Connect with us

Labarai

Jami’an lafiya na tsangwamar marasa lafiya a Kano -NHW

Published

on

A binciken da kungiya lura da harkokin lafiya ta kasa (Nigerian Health Watch) ta gudanar ta ce a asibitocin hukumar lafiya a matakin farko na kananan hukumomi 44 dake jihar Kano, jami’an lafiya na tsangwamar marasa lafiya.

Tawagar shugaban binciken kungiyar, Dr Bashar Abubakar ne, ya tabbatar da hakan a yayin taron da kungiyar ta gabatar tare da masu ruwa da tsaki a jihar Kano yau Talata.

Ya ce” Mun gudanar da binciken mu a kowane kananan asibitoci guda daya na kananan hukumomi 44 na jihar Kano wato (Primary Health Care), kuma aikin mu shine mu duba lafiyar asibitocin da tsaftar sa da kyaun asibitin da kuma isassun ma’aikata da magunguna, sannan mun gano cewa sama kashi 90 na asibitocin suna bada rigakafi yadda ya kamata, amma mun fahimci cewa a cikin mata 600 da suke zuwa awo amma a kalla mata 20 ne suke zuwa haihuwa kaga wannan babbar matsala ce, sabida mun fahimci cewa ma’aikatan lafiyar na yi wa marasa lafiyan tsawa da hantara kamar yadda muka tabbatar”.

Dr Bashar ya kuma ce” Kamata ya yi gwamnati ta shigo cikin lamarin domin wayar da ma’aikatan lafiya kan yadda ma’aikatan za su ke mu’amala da marasa lafiya ba tare da an tsangwama masu ba, domin in ba marasa lafiya ba ma amfanin karatun da za ka yi, ka ga dole sai da mutane za ka zo ka yi aiki kuma cikin mutunci da darajasu. Su kuma marasa lafiya musamman ma masu ciki da su rinka zuwa asibitoci domin a duba lafiyar su tare da ganin sun haihu cikin lafiya sabida haihuwar a asibiti yafi alheri akwai muhimmanci”.

Shi kuwa shugaban hukumar lafiya a matakin farko, Dr Tijjani Husaini, ya ce” Kalubale bangare ne na rayuwa amma yadda ake cimma sa a bibiya a gani da gyara an kuma dauki matakin gyara, kuma za mu ci gaba da bibiya mun dauki alkawari tun daga na sama har zuwa na kasa domin ganin an gyara baki daya”.

Wakilin mu Abba Isah Muhammad ya rawaito cewa, taron ya samu halartar masu lura da harkokin lafiya na jihar Kano da kuma masu rike da masarautun gargajiya harma da limamai.

 

 

Labarai

Gwamnatin tarayya ta ayyana gobe Laraba a matsayin ranar hutu

Published

on

Gwamnatin tarayya ta ayyana gobe Laraba, 1 ga watan Mayun 2024, a matsayin ranar hutu, domin bikin ranar ma’aikata na wannan shekara.

Ministan harkokin cikin gida, Olubunmi Tunji-Ojo, ne ya bayyana hakan, a cikin wata sanarwa da ya fitar a yau Talata.

Olubunmi, ya kuma sake nanata buƙatar ganin ma’aikata sun jajirce da yin aiki yadda ya kamata a dukkanib matakai daban-daban.

Continue Reading

Labarai

Wahalar Fetur ta haifar mana da koma baya a sana’ar mu – Mai Motar Haya

Published

on

Wani mai sana’ar tuƙin motar Haya, da kuma lodin fasinjoji mai suna Kabiru Muhammad, mazaunin ƙaramar hukumar Munjibir, ya ce ƙarancin motocin Haya da ake samu a yanzu, yana da alaƙa da wahalar man Fetur da ake fuskanta a sassan Najeriya.

A zantawar mutumin da wakilinmu Yusuf Nadabo Isma’il, ta cikin shirin rahotanni daga ƴan Zazu na yau Talata, ya ce a baya har motoci hamsin suke yiwa lodin fasinjoji su tashi, amma a yanzu Mota ɗaya suke iya cikawa sakamakon ƙarancin Fetur da ake fama da shi.

Ya kuma ce ƙaranci tare da tsadar man fetur ɗin da ake fama da shi, sun haddasa musu koma baya a sana’ar su, baya ga batun kuma matsalar da suke fuskanta da fasinjoji wajen biyan kuɗin Mota.

Wakiliyarmu da ta bibiyi shirin na ƴan Zazu Ummi Bala Ahmad ta rawaito cewa, matuƙin motar Kabiru Muhammad, ya kuma yi kira ga gwamnatin tarayya da ta jahohi, da su yi abinda ya kamata dan ganin farashin man Fetur ɗin ya sauka, domin al’umma su samun sauƙi.

Continue Reading

Labarai

Dilolin Wiwi sun yanki mai unguwa da Wuƙa, tare da cizon shi a hannu, kan ya shana su sha da siyar da wiwi a Kano

Published

on

Wasu matasa da ake zargin ƴan Daba ne, kuma dilolin Wiwi, sun kai wa mai unguwar yankin Bachirawar Tukwane ƙarshen kwalta hari da muggan makamai.

Tun farko dai mai unguwar yankin Malam Mustapha ya shawarci matasan ne, da su dai na ɗaurin tabar Wiwi, da siyar wa a kofar gidajen mutane lamarin da ya tunzura matasan.

Matasan dai sun rutsa mai unguwar Bachirawar ne inda suka yi yunƙurin hallaka shi, bayan da suka yanke shi da Wuƙa, tare da cizon sa a Hannu, sai dai ‘yan ƙungiyar bijilante na yankin sun kawo masa ɗauki inda suka kama wani matashi mai laƙabin Kokuwa.

A lokacin ne kuma mutanen yankin suka yi yunƙurin ɗaukar doka a hannu, sai dai mai unguwar Bachirawa Malam Mustapha dan Bachirawa Gabas Malam Abdulkadir Dandiyo, sun kuɓutar da matashin inda aka mika shi ofishin ƴan sanda, ragowar matasan suka tsere.

Shugaban kungiyar ci gaban al’ummar yankin Dakta Jibrin Sagir, ya ce a shirye suke su tinkari duk wani ɓata gari a yankin da yake addabar su.

Continue Reading

Trending