Connect with us

Labarai

Dola ne mu kare hakkin Jakuna a Kano- Hukumar hana fasa kauri

Published

on

Hukumar hana fasakauri (Custom) ta ce za ta dauki mataki mai tsauri kan masu yanka Jakuna domin fitar da fatarsu zuwa kasashen ketare.

Shugaban hukumar shiyar Kano da Jigawa, Ahmad Nasir ne, ya bayyana hakan lokacin da yake holin kayan da suka kama wanda suka hadar da Tumatirin Gwangwani, Maganin Sauro da kuma Fatar Jaki kimanin dubu takwas da dari da talatin da shida (8,136), wadanda kudin su ya kai fiye da miliyan Sittin da Biyar.

Da yake zantawa da manema labarai jiya Laraba, yayin kona fatar jakin, mai magana da yawun hukumar ta Kwastan a jihar Kano, Isah Dan Baba, ya ce “ Hukumar mu za ta yi duk mai yuwa wajen dakile ayyukan fasa kauri musamman ma fitar da fatar jaki da ake yi daga jihar Kano zuwa ketare, kuma hakan haramin ne a wurin mu sakamakon shi jaki ai ba a yanka shi sai dai a yi aiki da shi, kuma sauran kayayyakin da ake shigo da su tare da fitar da su ba bias ka’ida ba dukannin su a shirye mu ke da mu dakile tare da kwace su”.

A nasa bangaren shugaban kungiyar masu jimar Fata na Nijeriya, Lawan Sule Garo, yabawa hukumar hana fasa kaurin ta Kwastan ya yi tare da kira a garesu wajen kara sa idanu a cikin ayyukan sun a kare ‘yan Nijeriya daga bata gari.

Wakilin mu Abba Isah Muhammad, ya rawaito cewar hukumar ta Custom na jan hankali wajen kaucewa amfani da kayan da baNijeriya ce ta sarrafa su ba musamman maganin sauro mai dauke da rubutun China.

 

Labarai

Mahukunta ku kawo mana ɗauki a masallacin garin mu – Mazauna garin Ɗan-Dalama

Published

on

Al’ummar garin Ɗan-Dalama da ke ƙaramar hukumar Dawakin Tofa a jihar Kano, sun koka tare da neman ɗaukin mahukunta kan yadda katangar masallacin Juma’a na garin ta lalace, lamarin da hakan ke barazanar faɗuwar katangar.

Shugaban kwamitin masallacin juma’ar na garin Ɗan Dalama, Mallam Muhammad Mai Nama, ne ya magantu kan al’amarin, inda ya kuma yi kira ga al’umma ciki har da Attajirin ɗan kasuwar nan Alhaji Alhassan Aminu Ɗan Tata, da su kawo musu ɗauki domin gyara katangar masallacin na Ɗan Dalama, bisa yadda take neman faɗuwa.

Ya kuma ƙara da cewa ba iya katangar ce ke barazanar faɗuwar ba, haka ma cikin masallacin ba a cewa komai, duk kuwa da ƴan kwamitin sun yi bakin ƙokarin su, amma dai kawo yanzu akwai gyare-gyaren da ya ke buƙata.

Continue Reading

Labarai

Ba za’a iya wadata mutane da Fetur ba idan gwamnati ba ta sa hannu ba – Bashir Ɗan Mallam

Published

on

Yayin da ake ci gaba da fuskantar tsadar man fetur a ƙasar nan, shugaban kungiyar Dillalan Man fetur da Iskar Gas, ta ƙasa Bashir Ahmad Ɗan malam, ya ce koda kuwa matatar Mai ta Dangote za ta yi ƙarfi ka’in da na’in, ba lallai ne a samu saukin Man fetur ba a ƙasa, matuƙar gwamnatin tarayya bata sa hannu ba.

Bashir Ɗan Malam ya bayyana hakan ne yayin ganawarsa da gidan rediyon Dala FM, da safiyar yau Juma’ar.

Ɗan Mallam ya kuma ce sakamakon yadda gwamnati take taimakawa a fagen shan man, hakan yasa idan har bata sanya hannu ba za’a rinƙa shan wahala wajen samun man fetur ɗin a ƙasa.

Wannan dai na zuwa ne yayin da al’umma ke ci gaba da fuskantar ƙalubalen tsadar man fetur, lamarin da ya sa ake siyar da kowacce lita sama da Naira 800 a jihar Kano, inda ake ci gaba da fuskantar manyan layuka a gidajen man da dama.

Continue Reading

Labarai

Zamu yi aiki kafaɗa da kafaɗa da ƴan Jarida – Hukumar Zaɓe ta Kano

Published

on

Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta jihar Kano KANSEC, ta sha alwashin aiki kafaɗa-kafaɗa da ma’aikatan Jarida, musamman ma da zaɓen ƙananan hukumomin jihar nan 44 da ke tafe.

Sabon shugaban hukumar Farfesa Sani Lawan Manumfashi, ne ya bayyana hakan, yayin ziyarar da tawagar ƙuniyar matasan ƴan Jarida, ta Kano Youth Journalist Forum, suka kai masa a ofishin sa yau Alhamis, yayin da ya shafe kwanaki huɗu da kama aiki.

Ya kuma ce, za su yi aiki da ma’aikatan Jarida musamman ma yayin gudanar da ayyukan zaɓen ƙananan hukumomin Kano 44, da ke tafe, domin wayar da kan al’umma da ma samun nasara yayin zaɓen da ma bayan sa.

Farfesa Manumfashi, ya kuma ƙar da cewa, akwai buƙatar kowa ya bayar da tasa gudummawar a harkar zaɓe, domin kuwa yanzu haka suna ci gaba da aiki wajen shirya zaɓen ƙananan hukumomin.

Da yake nasa jawabin shugaban ƙungiyar matasa ƴan Jaridar ta jihar Kano Musa Zangina Adam, ya ce sun kai ziyarar ne, domin su ƙulla alaƙar aiki a tsakanin su da hukumar, bisa yadda kowanne ɓangare yake buƙatar juna, tare kuma da bayar da gudunmawar da ya kamata.

Zangina, ya kuma ce a shirye ƙungiyar su take wajen ci gaba da bibiyar al’amuran da suka shafi al’umma, tare da nusar da mahukunta dan ganin an wadata su da kayayyakin more rayuwa.

Continue Reading

Trending