke da sa hannun kwamishinan ta Murtala Sule Garo wanda mataimakin shugaban majalisar Hamisu Ibrahim Chidari ya karanta da safiyar yau laraba.
Ta cikin wasikar ta bayyana cewar ma’aikatar kananan hukumomi tayi la’akari da bukatun al’umma, gabanin amincewa da kididdigar kudaden da ta ke muradin kashewa.
Daga nan ne majalisar ta baiwa kwamitocin ta mai kula da kasafin kudi da na kananan hukumomi wa’adin makwanni hudu suyi nazarin kunshin kasafin kafin su dawo da shi gabanta.

Manyan Labarai
Ɗan Bijilante ya rasa ransa bisa arangamar su da wasu ƴan Daba a Kano

Ƙungiyar sintirin Bijilante ta ƙasa reshen jihar Kano, ƙarƙashin jagorancin kwamandan ta Ubale Barau Muhammad Badawa, ta tabbatar da rasuwar guda daga cikin jami’in ta mai suna Suraj Rabi’u mazaunin Jaba da ke ƙaramar hukumar Fagge a jihar, sakamakon arangama da ƴan Daba.
Mai magana da yawun ƙungiyar Bijilante na jihar Kano, kuma Kwamandan ta na ƙaramar hukumar Fagge, Usman Muhammad Ɗan Daji, shi ne ya bayyana hakan ta cikin wani saƙon murya da ya aikowa Dala FM Kano a ranar Lahadi.a
“Jami’in Bijilanten namu ya rasa ran nasa ne sakamakon arangama da suka yi da wasu Ƴan Daba yayin gudanar aikinsu a ranar Idin ƙaramar Sallah, inda ƴan dabar suka soke shi da Ɗanbida a Ƙirji da bayansa, wanda ya yi sanadiyar rasuwarsa, “in ji Usman”.
Ya kuma ce, an kama ɗaya daga cikin waɗanda ake zargi mai suna Usman Sharif mazaunin ƙaramar hukumar Dala, kuma tuni aka miƙa shi hannun jami’an tsaro.
Usman Ɗan daji, ya kuma yi addu’ar Allah ya jiƙan jami’in nasu ya gafarta masa.

Manyan Labarai
An ga watan ƙaramar Sallah a Najeriya – Sarkin Musulmi

Mai Alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar na uku ya tabbatar da ganin jinjirin watan Shawwal a Najeriya, inda za a yi karamar Sallah gobe Lahadi.
Sarkin Musulmin ya bayyana hakan ne a yayin jawabin da ya gabatar a cikin daren Asabar ɗin nan, ya ce sun samu rahotannin ganin watan ne daga sassa daban-daban na ƙasar nan.
Alhaji Sa’ad Abubakar ya ce daga cikin guraren da aiko musu da ganin jinjirin watan na Shawwal akwai Zazzau, da kuma daga Sarkin Dutse, da Arugungu, da kuma Shehun Borno, da dai sauran gurare daban-daban na Najeriya.
Ya kuma yi kira ga al’ummar Musulmi da su gabatar da bikin sallar cikin kwanciyar hankali, tare da taimaka wa mabuƙata.
Tashar Dala FM Kano ta ruwaito cewa, biyo bayan sanarwar fadar mai alfarma Sarkin Musulmi, ya kasance ranar Lahadi take 1 ga watan Shawwal na shekarar 1446, wato ranar ƙaramar Sallah.

Manyan Labarai
Shugaba Tinubu da Sifeton Ƴan Sanda ku bi wa mutanen mu da aka yi wa kisan gilla hakƙin su – Rt. Hon. Rurum

Ɗan majalisar tarayya mai wakiltar ƙananan hukumomin Rabo, Kibiya da Bunkure, Kabiru Alhassan Rurum, ya bayyana kaɗuwar sa bisa kisan gillan da aka yi wa wasu Mafarauta su kusan 16, a garin Uromi da ke jihar Edo, a lokacin da suke hanyar su ta komawa Kano daga jihar Rivers.
Honarable Kabiru Rurum, ya bayyana hakan ne ta cikin wata sanarwa da aka aikowa Dala FM Kano a ranar Asabar, ya ce daga cikin mutanen da aka ƙona akwai mutum 11 da suka fito daga mazaɓun yankin sa na Kibiya da Bunkure, inda wasu 6 suka samu muggan raunuka suna karɓar Magani yanzu haka a jihar Edo.
A cewar Ɗan Majalisar, “Wannan abu da matasan garin Uromi a jihar Edo, suka yi ya saɓa da dokar kasa, kuma mummunan laifi ne, a don haka za mu bi kadin hakƙin mutanen mu da aka kashe a kuma waɗanda aka jikkata, “in ji shi“.
Kabiru Rurum, ya ce a matsayinsa na wakilin mutanen da aka kashe a majalisar Wakilai ta ƙasa, yana kira ga shugaban Najeriya Bola Tinubu, da babban Sifeton ƴan sanda, da su yi duk mai yiyuwa wajen ganin an kamo waɗanda suka yi wannan aika-aikar tare da hukunta su, da kuma biyan diyya ga iyalan waɗanda suka rasu da kula da waɗanda suka jikkata.
“Kasancewar wannan bashi ne na farko da ake samun wasu ɓata gari na tare matafiya akan hanya da basu ji ba basu gani ba su kashe su, a don haka muna fatan wannan karon gwamnati da sauran hukumomin tsaro za su ƙaddamar da ƙwaƙƙwaran bincike don ɗaukae mataki kamar yadda dokar kasa ta tanada, “in ji Rurum”.
Ɗan majalisar ya kuma jajantawa dukkanin al’ummar jihar Kano musamman Iyalan waɗanda suka rasu, tare da addu’ar Allah ya gafarta musu yasa Jannatul Firdausi makomar su, su kuma waɗanda suka jikkata Allah ya basu lafiya.

-
Nishadi5 years ago
Ina neman mijin aure – Rayya
-
Labarai4 years ago
Hamisu Breaker ya kai kan sa wajen ‘yan sanda
-
Nishadi5 years ago
Mansura Isah ta yi kaca-kaca da Sadiya Haruna
-
Manyan Labarai5 years ago
KAROTA: An baiwa Baffa Babba wa’adin kwanaki bakwai
-
Labarai5 years ago
Auren dan Panshekara da ba Amurkiya ya samu cikas
-
Lafiya3 years ago
Rahoto: An gano wani gida da ake gini da takardun Kur’ani da Alluna
-
Manyan Labarai5 years ago
Sabuwar damfarar da ta fito a Kano
-
Nishadi5 years ago
An gano daliban da Adam Zango ya dauki nauyin karatun su