Connect with us

Manyan Labarai

Gwamnatin Kano zata kwaskware dokar batanci.

Published

on

Gwamnatin jahar kano ta bayyana cewar zata gyara dokar dake hukunci ga masu batawa mutane suna a kafafen yada labarai.

Kwamishinan Sharia na jahar Kano Barista Ibrahim Muktar shine ya bayyana hakan ga gidan radiyon Dala, yace cin zarafin shugabanni da sarakuna da malamai babu abin da zai haifar sai tashin hankali.

Kwamishinan ya bayyana cewar zasu gyara dokar dan ta kara tsauri hakan shine kawai zai kawo raguwar wannan lamari na sakin baki.

Ibrahim muktar ya kuma bayyana cewar sashe na 39 na kundin tsarin mulki ya bawa kowa damar ya shiga kafar yada labarai ya fadi manufarsa, amma yace yanci daga inda na wani ya tsaya daga nan na wani ya fara, hakan kuwa baya nufin bata sunan wani.

Barista Muktar ya kuma bayyana cewar kafafen yada labarai suna da tasiri sosai, a saboda haka akwai bukatar suyi taka tsan tsan.

Labarai

Corona: A yi maka gwaji idan ka kusance ni a kwanannan – Amitabh Batchchan

Published

on

Fitaccen jarumin masana’antar Bollywood a kasar Indiya, Amitabh Bachchan, ya kamu da cutar Corona bayan gwaji da a ka yi masa a yau Asabar.

Jarumin wanda ya dade ya na shura a masana’antar ya tabbatar da hakan ne a shafin sa na Tiwitter cewa bayan gwaji da a ka yi masa an tabbatar masa ya kamu da cutar Covid-19.

Ya ce” Yanzu haka iyalai na da kuma ma’aikata na dukan su an yi mu su gwajin cutar, kawai sakamako mu ke jira. Kuma ina kira ga duk wanda ya yi mu’amala da ni cikin kwanaki 10 da su ka wuce ya je a yi masa gwajin cutar”. A cewar Amitabh.

Yanzu haka dai an kulle Bengaluru da kuma wasu yankunan tun daga karfe 8 na safe har zuwa biyar na yamma wanda dokar za ta fara aiki a ranar 14 zuwa 22 ga watan da mu ke ciki, saboda barkewar cutar da a ka samu.

Wasu daga cikin abokan san a cikin shafin san a Twitter tuni su ka rinka yi wa jarumin fatan samun lafiya cikin gaggawa.

Continue Reading

Manyan Labarai

Liverpool ta yi wasa 58 a gida ba tare da an doke ta ba

Published

on

Liverpool ta yi wasa 58 ba tare da ta yi rashin nasara a gida ba a gasar Firmiya ta bana wanda kwallo daya da dan wasan ta Robertson ya zura a ragar Burnley ta samu nasarar zura kwallaye 150 a kakar bana.

Sai dai kuma kunen doki 1-1 da Liverpool ta yi da Burnley ya kawo karshen Liverpool na samun nasarar cin wasa kaso cikin dari a gasara wanda Jay Rodriguez ya farke kwallon.

Kungiyar kwallon kafa ta Manchester City it ace dai har yanzu ta taba lashe gasar da maki dari cif.a gasar ta kakar 2017-18.

Yanzu haka wasanni uku ne su ka rage a karkare gasar Firimiya ta bana wanda yanzu haka Liverpool ta hada maki 93, a wanda yanzu haka idan ta samu nasarar lashe wasa uku ta kafa sabon tarihi a gasar Firimiya ta bana da maki 102.

Continue Reading

Manyan Labarai

Matashi ya lashe kofin da mahaifin sa ya kasa dauka

Published

on

Matashin mai suna Cieren Fallon kuma dan tsohon zakaran tseren wasan Doki na Jockey Kieren, ya lashe gasar da mahaifin sa har ya kamala gasar tseren doki bait aba lashe gasar ba.

Cieren mai shekaru 21 ya dai lashe gasar tseren Doki na watan Yuli wadan a ke yi wa gasar lakani da July Cup.

Lokacin da yake tseren gasar doki.

Mahaifin sa Frankie Dettori wanda yake da burin lashe gasar July Cup a kasar Birtaniya har ya yi ritaya a na biyu ya kare gasar, sai dai a karo na farko dan say a lashe gasar da mahaifin say a dade ya na jira.

Tun dan wasan ya na karami mahaifin sa yake horas da shi a dokin katako.

Continue Reading

Trending

error: Content is protected !!
en_USEnglish
en_USEnglish