Connect with us

Baba Suda

Kano: wasu almajirai sun dumama tuwo da hasken rana

Published

on

Almajiran sun ajiye Tuwo da Shinkafar  akan  wata  `katuwar Taya da nufin za su dumama su da zafin hasken rana bayan da yayi sanyi.

Hasali tuwon na cikin wata leda gami da miyar a hade, gefe guda kuma wata shinkafa ce a cikin  Tasa.

Filin Baba Suda na tashar Dala Fm  yayi tozali da wadannan  Almajirai  da tsakar rana jiya Alhamis  dauke da tuwon a sun kokarin su dumama abincin.

Bugu da gari, almajiran sun kara da cewa bayan sun gama dumama abincin za su koma gefe guda wajen inuwa don cin abincin nasu.

Muna kiran gwamnati da ta kara zage dantse wajen taimakawa almajirai -Binta Lawal

Wakilan filin Baba Suda sun sami zarafin  tattaunawa da guda da daga cikin almajiran,wanda ya bayyana  cewa  sun yi  bara ne a wani gida inda aka basu wannan Tuwo wanda aka fito da shi daga  cikin Firji.

Almajirin ya kara da cewa sun saka wannan Tuwo ne  na Semovita da miyar Kubewa acikin Rana da nufin su dumama shi, sakamon sanyin da tuwon yake da shi kasancewar daga Firji aka fito da shi sannan kuma bayan wannan Tuwo yayi zafi sai su cinye shi.

Wata Likita mai suna  Dakta Nabila Ado Yau ta asibitin kwararru na Murtala ta bayyanawa filin Baba Suda cewa ,saka abici a cikin Leda yana da matsala ga lafiyar mutane,tace zafin Abincin zai sa ledar ta narke a jikin abincin,wanda hakan kan iya haifar da cutar Daji wadda aka fi sani da[ Cancer] a turance.

Baba Suda

Matashi ya shiga hannu bisa zargin sa da yin baɗala da Akuya

Published

on

Jami’an tsaron jihar Ogun na Amotekun, ta kama wani matashi mai suna Ibrahim Ismaila, bisa zargin laifin yin lalata da wata Akuya.

An kama Ismaila mai shekaru 18 a garin Ilu-Tuntun Olorunsogo, Ajowa, cikin karamar hukumar Ifo ta jihar.

Kwamandan Amotekun na jihar, David Akinremi, wanda ya bayyana hakan a ranar Talata ya ce, kama matashin ya biyo bayan karar da wani Jimoh Opeyemi ne ya yi, wanda ya ga Ismaila a lokacin da yake yin lalata da Akuyar.

Jimoh Opeyemi, ya je wajen wani gini sai ya hangi wanda ake zargin ya na amfani Akuyar.

Akinremi ya ce, Opeyemi ya ƙwarma ihu, inda ya jawo hankalin jama’a a yankin ciki har da wani jami’in Amotekun Corps, wanda ya samu nasarar cafke wanda ake zargin.

Continue Reading

Baba Suda

Toro: Namijin Agwagwa ya shafe tsawon shekaru 13 a raye – Umaru Tunkuli

Published

on

Wani matashi mai suna Umaru Yahaya mazaunin layin Kuka Sani Mai Nage (A), a jihar Kano, ya tabbatar mana da cewa Namijin Agwagwar (Toro) da ya ke kiwao ya shafe tsawon shekaru 13 ya na raye a wajen shi ba tare da ya gudu ba.

Matashin Umaru Tunkuli, ya ce a yanzu haka bay a sha’awar ya yanka wannan Toro, hasali ma ya kai shekaru 20 ya na kiwon Agwagi.

Ga tattaunawar su da wakilin mu Tijjani Alfindiki.

Continue Reading

Baba Suda

Rahoto: Zan bayar da kudin fansa domin a dawo da Kyanwa ta – Matashi

Published

on

Wani matashi a yankin unguwar Farawa dake karamar hukumar Kumbotso, Kawu Rufa’I, ya ce a kan Magen da ya ke zargin an yi masa garkuwa da an raba shi da abar kaunar shi, sakamakon yadda suka shaku da juna.

Kawu Rufa’I yacce zai dauki matakin shari’a mudum ya yi artabu da mutum da ya yi garkuwa da Magen, wanda ya bayyana cewa tun a baya sai da a ka dauke ta duk da furucin da a ka yi masa cewa za a dauke ta.

Wakilin mu Tijjani Adamu wanda ya tattauna da matashin ya aiko mana rahoto.

Continue Reading

Trending