Connect with us

Manyan Labarai

Kano -Mun kama dansandan da ake zargin ya yi amfani da Dattijuwa  –DSP Abdullahi

Published

on

Kakakin Rundunar Yansandan jihar Kano, DSP Abdullahi Haruna, ya bayyana cewar tuni sun kamo dansandan da wata Dattijuwa a karamar hukumar Dambatta ta yi korafin kan cewa ya yi mata fyade lokacin da aka tsare ta a kan bashi a ofishin ‘yansandan dake yankin.

A zantawar matar da Wakilin mu Abubakar Sabo, ta ce”Dansandan ya ne me ni a lokacin na bukaci zan kewaya domin yin fitsari inda a nan ne dansandan  ya yi min rakiya bayan na kamala biyan bukata ta sai ya ce in tabashi hadin kai ko kuma ya umarci alkali ya yanke min hukuncin rayuwa a gidan ajiya da gyaran hali wato daurin rai da rai, sai na amince da bukatar ta sa nan ta ke ya yi amfani da karfi wajen haike min”. Inji Dattijuwar

Kakakain rundunar, DSP Abdullahi Haruna, ya kuma tabbatar da cewa dansandan da ake zarggin aikata lafin ya na hannun su kuma su na gudanar da bincike dazarar sun kamala zai girbi abun da ya shuka.

Labarai

Rahoto: hukumar NDLEA na hukunta duk jami’in ta da ya yi laifi – Dakta Ibrahim Abdul

Published

on

Kwamandan hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi NDLEA, ta kasa reshen jihar Kano, Dakta Ibrahim Abdul ya ce, duk lokacin da ya samu daya daga cikin ma’aikatan su ya yi laifi, ya na hanzarin daukar matakin kora ko kuma hukuncin da ya dace.

Dakta Ibrahim Abdul ya bayyana hakan ne a zantawar sa da wakilin mu Abba Isah Muhammad, lokacin da yake mayar da martani a kan matasan da a ke zargin sun fada ruwan kududdufi lokacin da hukumar ta NDLEA ta kai simame yankin Dan Agundi da ke jihar Kano.

 

Domin jin cikakken rahoton saurari wannan

Continue Reading

Labarai

Rahoto: Matasa 2 sun gurfana a kotu kan zargin raunata jami’an KAROTA 3

Published

on

Kotu mai lamba 47, da ke rukunin kotunan majistret a unguwar Gyadi-gyadi, karkashin mai shari’a Huda Haruna Abdu, wasu matasa biyu Yunusa Sunusi da kuma Muhammad Babagana, sun gurfana a kotun da tuhumar a kan yi wa wasu jami’an hukumar KAROTA rotse, da suka hada da Usamatu Abdullahi da Sulaiman Musa da kuma Abdulkadir Isma’il.

Ana tuhumar matasan da laifuka guda uku, laifin hada baki da cin zarafi da kuma haddasa mummunan rauni, laifukan da suka saba da sashi na 93 da sashi na 264, sai kuma 247 na kundin laifuka, bayan kuma an karanta musu kunshin tuhumar zargin da a ke yi musu duk sun musanta.

 

Continue Reading

Labarai

Rahoto: Kotu ta fara sauraren shari’ar matar da a ke zargi da kazafin maita

Published

on

Wata mata ta gurfana a babbar kotun shari’ar musulunci da ke Kofar Kudu, karkashin mai shari’a Ibrahim Sarki Yola a kan zargin bin gari tana yada labarin cewa makwabciyarta da ‘ya’yanta duk mayu ne.

Tun da fari dai matar da a ke zargi da maitar, ta garzaya ofishin ‘yan sanda, tana karar makwabciyar tata, daga bisani kuma ‘yan sanda su ka tattara bayanai su ka mika su kotu domin fara sauraran shari’ar, bayan kuma karantawa matar mai yada labarin maita kunshin tuhumar ta musanta, inda kotu ta dage sauraren shari’ar.

Domin jin cikakken rahoton saurari wannan.

 

Continue Reading

Trending

error: Content is protected !!