Connect with us

Manyan Labarai

Gwamnatin Kano zata kwaskware dokar batanci.

Published

on

Gwamnatin jahar kano ta bayyana cewar zata gyara dokar dake hukunci ga masu batawa mutane suna a kafafen yada labarai.

Kwamishinan Sharia na jahar Kano Barista Ibrahim Muktar shine ya bayyana hakan ga gidan radiyon Dala, yace cin zarafin shugabanni da sarakuna da malamai babu abin da zai haifar sai tashin hankali.

Kwamishinan ya bayyana cewar zasu gyara dokar dan ta kara tsauri hakan shine kawai zai kawo raguwar wannan lamari na sakin baki.

Ibrahim muktar ya kuma bayyana cewar sashe na 39 na kundin tsarin mulki ya bawa kowa damar ya shiga kafar yada labarai ya fadi manufarsa, amma yace yanci daga inda na wani ya tsaya daga nan na wani ya fara, hakan kuwa baya nufin bata sunan wani.

Barista Muktar ya kuma bayyana cewar kafafen yada labarai suna da tasiri sosai, a saboda haka akwai bukatar suyi taka tsan tsan.

Manyan Labarai

Mutane uku sun rasu yayin ciro Waya a cikin Masai da ceto mutum ɗaya a Kano – Hukumar Kashe Gobara 

Published

on

Hukumar kashe Gobara ta jihar Kano, ta tabbatar da mutuwar wasu mutane uku, ciki har da Uba ɗan sa, a unguwar Ƴar Gwanda da ke ƙaramar hukumar Tsanyawa a jihar Kano.

Jami’in hulɗa da jama’a na hukumar kashe gobarar PFS Saminu Yusuf Abdullahi, ne ya bayyanawa gidan rediyon Dala FM, faruwar lamarin a daren jiya Lahadi.

Tunda fari dai mutum na farko mai suna Mallam Ɗan Juma mai laƙabin Black, wayar sa ce ta faɗa a cikin Masai, ya shiga domin ya cirota, sai dai gaza fitowar sa ke da wuya sauran mutane ukun suka bishi domin ceto shi lamarin da suma suka gaza fitowa.

Sauran mutane ukun akwai ɗan mutumin mai suna Ibrahim Ɗan Juma mai shekaru 35, sai na ukun mai suna Aminu T Gaye, da na huɗu mai suna Abbas Alhassan, ɗan shekara 28, amma shi an ciroshi a raye.

PSF Saminu Yusuf, ya kuma ce bayan faruwar lamarin ne jami’an su, suka ceto mutum na ƙarshe a raye, amma ukun farko basa cikin hayyacin su baki daya.

Ya ƙara da cewa tuni jami’an nasu suka miƙa mutanen a hannun jami’in hukumar ƴan Sanda, kuma babban baturen ƴan sanda da ke ƙaramar hukumar Tsanyawa a Kano mai suna SP Ibrahim Lado, inda suka kai su asibitin ƙwararru na ƙaramar hukumar Tsanyawa a Kano.

Continue Reading

Manyan Labarai

Gwamnan jihar Kano ya jagoranci ƙaddamar da fara aikin gadar sama da ƙasa ta Tal’udu

Published

on

Gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf ya jagoranci ƙaddamar da fara aikin gadar sama da ta ƙasa da za’ayi a shataletalen Tal’udu, da ke ƙaramar hukumar Gwale, domin samar wa al’ummar jihar saukin zirga-zirga a yankin.

Gwamnan yanyi wannan jawabin ne da yammacin yau Asabar yayin da yake ƙaddamar da aikin.

Haka kuma gwamnan ya ce gwamnatin Kano za ta sanya idanu wajen ganin an kammala aikin cikin ƙanƙanin lokaci, hakan ya sa yanzu haka gwamnatin ta tanadi duk wasu kayan aiki da ake buƙata domin gudanar da aikin.

Har ila yau, gwamna Abba Kabir, ya ce yanzu haka gwamnatin sa ta shirya tsaf wajen bayar da tallafi ga matasa, domin samar musu da hanyoyin sana’o’in dogaro da kai.

Wakilinmu na fadar gwamnatin Kano Umar Abdullahi Sheka ya rawaito cewa, gwamna Injiniya Abba Kabir Yusuf, ya ƙara da cewa an samo kamfani mai inganci wanda zai yi aikin cikin ƙanƙanin lokaci.

Continue Reading

Manyan Labarai

Bamu da wata alaƙa akan dakatar da Ganduje daga jam’iyyar APC – Gwamnatin Kano

Published

on

Gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf, ya ce basu da wata alaƙa da rikicin cikin gidan da ya kunno kai akan dakatar da Ganduje daga cikin jam’iyyar APC, a Kano.

Babban daraktan yaɗa labaran gwamnan Kano Sanusi Bature Dawakin Tofa, ne ya bayyana hakan ta cikin wani saƙon murya da ya aikowa Dala FM a yau Laraba.

Ya ce zargin da jam’iyyar APCn Kano ta yi a kan gwamnatin Kano, kan cewar tana da hannu akan dakatar da shugaban ta na riƙo a matakin ƙasa Abdullahi Umar Ganduje, zargin bashi da tushe ballantana makama.

A baya-bayan nan ne dai wani sashi na shugabancin jam’iyyar APC, a mazaɓar Ganduje da ke ƙaramar hukumar Dawakin Tofa, ya bayyana dakatar da Abdullahi Ganduje daga cikin jam’iyyar.

Sai dai daga bisani shugaban jam’iyyar na ƙaramar hukumar ya musanta batun dakatarwar inda ya ce ana shirin ɗaukar matakin da ya dace akan wanda ya fitar da sanarwar.

Bature, ya kuma ce lamarin rikici ne na cikin gidan jam’iyyar ta APC, wanda ya kamata su tsaya su gyara, mai-makon mayar da hankali akan gwamnatin Kano, lamarin da ba za suyi nasara ba.

“Tsagin jam’iyyar APCn, Kano suje can kada su ƙara tsomo mu a cikin rikicin su domin bamu da alaƙa da wani rikicin su ko wani abu, “in ji Sunusi”.

Ya kuma ce ko da yaushe jam’iyyar NNPP, mai mulki a jihar Kano burin su shine ci gaba da taimakawa al’ummar jihar ta hanyar damar da ayyukan ci gaban su.

Dawakin Tofa, ya kuma ƙara da cewa Ganduje bashi da tasiri ko da a ƙaramar hukumar sa ballantana kuma azo batun jahar Kano.

Continue Reading

Trending