Connect with us

Labarai

Shugabanni su kara kaimi wajen yakar cin hanci da rashawa – Farfesa Isah Sadik

Published

on

Tsohon mataimakin shugaban jami’ar Bayero, kuma daya daga cikin ‘yan kwamitin kungiyar Network for Justice, kungiyar dake rajin tabbatar da adalci a tsakanin al’umma farfesa Isah Sadik Rada.

Ya ce akwai bukatar al’umma su rinka yin tunani kafin zaben wani dan takara gabanin zabarsa domin tabbatar da ingancinsa.

Farfesa Isah Sadik Rada, ya bayyana hakan ne a yayin zantawarsa da gidan Rediyon Dala, yana mai cewa yin tunani gabanin zabar dan takarar ka iya dakile yawan cin hanci da rashawa da ake fuskanta a wannan lokacin.

Ya kara da cewa suma sauran shugabanni da su kara kaimi wajen yakar cin hanci da rashawa don samun ci gaba a cikin tattalin arzikin kasa.

Wakilinmu Hassan Mamuda Ya’u ya rawaito cewa, farfesa Isah Sadik Rada, ya kuma kara da cewa a lokuta da dama sukan wayar da kan al’umma ta hanyar kafafen yada labarai domin dakile cin hanci da rashawa.

Labarai

Ku tallafawa mazauna gidajen gyaran halin dan rage musu raɗaɗin rayuwa – Mallam Ibrahim Bunkure

Published

on

Limamin masallacin Salafussaleh dake unguwar Ɗorayi ƙarama a jihar Kano, Mallam Ibrahim Abdullahi Bunkure, ya shawarci al’umma da su ƙara dagewa wajen tallafawa mazauna gidajen ajiya da gyaran hali, da masu buƙata ta musamman, domin rage musu wani raɗaɗin rayuwa na yau da kullum.

Mallam Ibrahim Abdullahi Bunkure, ya bayyana hakan ne yayin da suka tallafawa mazauna gidan gyaran hali na Goron Dutse, da kayayyakin Abinci, da kuma na gidan yara, a wani ɓangare na taya su bikin ƙaramar Sallah, wajen ganin sun samu farin ciki a bukukuwan ƙaramar sallar da aka gudanar.

Ya ce matuƙar masu hali za su rinƙa tallafawa mazauna gidan gyaran halin da abubuwan da suka sawwaƙa, babu makawa za’a rage musu wata damuwa ta yau da kullum.

Wakilinmu Yakubu Ibrahim Dogarai ya rawaito cewa, Mallam Ibrahim Abdullahi Bunkure, ya ce daga cikin kayan abincin da suka kai wa mazauna gidajen akwai Tuwon Sallah, da garin Kwakwaki, da kuma sinadarin Ɗanɗano, da Sukari, domin ragewa mazaunan gidajen wani raɗaɗin rayuwa.

Continue Reading

Labarai

Iyaye ku dai ma marawa ƴaƴan ku baya akan abinda suke yi da ya saɓawa doka – Mai unguwar Ja’en Jigawa

Published

on

Mai unguwar Ja’en Jigawa da ke ƙaramar hukumar Gwale a jihar Kano Sani Muhammad, ya ce bai kamata a rinƙa samun wasu iyaye da ɗabi’ar nan ta marawa ƴaƴan su baya akan abinda yaran suke aikatawa na saɓawa Doka, domin gujewa abinda ka je ya dawo.

Mai unguwar ya bayyana hakan ne yayin zantwarsa da gidan rediyon Dala FM, a lokacin da yake tsokaci kan yadda ake samun wasu daga cikin iyayen yankin sa na marawa ƴaƴan su baya kan abinda suke yi na ba dai dai ba, lamarin da yake ƙara ƙara kangarar da tarbiyyar ƴaƴan tare da tayar da hankalin al’umma.

Mai unguwa Sani Muhammad, ya kuma ce matuƙar yaran ba za su zauna lafiya a cikin unguwa da al’umma ba, to kuwa za su rinƙa ɗaukar matakin miƙa yaran hannun jami’an tsaro mafi kusa, domin ɗaukar matakin da ya dace a kan su, wajen ganin sun sauke nauyin da aka ɗora musu.

Sani Muhammad, ya ƙara da cewa ko a baya bayan nan wasu matasa sai da suka yi yunƙurin yin abinda bai kamata ba, lamarin da yasa aka ɗauki mataki a kansu amma aka samu wasu daga cikin iyaye suka marawa yaran nasu baya, wanda hakan kan haifar da barazanar tsaro.

Continue Reading

Labarai

Matasa ku ƙara dagewa da neman Ilmin addini da na zamani – Dr. Abdallah Gadan Kaya

Published

on

Fitaccen malamin addinin Musluncin nan Dakta Abdallah Usman Umar, ya shawarci matasa da su ƙara mayar da hankali wajen neman ilmin addinin da na zamani, domin zama ababen koyi a tsakanin al’umma.

Dakta Abdallah Gadan Ƙaya, ya bayyana hakan ne ta cikin Tafsirin Al-ƙur’ani mai girma, da yake gabatarwa cikin wannan watan azumin Ramadana a jihar Gombe.

A cewar sa, “Akwai buƙatar matasa ku yi riƙo da ƙananan sana’o’in dogaro da kai, da za ku rinƙa biyawa kan ku kuɗin makaranta wajen neman ilimi domin kaucewa zama a cikin jahilci, “in ji shi”.

Dakta Abdallah, ya kuma yi kira ga shugabanni da su dukkan abinda ya dace wajen inganta makarantu a sassan ƙasar nan, domin ganin ɗalibai sun samu ingantaccen Ilmi.

Continue Reading

Trending