Connect with us

Addini

Kai tsaye: Ma’anar bikin Maukibi da akeyi yau a Kano

Published

on

Ku cigaba da bibiyar wannan shafi domin ana cigaba da sabinta shi.

Maukibi dai biki ne da mabiya darikar kadiriyya ke gabatarwa duk shekara a birnin Kano.

A yayin bikin dai mabiya darikar kadiriyya na yin jerin gwano daga shalkawatar darikar kadiriyyan ta Africa wato gidan shugaban darikar na Afrcia marigayi Sheikh Nasiru Kabara zuwa masallacin jumu’a na Jami’u Kanzil Mudalsami dake kan titin Katsina a birnin Kano.

Hoto yayin gudanar da maukibi a Kano

A wannan masallacin ne ake gudanar da addu’o’I da kuma jawabai daga jagororin taron a kowacce shekara.

Hoto yayin gudanar da maukibi a Kano

A duk shekara dai bikin Maukibi yana fara kankama ne daga ranar Laraba inda ake gudanar da bukukuwa, karatuka, da addu’o’I a gidan Kadiriyya dake unguwar Kabara a nan Kano.

Daga bisani kuma ranar Asabar a fita zuwa bikin na maukibi wanda ake yiwa lakabi da bikin waliyai.

Hoto yayin gudanar da maukibi a Kano

Al’umma daga kasashe daban-daban na duniya, da kuma wasu jihohin Najeriya da birane da kuma kauyuka na shigowa jihar Kano domin halartar bikin Maukibin.

Hoto yayin gudanar da maukibi a Kano

A yau Asabar 12 ga watan Disamba na shekara ta 2019 ake gabatar da bikin Maukibin na bana, wanda shi ne karo na 69.

Yayin wata tattaunawa da Dala FM tayi da shugaban darikar kadiriyya na Africa a daren jiya Sheikh Dakta Kariballahi Nasiru Kabara ya bayyana cewa babban sakonsa a wannan taron shi ne kira ga al’umma kan a zauna lafiya domin tabbatar da hadin kai da cigaba ga al’ummar mu.

Hoto yayin gudanar da maukibi a Kano

Kai tsaye dai muna kawo muku yadda bikin yake gudana ta akwatunan rediyonku akan mita 88.5 a zangon FM.

Labarai masu alaka:

Al’umma na cigaba da raya daren Mauludi a Kano

Yadda ake gudanar da bikin Takutaha a Kano

Addini

Matsin Rayuwa: Shugabanni ku sassautawa al’umma – Babban Limamin Kano

Published

on

Babban limamin Kano, kuma wanda ya jagoranci sallar idi a babban masallacin idin na Kofar Mata a nan Kano, Farfesa Muhammed Sani Zaharaddin, ya ja hankalin shugabanni da su sassautawa al’umma, sakamakon halin matsin rayuwar da ake ciki a yanzu.

Farfesa Muhammed Sani Zaharaddin, yayi jan hankalin ne yayin huɗubar da ya gabatar, bayan kammala sallar idi da ta gudana a yau Laraba, a babban masallacin idin dake unguwar Kofar Mata a Kano.

Ya kara da cewa kasancewar al’umma na cikin mawuyacin hali da kuncin rayuwa, akwai buƙatar shugabanni su yi bakin ƙoƙarin su, domin kawo sauki daga halin matsin halin rayuwar da ake fama dashi.

Yayin sallar Idin gwamnan Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf, da mataimakin sa Kwamared Aminu Abdulsalam Gwarzo, da sauran al’umma da dama ne suka halarta.

Wakilinmu na fadar gwamnatin Kano Abba Haruna Idris ya rawaito cewa, Farfesa Muhammed Sani ya kuma ja hankalin al’umma, da su koma ga Allah Subhanahu wata’ala domin samun dacewa a Duniya da gobe Ƙiyama.

Continue Reading

Addini

Ku fara duban watan Sallah daga gobe Litinin – Fadar Sarkin Musulmi

Published

on

Yanzu haka kwamitin ganin wata na Fadar mai alfarma sarkin Musulmi Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III, ya buƙaci al’ummar musulmin ƙasar nan da su fara duban jinjirin watan Shawwal, daga gobe Litinin, 8 ga watan Afrilun, 2024 da ake ciki.

Bayanin hakan na ƙunshe ne ta cikin wata sanarwa da kwamitin ya fitar a yammacin yau Lahadi a jihar Sokoto.

Sanarwar ta ce, duk wanda ya ga watan Shawwal, ya sanarwa Mai Gari ko Hakimi mafi kusa wanda kuma zai sanar har zuwa fadar Sarkin Musulmi.

Har ila yau, fadar Sarkin musulmin ta kuma bayar da lambobin waya waɗanda mutane za su yi amfani da su wajen ba da rahoton ganin watan Sallah ga fadar Sarkin musulmin, kamar yadda kafar yaɗa labarai ta BBC ta rawaito.

Continue Reading

Addini

Iyaye ku kula da tarbiyyar ƴaƴan ku – Malama Fatima Tsakuwa

Published

on

Malamar addinin musulunci dake nan Kano Malama Fatima Ahmad Tsakuwa, ta shawarci mata da su ƙara himma wajen kula da tarbiyyar ƴaƴansu, tare da kuma zaburar da su mahimmancin yin addu’a a cikin wannan wata na Ramadana, domin rabauta da rahamar Ubangiji S.W.T.

Malama Fatima Ahmad Tsakuwa, ta bayyana hakan ne yayin taron bita ta musamman da gidauniyar Bango Charity Foundation ƙarƙashin Malama Fatima Yusif Mai tama, wanda gidauniyar ta shirya wa Mata, da bitar ta shafi watan Azumin Ramadana, akan yadda iyaye matan za su kula da ƴaƴan su, da ya gudana a ofishin ƙungiyar dake unguwar Sharaɗa a Kano.

Wakiliyar tashar Dala FM Kano, ta rawaito cewa malama Fatima Tsakuwa ta ce akwai buƙatar iyayen su ƙara lura da tarbiyyar ƴaƴansu, tare da yawaita karatun Al-kur’ani mai girma domin rabauta da falala a wajen Allah S.W.T.

Continue Reading

Trending