Labarai
Shugabanni su kara kaimi wajen yakar cin hanci da rashawa – Farfesa Isah Sadik

Tsohon mataimakin shugaban jami’ar Bayero, kuma daya daga cikin ‘yan kwamitin kungiyar Network for Justice, kungiyar dake rajin tabbatar da adalci a tsakanin al’umma farfesa Isah Sadik Rada.
Ya ce akwai bukatar al’umma su rinka yin tunani kafin zaben wani dan takara gabanin zabarsa domin tabbatar da ingancinsa.
Farfesa Isah Sadik Rada, ya bayyana hakan ne a yayin zantawarsa da gidan Rediyon Dala, yana mai cewa yin tunani gabanin zabar dan takarar ka iya dakile yawan cin hanci da rashawa da ake fuskanta a wannan lokacin.
Ya kara da cewa suma sauran shugabanni da su kara kaimi wajen yakar cin hanci da rashawa don samun ci gaba a cikin tattalin arzikin kasa.
Wakilinmu Hassan Mamuda Ya’u ya rawaito cewa, farfesa Isah Sadik Rada, ya kuma kara da cewa a lokuta da dama sukan wayar da kan al’umma ta hanyar kafafen yada labarai domin dakile cin hanci da rashawa.
Labarai
Kotu zata yanke hukunci kan tsofafin shugabannin karamar hukumar Warawa

Kotu ta sanya ranar yanke hukunci kan tsofafin shugabannin karamar hukumar Warawa da ake zargi da aikata ba dai-dai ba.
Kotun majistret mai lamba 15 karkashin mai Sharia Muntari Garba Dandago ta sanya ranar 16 ga watan gobe dan zartas da hukunci a kunshin tuhumar da ‘yansanda suke yiwa tsofafin shugabaninn karamar hukumar Warawa.
Wadand ake tuhuma sun hada Ibrahim Abdullahi da Shehu Shazali wadanda ake zargi da lefin hada baki da yunkurin tayar da hankali da kuma lefin buga takardun jabu dangane da gonakin manoma na yankin katarkawa.
Wajibi ne bin umarnin kotu idan har ta bayar da umarni- Lauya
Kotu ta dakatar da Ganduje daga sabuwar dokar majalisar masarautar Kano
Buhari yayi nasara a kotun Koli.
wakilin mu Yusuf Nadabo ya rawaito cewar, sai dai a yayin da ake karanta kunshin tuhumar dukkanin su, sun musanta zargin.
Labarai
Ana zargin matashi da aikata kisan kai

Kotun majistret mai lamba 58 karkashin mai shari’a Zubairu Inuwa ta aike da wani matashi gidan gyaran hali.
‘yan sanda sun gurfanar da matashin mai suna Felix Abah wanda ake tuhumar sa da aikata kisan kai.
Kunshin tuhumar ya bayyana cewar tun a ranar 6/4/2017 Felix ya gayyaci wani mai koyar da tukin mota mai suna Sani Abbas dan ya koya masa mota, amma daga karshe sai ya hallakashi ya gudu da motar ya sayar da ita miliyan daya da dubu dari bakwai.
A karshe kuma ya mika kansa caji ofis yayi ikirari a gaban ‘yansanda cewar shine ya hallaka Sani.
Kotun ta sanya ranar 10/1/2020 dan jiran shawararar lauyoyin gwamnati.
Wakilinmu yusuf Nadabo Ismail ya zanta da mahaifiyar Sani wadda tace tun lokacin da aka kashe sani bata da kwanciyar hankali.
Shima Felix ya bayyana cewar ya mika kansa caji ofis ne sakamakon rashin nutsuwar da ya shiga tun lokacin da yayi kisan.
Labarai
DW ta baiwa Freedom Radio sabbin Babura don inganta ayyukansu

Shugaban sashin hausa na gidan radion DW Thomas Mosh, ya ce kyautata alaka tsakanin kafafen yada labarai na duniya zai kawo cigaba ta fannin aikin jarida.
Thomas Mosh, ya bayana hakan ne lokacin da yake mika makullin babura masu kafa biyu, guda hudu ga janar manajan gungun rukunin tashoshin Freedom Radio da yammacin Yau alhamis, a shelkwatar Freedom Radio dake unguwar Sharada a birnin Kano.
Moshe, ya kara da cewar DW ta bayar da baburan ne ga Freedom Radiyo Kaduna dan kara zaburar da ma’aikatanta musamman sashin wasanni.
Da yake nasa jawabin bayan karbar baburan janar manaja, na Freedom Radio Malam Adamu Isma’ila Garki, cewa yayi hakan zai kara inganta aikin tashar kasancewar dama akwai yarjejeniyar aiki tare.
Wakilinmu Abba Isah Muhammad, ya ruwaito cewa hukumar gudanarwa ta Freedom Radio da Dala Fm Kano sun mika Kyauta ga shugaban sashin hausan na tashar DW, haka kuma shugaban tashar Freedom Radio Kano Malam Ado Saidu Warawa, da na Dala Fm Kano Ahmad Garzali Yakubu, da sauran shugabanni na daga cikin wadanda suka kasance a gurin taron.
-
Nishadi2 months ago
Mansura Isah ta yi kaca-kaca da Sadiya Haruna
-
Labarai2 weeks ago
Yanzu-yanzu: Gobara ta tashi a kasuwar Kantin Kwari
-
Nishadi5 days ago
Ina neman mijin aure – Rayya
-
Nishadi2 months ago
An gano daliban da Adam Zango ya dauki nauyin karatun su
-
Labarai2 months ago
Dan KAROTA ya gamu da Ajalin sa
-
Labarai1 month ago
Likitoci na kokarin ce to rayuwar mutumin da ake zargi da kwartanci a Kano
-
Labarai1 month ago
Mutanen Rimin Gado sunyi zanga-zanga
-
Nishadi1 month ago
Kannywood: Kotu ta kori shari’ar Amina Amal
You must be logged in to post a comment Login