Connect with us

Labarai

Rashin sanin hakkin aure ke haifar da mutuwar aure a Kano –Dr Nasir Kankarofi

Published

on

Abun da ya ke jawo tasgaro a rayuwar aure shi ne watsi da hakkin aure tsakanin mace da miji shi ne babban kalubale a zamantakewar aure.

Dr Nasir Tijjani Kankarofi, wanda ya tabbatar da hakan jim kadan bayan kamala sallar juma’a wanda ya gudanar da hudubar sa a masallacin Juma’a na tashar jirgin Kasa wato Railway dake karamar hukumar Nasarawa a jihar Kano.

Daga cikin hakokin auren shi ne “ mace wajibi ne ta yi wa mijin ta biyayya ta zama a kasan sa ta ke matukar bai umarce  ta da sabon Allah ba, shi kuma ka da mijin ya zama mai jin izza  mai jin girma kada ya yi mata mulkin kama karya, tun da mun ji manzon Allah (S.A.W) lokacin Hudebiyya ya yi shawara da matar sa Nana Umul Salama, cewa idan za ta yi azumin nafula sai ta fada masa in ya yarda za ta yi in bai yarda ba, ba za ta yi ba”. Inji Dr Tijjani.

Ko akwai sharadi da musulunci ya gindaya cewa idan mace ko na miji zai yi aure sai ya nemi wani ilimi na aurataya?

“A akwai tun da musulunci bai yadda da zaman jahilci ba, Allah ya na cewa kusan ni kafin ku bauta min, to ya na da kyau a san me ne ne aure kafin yin aure, wannan abu ne da zai kawo kyakkawan yanayi da rayuwa ta aure ta soyayya da jin kai kamar yadda musulunci ya shimfida”.

Rashin sanin me ne ne auren ya na haifar da matsaloli?

“Ya na haifar da matsaloli kwarai da gaske, yawancin irin wannan matsaloli da a ke samu kala-kala rashin sanin auren ne, domin kuwa a na gina rayuwar aure a kan son duniya ne wani ya na ganin kyau ba ruwan sa da nagarta mace kudi kawai ta ke kallo ba ruwan ta da nagarta, musulunci bai haramta ma ka ba, amma ana son ya zama tushe da jin tsoron Allah. Kuma ya kamata a rinka yi wa duk wanda za su yi aure bita domin samar da aure mai jin kai da biyayya mai daure wa”. Inji Dr Nasir Tijjani Kankarofi.

Tattaunawar limamin da wakilin mu Abba Isah Muhammad jim kadan bayan kamala sallar juma’ar.

Labarai

Shugabanni ku fito da sabbin dabaru domin kawo ƙarshen matsalar tsaro da ta tsadar rayuwa a ƙasa – Human Rights

Published

on

Ƙungiyar kare haƙƙin ɗan adam ta Universal Declaration of Human Rights dake jihar Kano, ta ce akwai buƙatar shugabanni suyi abinda ya dace dan ganin an kawo karshen matsalar tsaro, da kuma ta harkar tsaro dake ci gaba da addabar mutane a sassa ƙasar nan.

Daraktan ƙungiyar Kwamared Umar Sani Galadanci, ne ya bayyana hakan yayin zantwarsa da gidan rediyon Dala FM, a ranar Laraba, ya ce yadda ake ƙara samun ƴan ta’adda suna sace mutane tare da kashe su a sassan ƙasar nan, da kuma halin matsin rayuwar da ake fuskanta akwai buƙatar shugabanni suyi abinda ya kamata dan ganin an kawo ƙarshen matsalolin.

“Yawaitar kai hare-haren da ake samu daga ɓangaren ƴan bindiga a cikin al’ummar gari akan kashe su tare da sace su matuƙar ana son a kawo karshen matsalar, sai an ƙara himma wajen samar da makamai ga jami’an tsaro tare da samar da sabbin dabaru domin kawar da matsalar, “in ji Galadanci”.

Wannan dai na zuwa ne kwanaki kaɗan da sako ɗalibai aƙalla su sama da 285, na makarantar Kuriga dake ƙaramar hukumar Chikun ta jihar Kaduna, da ƴan bindiga suka sace su a baya, baya ga wasu ɗaliban da aka sace a wata makarantar Tsangaya a jihar ta Kaduna, wanda ko a jihar Borno ma aka jiyo yadda aka sace ƴan gudun hijira da dama a baya-bayan nan, inda matsalolin tsaron ke ƙara yin gaba a sassan ƙasar nan.

Continue Reading

Labarai

Gwamnan Kano ya kafa kwamitin duba yadda ake rabon tallafin abincin Azumi

Published

on

Gwamnatin Kano ta kafa kwamitin duba yadda ake ciyarwar azumin watan Ramadan, a kananan hokumomin cikin birnin jihar 8, domin sa ido da duba yadda ake gudanar da aikin dafawa da rabawa al’umma abincin.

Gwamnan Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf, ya kafa kwamitin ne ƙarƙashin kulawar mataimakin gwamnan Kano Kwamared Aminu Abdulsalam Gwarzo, da wasu ƴan kwamitin.

Hakan na zuwa ne dai bayan da gwamna Abba Kabir, ya ziyarci wasu daga cikin wuraren da ake dafa abincin, inda ya nuna rashin jin daɗin sa kan yadda ya ga aikin ke gudana a karamar hukumar kumbotso.

Bayanin hakan ya fito ne ta cikin wata sanarwar da babban mai taimakawa gwamnan Kano, na musamman akan gidajen rediyo Bashir Aminu Fanshekara, ya aikowa manema labarai, ya ce an bayyana Alhaji Danyaro Yakasai, a matsayin wanda zai jagoranci kwamitin mai mambobi 7.

Fanshekara ya ce kwamitin ya fara zagayawa wasu daga cikin mazaɓu dake karamar hukumar kumbotso, domin duba yadda ake dafawa da kuma raba abincin tallafin ga al’umma, inda suka suka fara da mazaɓar Na’ibawa a ranar Asabar 23 ga watan Maris ɗin shekarar 2024.

Continue Reading

Ilimi

Kaduna:- Daliban Kuriga sun sha ki iskar ‘yanci

Published

on

Gwamnatin jihar Kaduna ta bayar da rahoton cewa an sako duka ɗaliban makarantar Kuriga da ƴanbindiga suka sace.

 

An sace ɗaliban firamare da na sakandare su kusan 287 a makarantarsu da ke ƙauyen Kuriga a karamar hukumar Chikun ta jihar Kaduna fiye da makonni biyu da suka wuce.

 

Sanarwar da gwamnan jihar Kaduna, Sanata Uba Sani ya fitar ta ce an sako duka ɗaliban kuma suna cikin koshin lafiya.

 

Sanarwar ba tayi karin bayani ba game da irin matakan da aka bi wajen sako ɗaliban, sai dai gwamna Uba Sani ya nuna godiya ga shugaba Tinubu da mai bashi shawara kan tsaro da kuma sojojin Najeriya saboda irin rawar da suka taka wajen ganin an sako ɗaliban.

 

“Ba dare babu rana ina tattaunawa da Malam Nuhu Ribadu domin lalubo hanyoyin da za a bi wajen kubutar da daliban, kafin mu samu nasara,” in ji Uba Sani.

 

Galibinsu ɗaliban da aka sace ƴan shekaru biyar ne zuwa 18.

Continue Reading

Trending