Labarai
Matasa sunyi aure ba tare da sanin iyayensu ba a Kano
An gurfanar da wasu matasa biyu da aka boye sunayensu mazauna yankin Kurna dake nan Kano, a gaban hukumar Hisbah ta jiha kan sunyi aure ba tare da sanin iyayensu ba.
Tunda farko dai matasan ne suka hangi yadda wasu mata da miji suke soyayya a yayinda suke wucewa ta gabansu, hakan yasa suka ga baza su iya jurewa ba, don haka suka nemi abokanansu kan suyi musu walicci wajen daura musu aure.
Hakan kuwa akayi inda a karshe abokanansu suka zama waliyan ango dana amarya aka kuma daura auren akan sadaki naira dubu ashirin, ango ya bada naira dubu biyu amarya kuma ta ranta masa naira dubu goma sha takwas.
Tsawon wata uku kenan da aka daura wannan aure, inda Ango da Amarya suke cigaba da mu’amalarsu a matsayin saurayi da budurwa, sai dai wani abin mamaki shi ne wannan aure har ya kai ga yanzu haka an samu rabo, domin kuwa amaryar tuni ta samu juna biyu.
Wakilinmu Ibrahim Abdullahi Soron Dinki ya nemi zantawa da ango da amarya amma danginsu suka ki amincewa.
Mataimakin babban Kwamandan hukumar Hisbah Malam Shehu Tasi’u Ishaq ya ce auren bai dauru ba tunda mahaifin yarinya yana nan a raye, amma ‘dan dake cikin amaryar idan an haifeshi ba za’a kirashi da ‘dan gaba da fatiha ba, suma kuma ba za’a kirasu da sunyi zina ba.
Kazalika Shehu Tasi’u yaja hankalin ma’auratan da suke fitowa fili suna soyayya, yace su sani kunya jigoce ta imani rashinta kuwa jigone na karancin imani, saboda haka yake jan kunne ga ma’aurata dasu rika kiyayewa, saboda rashin hakan kan jawo tabarbarewar tarbiyyar al’umma.
Idan zaku iya tunawa dai a watan Yulin da ya gabata ne akayi wata dambarwa kan wasu matasa da suka daura auren wasa a dandalin sada zumunta na Facebook wanda Hisbah da hukumomin shari’a a Kano suka sha alwashin daukar mataki akai.
Labarai masu alaka:
Baba Suda: Hisbah ta hana cakuduwar maza da mata a cikin babur mai kafa uku
Hisbah ta yiwa wasu ‘yan “Good Evening” ritaya
Labarai
Sarkin Kano Khalifa Muhammadu Sunusi na biyu, ya naɗa Ɗan Sa a matsayin Chiroman Kano.
Mai martaba sarkin Kano Dakta Khalifa Muhammadu Sunusi na biyu, ya buƙaci dukkanin hakimansa da ke faɗin jihar nan da su mayar da hankali wajen gudanar da aikin su bisa gaskiya da riƙon Amana.
Sarkin ya bayyana hakan ne a lokacin da ya naɗa DSP Aminu Lamiɗo Sunusi a matsayin Chiroman Kano, kuma babban ɗan fadar Sarki, yau Juma’a a fadar sa.
Khalifa Muhammadu Sunusi na biyu, ya ce ya naɗa DSP Aminu Lamiɗo Sunusi a matsayin Chiroman Kano, ne bisa cancanta da zuminci da kuma gogewarsa akan aikinsa na ƴan sanda, tare kuma da taimakawa al’umma da yake yi a koda yaushe.
Mai martaba sarkin ya kuma taya Chiroman Kano, murna bisa wannan naɗin da aka yi masa, tare da fatan zai zamo jakada na gari musamman wajen samar da cigaban Al’umma da kuma masarautar Kano.
Wakilinmu na masarautar Kano Shamsu Da’u Abdullahi ya rawaito cewa taron naɗin ya samu halartar gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf, da sarakunan gargajiya daga wasu daga cikin jahohin ƙasar nan.
