Connect with us

Manyan Labarai

Pillars ta yi kunnen doki a jihar Katsina

Published

on

Kungiyar Kwallon kafa ta Kano Pillars ta ya yi kunnen doki daya da daya da abokiyar hamayyar ta ta Katsina United a gasar cin kofin kwarru ta kasa wato (NPFL).

Dan wasan Kano Pillars, Seun Adelani Yusuf ne ya fara zura kwallo a minti 34 na zagayen farko daga baya kuma dan wasan Katsina United Tasiu Lawal ya farke kwallon a daf da a tafi hutun rabin lokaci wato minyi 44.

Yanzu haka Pillars na mataki na 13 da maki 17 yayin da Lobi Stars take matsayi na daya da maki 27 a wasa 14 da ta yi.

Kano Pillars za ta yi wasan ta na gaba da Akwa United

Ga ragowar wasannin da aka buga a yau.

Adamawa Utd 0-0 Wikki

MFM 2-1 Jigawa GS

Joshua Akpudje 41’, 69’ – Joshua Akpudje 30’ (OG)

Enyimba 0-2 Heartland

Sadiq Abubakar 30’, Chukwuemeka Obioma 45+1’

Sunshine Stars 2-1 Plateau Utd

Timileyin Ogunniyi 11’, Fuad Ekelojuoti 33’ – Uche Onwuasoanya 57’

Rivers Utd 1-1 Lobi Stars

Nelson Esor 2’ , Malachi Ohawume 75′ – John Lazarus 19’

Katsina Utd 1-1 Kano Pillars

Abia Warriors 2-1 FC Ifeanyiubah

Lukman Bello 28’, Yakub Hammed 75’ – Jimoh Gbadamosi 55’ (PEN)

Wolves 1-2 Rangers

Charles Atsemene 41’ – Kelvin Itoya 3’, Kenechukwu Agu 14’

Akwa Utd 0-2 Kwara Utd

Alao Dambani 26′ 49′

Manyan Labarai

Gididdiba burtalan garuruwan mu da akayi ka iya haifar mana da barazana – Fulani mazauna ƙaramar hukumar Tofa

Published

on

Fulani Makiyaya na garuruwan Yanoko, da Gajida, da kuma garin Dindere da ke ƙaramar hukumar Tofa, sun koka tare da neman ɗaukin mahukunta, bisa yadda suka ce sun wayi gari da ganin wasu mutane tare da yanka burtalan garuruwan su,

Fulanin sun ce zargi ya nuna yadda aka godiddiba burtalan inda aka siyarwa da wasu shafaffu da mai, lamarin da suka ce hakan babbar barazana ce a gare su, kasancewar babu wajen da za suyi kiwon shanun su.

A zantawar Dala FM Kano, da shugaban ƙungiyar Fulani Makiyaya reshen ƙaramar hukumar Tofa, ta Gan Allah, Mallam Ahmad Shehu, ya ce gididdiba burtalan ka iya haifar musu da gagarumar matsala a rayuwa, a dan haka ne ma suke kira ga gwamnatin Kano da ta kawo musu ɗauki.

Alhaji Mamuda mazaunin Dawakin Tofa, na ɗaya daga cikin waɗanda aka yankarwa burtalin a yankin Dindere, aka kuma siyar masa, ya ce wasu ne suka siyar masa kuma an bashi takarda hakan ya sa har ya fara aiki a wajen

Wakilin dagacin garin Dindere Isah Sulaiman ya ce, lamarin yaje ga ofishin hakimin Tofa, a dan haka ne muka zanta da Turakin Tofa, Alhaji Sunusi Abubakar Tofa, kuma wakilin Makaman Bichi hakimin Tofa Alhaji Dakta Isyaku Umar Tofa, ya ce sun san da al’amarin ana ci gaba da ɗaukar mataki, kuma masarautar yankin bata bai wa kowa damar yankar burtalin ba, ko da kuwa mai unguwar Yalwal Rimi da ke garin Dindere da akace shima ya yanki burtalin.

