Connect with us

Addini

Majalisar shura ta Tijjaniyya bata goyan bayan raba masarautar Kano- Mai hula

Published

on

Shugaban majalisar shura ta darikar Tijjaniyya Halifa Sani Shehu Mai hula ya ce darikar Tijjaniyya bata goyon bayan taba masarautar Kano wanda gwamnatin Kanon take yi a halin yanzu.

Halifa Sani Shehu me Hula ya bayyana hakan ne a wani taron manema labarai wanda ya gudana da safiyar Alhamis din nan a nan Kano.

Ya kuma Kara da cewa tun a baya sun zauna da gwamnati da kuma masarautar suka kuma bada shawarwari amma kuma aka ki amfani da shawarar aka ci gaba da taba masarautar don haka ne ya zamar musu dole su bayyana matsayar su akai kamar yadda shima sheik Dahiru Usman Bauchi ya riga ya yi bayani.

Darikar tijjaniyya ta ce ba ta goyon bayan taba masarautar Kano

Raba Masarautar Kano: Umarnin kotu baizo mana akan lokaci ba -Sakataren gwamnatin Kano

Gwamnati za ta kashe masarautar Kano- Farfesa Naniya

Wakilinmu Ibrahim Abdullahi Sorondinki ya rawaito cewa Halifa Shehu Sani mai Hula ya kuma ce wannan Ita ce matsayar da dukkanin mabiya darikar Tijjaniya suke kai.

 

 

Addini

Kano: Mun bayar da kwana 40 a mayar da almajirai gidajen su – Dr. Zahra’u

Published

on

Gwamnatijn Jihar Kano za ta fara kwashi almajirai da ke barace-barace a kan Shatale-tale, da mahadar tituna a fadin jihar Kano tare da bai wa alaranmomin wa’adin kwanaki Arba’in, da su mayar da almajiaran su gidajen su.

Kwamishiniyar harkokin mata da kananan yara ta Jihar kano Dr. Zahra’u Muhammad Umar ce ta bayana hakan a wani taron manema labarai a ranar Laraba.

Ta ce, “Daukan wannan mataki ya zama dole sakamakon bayanan sirri da gwamnati ke samu na yin lalata da wasu yara mata da a ke zargin mabarata ne”.

Ta kuma ce, “A bangaren kananan al’amajirai kuwa gwamnati ta bai wa alaranmomin su kwanaki Arba’in domin mayar da su gidajen su”. A cewar Dr. Zahra’u Muhammad

Wakiliyarmu Yusuf Ali Abdullah ya ruwaito cewa, gwamnatin ba za ta saurarawa duk alaranmomin da suka bujirewa umarninta ba.

Continue Reading

Addini

Rahoto: An fara sallah a masallacin Juma’a na Yamadawa

Published

on

An bude sabon masallacin Jum’a a unguwar Yamadawa, Dorayi Babba da ke karamar Hukumar Gwale a jihar Kano, wanda a ka sakawa suna Masjidul Su’ada.

Hudubar da Limamin masallacin, Muhammad Hadi Sarki ya gabatar ta kunshi kiran al’umma da yin Istigfari domin neman gafarar ubangiji.

Domin jin cikakken rahoton saurari wannan.

 

Continue Reading

Addini

Ka da mutum ya zauna ba ya aikin da zai taimaki kan sa – Dr. Khidir

Published

on

Limamin masallacin Juma’a na Uhud da ke unguwar Maikalwa a ƙaramar hukumar Kumbotso Dr. Khidir Bashir ya ce, ba daidai ba ne musulmi ya zauna ba ya aikin komai, ya koma gefe ya ce Allah zai tallafa ma sa.

Dr. Khidir Bashir ya bayyana hakan a yayin huɗubar sallar Juma’a da ta gudana a ranar Juma’a.

Ya ce, “Ko lokacin da Manzon Allah (S.A.W) zai yi hijira ba komawa gefe ya yi ba ya dogara ga Allah, sai da ya aikata wasu ayyuka da za su bas hi nasarar yin hijira sannan ya bar wa Allah lamarin”.

Ya kuma ce, “Sahabbai sun taka muhimmiyar gudunmawa wajen samun nasarar yin hijirar manzon Allah (S.A.W) daga Makkah zuwa Madina”. A cewar Dr. Khidir Bashir

Wakilin mu Nasir Khalid Abubakar ya rawaito cewa, Dr. Khidir Bashir ya kuma kara da cewa, ba daidai ba ne yadda wasu ke zama su na zagin Sahabbai duba da yadda suka baiwa Manzon Allah (S.A.W) gudummawa wajen daukaka addini.

Continue Reading

Trending

error: Content is protected !!