Connect with us

Nishadi

Ina neman mijin aure – Rayya

Published

on

Fitacciyar jarumar fina-finan hausar nan Surayya Aminu wadda aka fi sani da Rayya ta bayyana cewa a kasuwa take tana neman miji domin tayi aure.

Jaruma Rayya ta bayyana cewa a shirye take ga duk wanda yake so da kaunarta tsakani da Allah zai aure ta, kuma shi aure lokaci ne “ina sa ran nayi aure nan bada jimawa ba cikin ikon Allah” a cewar Rayya.

Idan zaku iya tunawa dai a kwanakin baya a wata tattaunawa da Dala FM tayi da abokin aikin Rayya jarumi Yawale ya bayyana cewa a shirye yake kuma zai iya auren Rayyan a zahiri.

Sai dai a wancan lokacin jaruma Rayya ta bayyana wa Dala FM cewa abu biyu ne zai hanata auren Yawale, na farko yana da aure ita kuma bata son kishiya, sannan Yawale bashi da kudi ita kuma mai kudi take so.

Amma daga bisani jaruma Rayya ta sanar da janye wannan kalaman a shafinta na Instagram.

Labarai masu alaka:

Mu muka haifi Kannywood –Inji Kamaye

Nayi mamakin baiwa Fati Washa Gwarzuwar Kannywood –Kamaye

Labarai

Da Ɗuminsa: Ƴan sanda sun hana Tashe a Kano

Published

on

Rundunar ƴan sandan jihar Kano, ta haramta yin wasan al’adar Tashe a faɗin jihar.

Rundunar ta bakin mai magana da yawun ta, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya tabbatar da hakan ga manema labarai a yau Litinin.

Ya ce,”Sakamakon yadda wasu matasa ke fakewa da Tashen, suna yi wa mutane ƙwace a lokacin da su ke tsaka da wasan”.

Wannan matakin ya biyo bayan umarnin ƙwamishinan ƴan sanda CP Sama’ila Shu’aibu Dikko.

Continue Reading

Kannywood

Cutar rashin ji: Jarumin Hollywood Bruce Willis ya hakura da yin fim

Published

on

Fitaccen jarumi a cikin masana’antar fina-finan Amurka ta Hollywood, Bruce Willis, ya samu matsala a kwakwalwar sa wanda ya janyo kunnen sa ya tabu, wanda hakan ya haddasa masa daina ji.

Bruce Willis mai shekaru 67, wanda iyalan sa suka tabbatar da hakan cewa, ya sanya shi ritayar dole na dai na fitowa a cikin harkokin fina-finai.

A wata sanarwa da iyalansa suka fitar, sun ce, an gano cewa, ya na fama da matsalar jin magana a sanadiyar matsalar ƙwaƙwBrucealwa.

Bruce Willis ya ya fito a cikin fim din Die Hard  da Red da Unbreakable Friends da dai sauransu da dama.

Continue Reading

Labarai

Tirkashi: Matashi ya yi garkuwa da hoton bidiyon badalar wata mata

Published

on

Hisbah ta yiwa wasu ‘yan “Good Evening” ritaya

A na zargin wani matashi da yin garkuwa da hoton bidiyon badalar wata mata tare da neman kudin fansa, ko kuma ya yada ta a duniya al’umma su gani.

An dai yi zargin matashin wanda muka boye sunan sa, ya ce, ya dauki hoton bidiyon ne a wayar mai gidan sa da kuma lambar matar, ba tare da shi mai gidan nasa ya sani ba, wanda ya kirawo ta a waya, sannan ya tura mata hoton bidiyon a wayar ta, tare da yi mata barazanar ko dai ta biya shi makudan kudi, ko kuma ya yada ta a duniya.

A kokarin yadda zai tura asusun da za a saka masa kudin ne ‘yan Hisba suka damke shi, sai dai ya ce,“Ni dai ba wannan ce manufa ta ba, kawai dai ina so da dakile badalar da ta ke yi, saboda ni ma aikin Hisba na ke yi”. In ji Matashin wanda wakilin mu Ibrahim Abdullahi Sorondinki ya rawaito mana.

Continue Reading

Trending