Al’amarin gididdiba burtalin dai wasu sun danganta shi da shugabancin ƙaramar hukumar Tofa mai ci a yanzu, a dan haka ne muka yi duk mai yiyuwa wajen ji daga shugaban riƙo na ƙaramar hukumar Abubakar Sulaiman Mai Goro, sai dai bai samu damar ɗaga wayar mu ba, kuma mun aike masa da saƙon karta kwana sai dai har wannan lokaci ba muji daga gareshi ba.

Continue Reading

Manyan Labarai

Bama goyon bayan ƙirƙiro ƴan sandan jahohi dan ba zai haifar da Ɗa mai ido ba a ƙasa – Human Rights

Published

on

Ƙungiyar kare haƙƙin ɗan adam ta Universal Declaration of Human Rights, ta ce akwai buƙatar duba na tsanaki gabanin sahale ƙirƙirar ƴan sandan jahohi, domin gujewa abinda ka je ya dawo.

Daraktan ƙungiyar a nan Kano Kwamared Umar Sani Galadanci, ne ya bayyana hakan yayin zantawar sa da gidan rediyon Dala FM, a yau Talata.

Galadanci, ya kuma ce duba da a mafi yawan lokuta ake samun baragurbi a harkar samar da taro, kamata ya yi a wadata jami’an tsaron da ake da su da kayan aiki na zamani, ta yadda za’a ƙara musu Gwiwa akan aikin su.

“A ɓangaren ƙungiyar mu bama goyon bayan samar da ƴan sandan jahohi, domin hakan ka iya haifar da koma baya; kuma ba zai haifar da Ɗa mai ido ba a sassan ƙasar nan, “in ji shi”.

Wakilinmu Hassan Mamuda Ya’u ya rawaito cewa Kwamared Umar Sani Galadanci, ya ƙara da cewa akwai buƙatar gwamnatin tarayya da ta jahohi, su kula da al’ummar su tare da samar musu kayayyakin more rayuwa, dan rayuwar su ta tafi yadda ya kamata.

Continue Reading

Manyan Labarai

Mutane uku sun rasu yayin ciro Waya a cikin Masai da ceto mutum ɗaya a Kano – Hukumar Kashe Gobara 

Published

on

Hukumar kashe Gobara ta jihar Kano, ta tabbatar da mutuwar wasu mutane uku, ciki har da Uba ɗan sa, a unguwar Ƴar Gwanda da ke ƙaramar hukumar Tsanyawa a jihar Kano.

Jami’in hulɗa da jama’a na hukumar kashe gobarar PFS Saminu Yusuf Abdullahi, ne ya bayyanawa gidan rediyon Dala FM, faruwar lamarin a daren jiya Lahadi.

Tunda fari dai mutum na farko mai suna Mallam Ɗan Juma mai laƙabin Black, wayar sa ce ta faɗa a cikin Masai, ya shiga domin ya cirota, sai dai gaza fitowar sa ke da wuya sauran mutane ukun suka bishi domin ceto shi lamarin da suma suka gaza fitowa.

Sauran mutane ukun akwai ɗan mutumin mai suna Ibrahim Ɗan Juma mai shekaru 35, sai na ukun mai suna Aminu T Gaye, da na huɗu mai suna Abbas Alhassan, ɗan shekara 28, amma shi an ciroshi a raye.

PSF Saminu Yusuf, ya kuma ce bayan faruwar lamarin ne jami’an su, suka ceto mutum na ƙarshe a raye, amma ukun farko basa cikin hayyacin su baki daya.

Ya ƙara da cewa tuni jami’an nasu suka miƙa mutanen a hannun jami’in hukumar ƴan Sanda, kuma babban baturen ƴan sanda da ke ƙaramar hukumar Tsanyawa a Kano mai suna SP Ibrahim Lado, inda suka kai su asibitin ƙwararru na ƙaramar hukumar Tsanyawa a Kano.

Continue Reading

Trending