Labarai
Za mu magance matsalolin da hukumar Hisbah ta Dala ke fuskanta – Shugaban ƙaramar hukumar Dala
Ƙaramar hukumar Dala ta ce za ta yi bakin ƙoƙarin ta wajen magance matsalolin da hukumar Hisbah ta ƙaramar hukumar Dala ke fuskanta, domin ƙara ƙarfafa musu gwiwa wajen gudanar da ayyukan al’umma.
Shugaban ƙaramar hukumar Suraj Ibrahim Imam ne ya bayyana hakan, a lokacin da jami’an hukumar Hisbah ta ƙaramar hukumar Dala, suka ziyarce shi a ofishinsa, domin taya shi murnar nasarar cin zaɓe da suka yi, tare da sanar dashi halin da hukumar Hisbar ke ciki a halin yanzu.
“Daga cikin ƙalubalen da zan yi ƙoƙarin magance wa akwai samar da ruwa da wutar lantarki da kuma samar wa hukumar kayan aiki, bisa yadda suke fama da rashin su, “in ji Suraj Imam”.
Shugaban ƙaramar hukumar ta Dala Sura ya kuma yi kira ga babban kwamandan hukumar Hisbah ta jihar Kano Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa, da ya ƙara kulawa da walwalar hukumar ta ƙaramar hukumar Dala bisa ƙalubalen da suke fuskanta.
Da yake nasa jawabin kwamandan hukumar Hisbah ta ƙaramar hukumar Dala Mallam Umar Bala Muhammad, ya ce sun ziyarci shugaban ƙaramar hukumar ne domin taya shi murnar nasarar cin zaɓe da kuma sanar da shi halin da hukumar ke ciki, domin haɗa ƙari da ƙarfe wajen magance ƙalubalen da suke fuskanta.
Wakiliyarmu Hadiza Balanti ta rawaito cewa Mallam Umar Bala ya kuma ƙara da cewa a shirye hukumar hisbar ta ƙaramar hukumar Dala take wajen gudanar da ayyukan al’umma babu gajiyawa.
Labarai
Mun dakatar da karɓar kuɗin haraji a Fagge har sai an kammala bincike – Shugaban Ƙaramar hukumar Fagge
Ƙaramar hukumar Fagge ta dakatar da dukkannin harkokin karɓar haraji har zuwa lokacin da za’a kammala bincike, don tabbatar da cewa bangaren harajin nayin aiki bisa doka domin ciyar da ƙaramar hukumar gaba.
Shugaban ƙaramar hukumar ta Fagge Salisu Usman Masu ne ya bayyana hakan yayin zantawar sa da tashar Dala FM Kano, a safiyar yau Talata.
Salisu Usman ya kuma bayyana cewar duk filotan da aka yanka aka sayar ko aka bayar ba bisa ƙa’ida ba shima an soki shi.
Shugaban ya kuma yi kira ga ƴan kwangila waɗanda suka watsar da ayyukan da aka basu da su dawo bakin aiki ka’in da na’in.
A cewar sa, “Na fahimci irin kalubalen da ke damun al’umma a ɓangaren lafiya a ƙaramar hukumar mu ta Fagge; kuma za mu yi ƙoƙarin samar da kayan aiki domin magance matsalar, “in ji shi”.
Masu ya kuma bayyana cewar ƙaramar hukumar ta Fagge za ta inganta harkar ilimi da tsaro, da Lafiya, inda kuma yi kira ga duk wani mai kaunar ci gaban karamar hukumar Fagge da ya taho a hada hannu ko da shawara zai bayar dan ciyar da karamar hukumar gaba.
-
Nishadi5 years ago
Ina neman mijin aure – Rayya
-
Labarai4 years ago
Hamisu Breaker ya kai kan sa wajen ‘yan sanda
-
Nishadi5 years ago
Mansura Isah ta yi kaca-kaca da Sadiya Haruna
-
Manyan Labarai5 years ago
KAROTA: An baiwa Baffa Babba wa’adin kwanaki bakwai
-
Labarai5 years ago
Auren dan Panshekara da ba Amurkiya ya samu cikas
-
Lafiya2 years ago
Rahoto: An gano wani gida da ake gini da takardun Kur’ani da Alluna
-
Manyan Labarai5 years ago
Sabuwar damfarar da ta fito a Kano
-
Nishadi5 years ago
An gano daliban da Adam Zango ya dauki nauyin karatun su