Connect with us

Manyan Labarai

Duk shekara za mu ya ye matasa dubu 15 -Sha’aban Sharada

Published

on

Mai wakiltar karamar hukumar birni a majalisar wakilai ta tarayya, Sha’aban Ibrahim Sharada, ya sha alwashin ya ye matasa dubu 15,000 a duk shekara.

Sha’aban Ibrahim Sharada ya tabbatar da hakan ne a ya yin da ya ke gabatar da daliban da ya dauki nauyin su karatu zuwa kasar waje.

Sha’aban ya ce” Zai koyawa matasan sana’ao’in dogaro dakai kuma kowa za a bas u kayan aikin su a hannu a irin sana’ar da suka koya. Kuma za a gina wurin koyon sana’o’in dogaro dakai wanda al’ummar jihar Kano za su amfana baki daya”.

Ya kuma ce”Daliban za su yi karatu ne a jami’ar Afrikiya ta Khartoum kuma yanzu haka an biya ma su kudin karatun sun a wannan shekarar da ma shekara mai zuwa, sakamakon yawancin dalibai suna fuskantar rashin biya ma su kudin karatu shi ya san a yi mu su wannan dabarar domin ganin ba bu bashin ko da Naira guda a kan daliban”. Inji Sha’aban

A nasa jawabin gwamnan Kano, Dr Abdullahi Umar Ganduje, ya yabawa Sha’aban Ibrahim Sharada sakamakon ayyukan da ya dauka na tallafawa matasa da sana’o’in dogaro da kai da kuma daukar nauyin karatun su zuwa kasar waje.

Ya ce “haka ake bukatar wakilci na gari a majalisa kuma a ce duk wani dan majalisa idan ya tafi majalisa ya rinka yin irin wadannan ayyukan alherin tabbas da hakan za a rage rashin yin aiki a tsakankanin matasa”. Inji Ganduje

Sanarwar mai kunshe da sa hannun Farouk Mallami Sharada, mashawarci na musamman ga Sha’aban Ibrahim Sharada, ta rawaito cewa tuni kaso na farko  na daliban suka tafi kasar Sudan domin yin karatun su zangon farko.

 

 

Manyan Labarai

Za’a ɗauki mataki akan duk wanda yake da hannu Gini ya ruftawa mutane a Kuntau – Ƙaramar hukumar Gwale.

Published

on

Yayin da wani ginin Bene mai hawa biyu ya danne aƙalla sama da Leburori goma a unguwar Kuntau kusa da KEDCO, a safiyar yau Juma’a, Shugaban riƙo na ƙaramar hukumar Gwale Abubakar Mu’azu Mojo, ya ce za’a ɗauki mataki akan dukkan wanda aka samu da laifi har al’amarin ya faru.

Abubakar Mu’azu Mojo, ya bayyana hakan ne yayin zantawar sa da manema labarai, yayin da ya ziyarci gurin da lamarin ya faru lokacin da ake ci gaba da aikin ceto mutanen.

Mojo, ya kuma ce babu makawa za’a ɗauki matakin doka akan duk wanda aka samu da hannu akan faruwar lamarin, kama daga ɗan kwangilar da aka bai wa aikin ginin, zuwa kuma mamallakin gidan.

Rahotanni sun bayyana cewa zuwa tsakar ranar yau aƙalla mutane bakwa aka ciro daga ƙasan ginin shida daga cikin su basa iya motsa jikin su, yayin da hukumomi suka ci gaba da gudanar da aikin ceto sauran mutanen da ginin ya danne.

Continue Reading

Manyan Labarai

Sulhu da ƴan Bindiga ba zai haifar da Ɗa mai ido ba – Human Rights 

Published

on

Ƙungiyar kare haƙƙin ɗan adam ta ƙasa da ƙasa wato International Human Rights Commission, ta ce sulhu da ƴan bindiga ba zai haifar da Ɗa mai ido ba a ƙasar nan.

Babban daraktan ƙungiyar Kyaftin Abdullahi Bakoji Adamu mai ritaya, shi ne ya bayyana hakan yayin zantawar sa da gidan rediyon Dala FM Kano.

Ya ce kasancewar ƴan bindigar basu da wata manufa bai kamata ayi sulhu da su ba, mai-makon hakan yafi dacewa a rinƙa ɗaukar tsauttsauran mataki akan su duba da yadda suke cutar da al’umma.

Ya kuma ce batun da mai bai wa shugaban ƙasa akan sha’anin tsaro Malam Nuhu Ribaɗo, ya yi a baya baya nan, kam cewar an fara samun fashimtar juna da wasu daga cikin ƴan Bindigar da suka addabi mutane a sassan ƙasar nan, a wani ɓangare ma kama da yin sulhu da su, ya faɗi hakan ne kawai amma hakan ba zai haifar da Ɗa mai ido ba.

Continue Reading

Manyan Labarai

Gwamnatin Kano ta kulle wata makaranta mai zaman kan ta a jihar

Published

on

Gwamnatin jihar Kano ta rufe wata makaranta mai suna Golden Crown International School a jihar, da ke yankin Sabon gari, bisa zargin an fake da sunan makarantar ana haɗa magani mara inganci mai-makon koyar da karatu a ciki.

Shugaban kwamitin yaki da miyagun ƙwayoyi da ƙwacen waya na jihar Kano General Gambo Mai Aduwa Mai ritaya, ne ya bayyana hakan, a lokacin da Kwamitin ya kai wani sumame da karfe uku da rabi na daren jiya Talata.

Rahotanni sun bayyana cewa makarantar tana kan titin Zungero da ke cikin ƙaramar hukumar Fagge a jihar Kano, wanda bayan samun bayanan sirri aka ɗauki matakin kulle ta.

Mai Aduwa, ya ƙara da cewar tsarin gurin ta waje ya nuna makaranta ce amma kuma sai ake sarrafa magani da ake zargin ingancin sa da bai kai yadda ya kamata ba, tare da ajiye Allurai da kayan haɗa magani cikin ajujuwan mai-makon ɗalibai.

“Za mu faɗaɗa bincike akan al’amarin dan sanin matakin da za mu ɗauka na gaba, “in ji shi”.

Suma masu gadin gurin da muka zanta da su sun bayana cewar, aikin gadi kawai suke yi amma basu da masaniyar abubuwan dake gudana a cikin makarantar, da ake zargin ana sarrafa magani mara ingani da ajiye shi a muhalin da ake zargin bai yi dai-dai da tsarin doka ba.

Wakilinmu Abba Isah Muhammad ya rawaito cewa shugaban kwamitin ya ce, zai ci gaba da bibiyar guraren dake yin abubuwan da za su kawo koma baya ga harkokin lafiya, da ci gaban jihar Kano, musmman wajen yaƙi da miyagun ƙwayoyi da ƙwacen waya.

Continue Reading

Trending