Connect with us

Wasanni

Magoya bayan Pillars 40 aka raunata a jihar Katsina –Bashir mu’azu Jide

Published

on

Shugaban magoya bayan kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars, Bashir Mu’azu Jide, ya tabbatarwa mana da cewa magoya bayan Pillars mutane (40) ne suka jikata a farmakin da magoya bayan kwallon kafa ta jihar Katsina suka yi masu bayan kamala wasan da suka yi kunnen doki daya da daya da Katsina United.

Bashir Mu’azu Jide, ya tabbatarwa da Dala Fm a zantawar sa ta wayar tarho da muka yi da shi.

Ya ce “Abun da ya faru a tarihin haduwar Pillars da Katsina United ba a taba ganin irin jikata magoya bayan dukannin kungiyoyin ba kamar yadda suka yi wa Pillars duk da irin zaman da aka yi har sau biyu a tsakanin juna gudun ka da a sami yamutsi. Kawai dai yanzu hukumar LMC muke jira mu ji hukuncin da za a yi wa Katsina United kuma mutanen mu wanda aka jikata suka ji babban ciwo sun kai mutane 40 ban san adadin wadan da ba su je asibiti ba”.

Ko ya ka ke kallon wannan batun cewa wasu daga cikin magoya bayan Pillars sun ce za su rama mudin suka zo Kano?

Sai ya ce “Gaskiya doka ya na hannun hukumar shirya wasanni LMC sabida haka magoya bayan mu ba za su dauki doka a hannun su ba sakamakon mun barwa Allah lamarin. Kuma muna kara kiran magoya bayan mu da su yi hakuri kada su ce za su dauki mataki a hannun su”. A cewar BashirJide.

 

 

 

Wasanni

Bayer Leverkusen ta zama zakarar gasar Bundesliga ta 2023/2024.

Published

on

Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Bayer Leverkusen ta zama zakarar gasar Bundesliga ta shekarar 2023/2024, bayan da suka samu nasara a kan Weder Bremen da ci 5-0.

Hakan ne kuma ya kawo ƙarshen shekaru 11 da Bayern Munich, da ta yi tana lashe gasar.

Wannan dai shi ne karo na farko da Bayer Leverkusen suka taɓa lashe gasar a tarihi, ida suka gaza ɗaukar kofin a shekarar 2002 a ranar ƙarshe ta gasar.

Har ila yau, a dai wannan shekarar ne su kayi rashin nasara hannun Shalke 04, a wasan ƙarshe na German Cup Da ci 4-2.

Haka kuma, Real Madrid suka doke su a wasan ƙarshe na zakarun nahiyar turai.

Rahotanni sun bayyana cewa ƙungiyar bata taɓa ɗaukar wata gasa ba a ƙarni na 21, sai bayan da Xavi Alonso ya karɓe su.

Continue Reading

Wasanni

Hukumar NPFL, ta amince da buƙatar Kano Pillars na ɗage wasan ta na mako na 28 da Enyimba

Published

on

Yanzu haka an samu dai-daito da hukumar NPFL, wanda ta amince da bukatar Kano Pillars na dage wasanta na mako na 28, da Enyimba zuwa ranar Alhamis, mai zuwa.

Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Kano Pillars, ce ta wallafa hakan a shafin ta na Facebook da yammacin Litinin ɗin nan, ta ce ƴan wasan ta za su tashi a gobe Talata, da safe zuwa Aba domin fafata wasannin su.

Idan dai ba’a manta ba ƙungiyar ta wallafa kaɗan daga irin ƙalubalen da take fuskanta a harkokin gudanarwar ta.

Pillars, ta wallafa ƙalubalen ne kamar haka, “A yanzu haka zancan da muke muku Kano Pillars ta rasa kudin da za taje garin Aba, domin buga wasan hamayya na Nigeria Premier league wato Zobia Classic”.

Wasan dai shine wasa mafi ɗaukar hankali a league din Nigeria baki ɗaya, ku taya mu yadawa dan Allah.

Continue Reading

Wasanni

Glesner ya zama sabon mai horas da Palace.

Published

on

Kungiyar kwallon kafa ta Crystal Palace ta sanar da nadin Oliver Glesner a matsayin sabon mai horaswar ta.

Glesner wanda tsohon mai horas da kungiyar kwallon kafa ta Eintracht Frankfurt ne mai shekaru 49 dan asalin kasar Austrian, ya maye gurbin tsohon mai horaswa Roy Hodson, wanda ake ganin ya gaza kai kungiyar ga tudun mun tsira.

A wasanni 16 da Crystal Palace ta buga a bayan nan ta yi rashin nasara a wasanni 10 duk karkashin jagorancin Roy Hodson wanda hakan yasa take mataki na 16 a teburin gasar firimiyar kasar Ingila.

Glesner dai ya rattaba kwantaragi da Palace har na tsawon shekaru biyu, zai kuma jagoranci kungiyar a wasan sa na farko da kungiyar kwallon kafa ta Burnley a ranar Asabar mai kamawa.

Continue Reading

Trending