Connect with us

Labarai

Wasu kauyuka a Kano sun fara amfani da bahaya a matsayin taki

Published

on

Mutanen garin kududdufawa dake y ankin karamar hukumar Ungogo sun fara sarrafa bahayar mutane suna yin taki dan sayarwa ga manoma suna samun abinda za su ciyar da iyalansu.

Wakilin mu Yusuf Nadabo ya ziyarci dajin malale dake kauyen kududdufawa a karamar hukumar Ungogo inda ya iske bahaya tsubi tsubi danye da busasshe da kuma wanda aka nike shi aka dura a buhunhuna.

Ya kuma iske wasu mutane malam Idi da Isa Musa wadanda sune suke sarrafa bahayar harma Isa Musa ke bayyana cewar suna busar da turoson ta hanyar bada masa wani sinadari.

Domin ya daina doyi kuma ya bushe cikin kankanin lokaci daga nan su fitar da duk wani datti dake jikin turoson su kuma nike shi su dura a buhu daga nan ya zama kudi.

Isa Musa ya bayyana cewar suna sayar da buhun nikakken bahaya a naira dari da hamsin kuma suna samun bahayar ne daga masu kwaso shi daga gidajen mutane.

A duk rana ana samun motocin yar kurkura kamar sawu 20 kuma kowace kurkura tana dakko duro 4 idan aka kawo sais u sarrafa shi su sayar da shi.

Ya kuma bayyana cewar baya nadamar yin sana’ar tunda dai ba kayan wani ya sata ba.

Ya kuma bayyana cewar yana da mata da yaya harda marayu da yake rike da su.

Shima wani mai aikin turoson mai suna malam Idi ya bayyana cewar ba sa kallon sana’ar ta su da kaskanci tunda tana biya musu bukatu.

Sai dai wasu na kallon yin taki da turoso na da illa ga amfanin gona da al’umma.

Ko menene illar yin tasarrafi da turoso ga lafiyar mutane da amfanin gona ku bibiyi shirin rahotanni daga yan zazu na gobe Alhamis dan ji daga bakin masana.

Labarai

Ƴan kasuwa ku tsaftace magudanan ruwa bisa gabatowar Damuna – Ƙungiyar Amata ta kasuwar Singa

Published

on

An buƙaci ƴan kasuwa da su rinƙa tsaftace tare da gyara magudanan ruwa a cikin kasuwannin su, bisa yadda damuna ke ƙara gabatowa.

Shugaban ƙungiyar Amata reshen kasuwar Singa Alhaji Musa Ibrahim Ɗan gaske, ne ya bukacin hakan a zantawar sa da manema labarai, yayin kaddamar da tsaftace kasuwar da kuma gyara mugudanun ruwan kasuwar.

Alhaji Musa, ya kuma ce ta hanyar tsaftace magudanan ruwan ne za a gujewa kowacce irin ambaliyar ruwa a cikin kasuwanni.

Continue Reading

Hangen Dala

Yau za’a fara Shari’ar Ganduje da gwamnatin Kano

Published

on

A yau ne babbar kotun jaha mai lamba 4 zata fara sauraron wata sharia wadda gwamnatin kano ta ahigar.

 

Gwamnatin jahar kano dai ta shigar da karar tsohon gwamnan jahar kano Dr Abdullahi Umar Ganduje da mai dakinsa Hafsat Umar Ganduje da kuma dansu Umar Abdullahi Ganduje da kuma wani kamfani mai suna Lamash da kuma Dr Jibrilla Muhammad.

 

Gwamnatin jahar kano dai tana zargin Ganduje da wadanna mutane da laifin hada baki da barnatar da dukiyoyin gwamnati.

 

 

Cikin zarge-zargen da ake yiwa su Ganduje akwai batun sun sayar da wasu filotai ba bisa ka’ida ba.

 

 

Da kuma batun zargin da akewa Ganduje na badakalar karbar dala tun a shekarar 2019.

 

 

Yanzu haka an girke jami,an tsaro a harabar sakateriyar Audu Bako inda kuma daga yanzu zuwa kowane lokaci kotun zata fara sauraron korafin kamar yadda wakilinmu Yusuf Nadabo Ismail ya rawaito

Continue Reading

Labarai

Ku tallafawa mazauna gidajen gyaran halin dan rage musu raɗaɗin rayuwa – Mallam Ibrahim Bunkure

Published

on

Limamin masallacin Salafussaleh dake unguwar Ɗorayi ƙarama a jihar Kano, Mallam Ibrahim Abdullahi Bunkure, ya shawarci al’umma da su ƙara dagewa wajen tallafawa mazauna gidajen ajiya da gyaran hali, da masu buƙata ta musamman, domin rage musu wani raɗaɗin rayuwa na yau da kullum.

Mallam Ibrahim Abdullahi Bunkure, ya bayyana hakan ne yayin da suka tallafawa mazauna gidan gyaran hali na Goron Dutse, da kayayyakin Abinci, da kuma na gidan yara, a wani ɓangare na taya su bikin ƙaramar Sallah, wajen ganin sun samu farin ciki a bukukuwan ƙaramar sallar da aka gudanar.

Ya ce matuƙar masu hali za su rinƙa tallafawa mazauna gidan gyaran halin da abubuwan da suka sawwaƙa, babu makawa za’a rage musu wata damuwa ta yau da kullum.

Wakilinmu Yakubu Ibrahim Dogarai ya rawaito cewa, Mallam Ibrahim Abdullahi Bunkure, ya ce daga cikin kayan abincin da suka kai wa mazauna gidajen akwai Tuwon Sallah, da garin Kwakwaki, da kuma sinadarin Ɗanɗano, da Sukari, domin ragewa mazaunan gidajen wani raɗaɗin rayuwa.

Continue Reading

Trending