Connect with us

Baba Suda

Mata sun fi maza shan kayayyakin maye- NDLEA

Published

on

Shugaban gamayyar masu yaki da sha da hana fataucin miyagun kwayoyi karkashin hukumar  NDLEA ta jihar Kano  Ali Ado Kobau, ya bayyana cewa, sun kai samame cikin dare inda suka samu mata da maza suna shaye-shayen miyagun kwayoyi, yana mai cewa, matan sunfi yawa a wajan, har ma ana zargin mata sun fi mazan buguwa.

Matan dai akasarin su farin shiga ne wanda suke satar hanya cikin dare suje su hadu da maza a sansanin shaye-shayen na su, ana dai zargin matan suna fin mazan shan kayayyakin maye musamman kodin da Roci.

NDLEA ta kama masu safarar miyagun kwayoyi

NDLEA ta shawarci iyaye mata da su guji jefa kansu cikin ta’ammali da miyagun kwayoyi

CP. Shingham yana wuce makadi da rawa –inji NDLEA

Wakilin mu Abba Isa Muhammad ya zanta da matan da aka kama, sun kuma bayyana nadamar su da alkawarin ba zasu sake ba.
Shugaban ya kara da cewa za su tantance kowanne daga cikin su domin su yi musu hukunci dai-dai da lefin su.

Baba Suda

Gwamnatin Kano ta musanta labarin da ke cewa za ta saka kafar Wando daya da Sojojin Baka

Published

on

Gwamnatin jihar Kano ta musanta labarin da ke yawo na cewa za ta saka kafar wando daya da Sojojin Baka.

 

Kwamishinan yada labaran jihar Kwamred Ibrahim Waiya shi ne ya bayyana hakan lokacin wani taron karawa juna sani da hukumar kula da kafafen yada labarai NBC ta shirya a yau Alhamis.

 

Yace gwamnatin Kano za ta hada kai da Yan siyasa masu magana a Rediyo da aka fi Sani da Sojojin Baka, domin tsaftace harkokin siyasar Kano.

 

Haka kuma kwamishinan ya musanta labarin da ke cewa Gwamnatin Kano za ta saka kafar wando daya da Sojojin Baka.

 

Kwamishina Waiya ya kuma ce za su hada kai da kafafen yada labarai domin Kara kawo tsafta a harkokin siyasar Kano.

Continue Reading

Baba Suda

Matashi ya shiga hannu bisa zargin sa da yin baɗala da Akuya

Published

on

Jami’an tsaron jihar Ogun na Amotekun, ta kama wani matashi mai suna Ibrahim Ismaila, bisa zargin laifin yin lalata da wata Akuya.

An kama Ismaila mai shekaru 18 a garin Ilu-Tuntun Olorunsogo, Ajowa, cikin karamar hukumar Ifo ta jihar.

Kwamandan Amotekun na jihar, David Akinremi, wanda ya bayyana hakan a ranar Talata ya ce, kama matashin ya biyo bayan karar da wani Jimoh Opeyemi ne ya yi, wanda ya ga Ismaila a lokacin da yake yin lalata da Akuyar.

Jimoh Opeyemi, ya je wajen wani gini sai ya hangi wanda ake zargin ya na amfani Akuyar.

Akinremi ya ce, Opeyemi ya ƙwarma ihu, inda ya jawo hankalin jama’a a yankin ciki har da wani jami’in Amotekun Corps, wanda ya samu nasarar cafke wanda ake zargin.

Continue Reading

Baba Suda

Toro: Namijin Agwagwa ya shafe tsawon shekaru 13 a raye – Umaru Tunkuli

Published

on

Wani matashi mai suna Umaru Yahaya mazaunin layin Kuka Sani Mai Nage (A), a jihar Kano, ya tabbatar mana da cewa Namijin Agwagwar (Toro) da ya ke kiwao ya shafe tsawon shekaru 13 ya na raye a wajen shi ba tare da ya gudu ba.

Matashin Umaru Tunkuli, ya ce a yanzu haka bay a sha’awar ya yanka wannan Toro, hasali ma ya kai shekaru 20 ya na kiwon Agwagi.

Ga tattaunawar su da wakilin mu Tijjani Alfindiki.

Audio Player



Continue Reading

Trending