Connect with us

Labarai

Shigar matasa harkar noma zai rage zaman kashe wando- AFAN 

Published

on

Shugaban hadaddiyar kungiyar manoma ta Nijeriya wato (AFAN),  reshen jihar Kano, Faruk Rabi’u Mudi, ya bukaci masu hannu da shuni musamman ma a fadin jihar Kano da su rinka tallafawa gwamnati a bangaren baiwa matasa jari a kan harkokin noma, don kakkabe zaman kasha wando ga matasa a fadin Jihar Kano da ma kasar baki daya.

Faruk Mudi ya bayyana hakan ne, ya yin zantawarsa da gidan rediyon Dala a jiya Lahadi ta cikin shirin Noman Zamani.

Ya ce,” kasancewar matasan su ne kashin bayan cigaban kowace al’umma domin haka su na bukatar a tallafa ma su domin kaiwa ga gaci wanda ta haka ne za a rage rashin aikin yi da ke addabar matasan.”

Ya kuma kara da cewa,” masu kudi na da rawar takawa wajen zuba jari a shirin gwamnati na bunkasa harkar noman zamani tare da samarwa matasa ayyukan yi.”                                    

Wakilinmu Aminu Ahmad Abbas ya rawaito cewa, a watan Disambar shekarar da ta gabata ne, kungiyar ta AFAN ta bude sabon bankin manoma don ganin manoman sun tsaya da kafafunsu.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a Reply

Labarai

Sinadarin hada shayi ya haddasa asarar rayuka a Kano

Published

on

Tsohon daraktan ma’ikatan jinya a asibitin kwararru na Murtala Muhammad a jihar Kano, Yusuf Yakubu, ya ja hankalin al’umma da su kauracewa yin amfani da kayayyakin da wa’adin su ya kare wato dameji.

Jami’in lafiyar ya bayyana hakan ne, lokacin da ya ke tsokaci tare da bayyana alhinin sa a kan yadda ake zargin kananan ‘ya’yansa sun sha wani sinadarin hada shayi kalar makuba wanda ake amfani da shi a shayi yau da kullum.

Yusuf Yakubu, ya ce “Ta sanadiyar shan sinadarin suka rasa ransu wanda wa’adin amfani da shi yak are, kuma suna shan garin cikin su ya rinka kadawa su hudu a lokacin. Mun yi kokarin kai su asibiti biyu sun mutu daga cikin su”.

Wakilin mu Ibrahim Abdullahi Sorondinki ya rawaito mana cewa, masanin lafiyar ya kuma shawarci mahukunta da su kara kaimai wajen dakile samuwar irin wadannan kayayyaki a kasuwanni.

Continue Reading

Labarai

Rashin tsaro barayi sun takura mana a Ja’en –Kungiyar Zumunta

Published

on

Shugaban Kungiyar Zumunta da take a unguwar Ja’en cikin karamar hukumar Gwale a jihar Kano, Abubakar Muhammad, ya yi kira ga gwamnatin jihar Kano da ta shiga tsakanin ‘yan Bijilantin yankin, domin su dawo da aikin sintiri kamar yadda suka saba a baya.

Abubakar Muhammad ya yi kiran ne, a ya yin ganawarsa da gidan rediyon Dala.

Ya na mai cewa” Tun bayan da ‘yan Bijilantin yankin suka dakatar da aikin su a unguwar ta Ja’en mu ke fama da yawan sace-sace daga wasu bata gari ba tare da kakkautawa ba, sabida haka dole sai gwamnati ta shigo cikin lamarin mu. Kuma Kungiyarsu mu ta Zumunta ta yi iya bakin kokarin ta wajen ganin ‘yan Vijilanten sun dawo aikin su ka’in da na’in, amma basu samu nasarar hakan ba, saboda hakan ne ma mu ke bukatar gwamnatin Kano da Kwamishinan ‘yansandan jihar Kano da su kawo ma na dauki”.

Wakilin mu Hassan Mamuda Ya’u ya rawaito cewa, shugaban Kungiyar Abubakar Muhammad, ya kuma bukaci al’ummar garin na Ja’en, da su baiwa yan kungiyar Sintirin hadin kan da ya dace musamman ma idan suka dawo bakin aikin su a yankin domin kara karfafa mu su gwiwa.

Continue Reading

Labarai

Tsofaffi tukuf sun koma makarantar islamiyya a Kano

Published

on

Wasu iyaye tsofaffi ‘yan kimanin shekaru 70 zuwa 80 sun bayyana cewa da su yi yawo zuwa gidan makwabta ko kuma a cikin unguwanni sun gwammace su koma su koyi karatun al’kurani mai girma.

Tsofaffin sun tabbatar da hakan ne a yayin saukar karatu na makarantar Khalid Bin Walid, dake unguwar Ja’en Shago Tara a karamar hukumar Kumbotso a jihar Kano.

Guda daga cikin wata tsohuwa mai shekaru 70 da haihuwa mai suna Rabi Abdullahi, ta ce” Da na tafi ina yawo a unguwa yafi in koma makaranta na samu ilimi sabida ilimi shi ne rayuwar mutum har lahira, su kuma tsofaffi irina su koma makaranta domin samin rabo”.

Ita kuwa Zainab Adamu mai shekaru 60 ta ce” Da in rinka yawon shige da fice a unguwa yafi na koma makaranta sabida ba dadi yawo haka kawai ba ilimi”.

Maryam Alhassan mai shekaru 75 cewa ta yi” Yafi in rinka yin tilawa maimakon zama kai babu komai sabida yanzu haka zan iya karatun al’kurani da hadisi da kuma al’azkar”.

Hajara Sa’adu mai shekaru 80 ta ce” gashi har shaidar karatu aka bamu na girmamawa sabida mun koma makaranta ko daga nan ai mun ci riba”.

Shi kuwa shugaban makarantar, Mustapha Abba Abdulsalam ya ce” Wannan saukar ta zo da wani sabani sakamakon iyaye dattijawa sun mayar da kai wajan neman ilimin Al’kurani mai girma, kuma ina kira ga matasa su mayar dakai wajen neman ilimi”.

Wakiliyar mu Aisha Ibrahim Abdul ta rawaito cewa dalibai (38) ne suka yi sauka a makarantar ta Khalid Bin Walid, ciki kuwa akwai matan aure biyar da maza biyar tare da kuma samari maza da mata (28).

Continue Reading

Trending

error: Content is protected !!
en_USEnglish
en_USEnglish