Connect with us

Manyan Labarai

Ba’amurkiya da masoyin ta sun hada cinkoso a kasuwar Sabon Gari

Published

on

Masoyan biyu sun dai kai ziyara ne kasuwar Muhammdu Abubakar Rimi dake sabon Gari a jihar Kano a yau Alhamis domin yin siyayyar kayan auren na su.

Ba Amurka Janine Sanchez mai shekaru 46 da haihuwa yar asalin jihar Carlifonia dake can kasar ta Amurk wadda ta yi tsaiwar daka kan cewar sai ta auri Sulaiman Isah Panshekara mai shekaru 23 da haihuwa wanda suka hadu a shafin sada zumunta na instgarm, kuma abun mamakin shi ne duk kokarin da mahukunta da sauran al’umma ke yin a ankarar da shi Sulaiman din kan illar aurar baturiyar ta yi burus da kalubalantar da ake yi mata na biyo sahibin na ta har garin Panshekara dake karamar hukumar Kuimbotso a jihar Kano.

Sai dai kuma a yau dinnan kasuwar ta Sabon Gari ta na tsaka da ciki sai masoyan suka bayyana a kasuwar domin yin siyayyar kayayyakin auren su lamarin da ya dau hankalin yan kasuwar da masu siyayya wanda kallo ya koma kan su lamarin da ya janyo siyayyar ta gagare su saboda yan hoton selfie da masoyan biyu.

Sakamakon cincirindon al’ummar zuwa yanzu ba a iya kayyade iya adadin mutanen da suka nuna bukatar su domin daukar hoto da masoyan ba wanda ya janyo siyayyar kayan auren ta gagara sai kai musu kayan a kayi har ofishin sarkin kasuwar.

Mun kuma zanta da sakataren sarkin kasuwar ta sabon gari, Sulaiman Adamu Indabo wanda ya ce” Mune muka kai su ofishin mu domin yawon mutanen ya kai yawan das ba za a iya iyakance sub a saboda farin jinin masoyan da suke shirin angon cewa”.

Mun kuma yi kokarin jin ta bakin masoyan amma hakar mu bai cimma ruwa ba.

 

Manyan Labarai

APC ta dakatar da Dakta Abdullahi Ganduje daga jam’iyyar

Published

on

Jam’iyyar APC ta dakatar da tsohon gwamnan jihar Kano kuma shugaban jam’iyyar na kasa Dakta Abdullahi Umar Ganduje daga jam’iyyar.

Mai bai wa jam’iyyar shawara a ɓangaren shari’a a mazaɓar Ganduje, da ke ƙaramar hukumar Dawakin Tofa, Halliru Gwanzo, ya bayyana hakan ne a zantawar sa da manema labarai a jihar ta Kano, kamar yadda jaridar online ta Nigerian Triker ta rawaito.

Halliru Gwanzo, ya kuma ce sun ɗauki matakin dakatar da tsohon gwamnan Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ne sakamakon zarge-zargen da gwamnatin jihar Kano take masa a kan yin badaƙala da kuɗin al’ummar jahar.

Continue Reading

Manyan Labarai

Gwamnan Kano ya yi alƙawarin gyara titin garin Kundila da ke ƙaramar hukumar Shanono

Published

on

Gwamnatin jihar Kano ta yi alkawari gyara titin da ya taso daga babban titin karamar hukumar Shanono zuwa garin Kundila da ke karamar hukumar.

Gwamnan Kano Injiniya Abba Kabir Yusif, ne ya bayyana hakan yayin ta’aziyyar da ya kai na rasuwar ɗan majalisar dokokin jiha mai wakiltar ƙananan hukumomin Ɓagwai da Shanono Honorable Halilu Ibrahim Kundila.

Marigayin dai ya rasu ne a makon da ya gabata.

Gwamna Abba Kabir Yusif ya kuma bayyana kaɗuwar sa a lokacin da yaji rasuwar Marigayin, inda ya ce mutum ne mai gaskiya da rukon amana.

Wakilinmu na fadar gwamnatin jihar Kano Abba Haruna Idris ya rawaito cewa, Abba Kabir ya kuma ce gwamnatin Jihar Kano za ta dauki nauyin karatun iyalan mamacin daga inda suka tsaya har su kammala karatun nasu.

Continue Reading

Manyan Labarai

Fitacciyar Jarumar Kannywood Saratu Giɗaɗo (Daso) ta rasu

Published

on

Fitacciyar Jaruma a masana’antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood Saratu Gidaɗo wadda akafi sani da Daso, ta rasu a yau Talata.

Mijin ƙanwar marigayiya Daso, kuma mai baiwa gwamnan Kano shawara a kan harkokin tafiye-tafiye da shaƙatawa Mustapha Ibrahim Chidari, ne ya tabbatar wa wakilinmu Bashir Sharfaɗi rasuwar ta a ranar Talata.

Ya ce da Asubar yau tayi Sahur, ta koma Bacci, sai dai kuma zuwa wajen ƙarfe 10 na safe aka ga bata fito daga ɗakin ta ba, ko da aka shiga ɗakin ne aka tarar ta rasu.

Mustapha, ya ce za’a yi jana’izar ta da yammacin Talatar nan, da misalin ƙarfe 04:30 a gidanta dake Chiranchi cikin garin Kano.

Marigayiya Daso, guda ce daga cikin fitattun jarumai a masana’antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood, wadda ta shafe shekaru a masana’antar.

Continue Reading

Trending