Connect with us

Labarai

Ministan lafiya zai kawo ziyara asibitin AKTH

Published

on

Ministan ma’aikatar lafiya ta tarayyar Nijeriya, Osagie Emmanuel Ehanire, zai kawo ziyarar jaje ga asibitin koyarwa na Mallam Aminu Kano wato AKTH, sakamakon ballewar cutar zazzabin Lassa da a ka samu a asibitin har ta yi sanadiyar rasa rayukan wasu likitoci guda biyu Dr Habibu Musa da Kaltum Abba da kuma Dr Abdulkadir Abubakar wanda ya rasa ransa ta sanadiyar hadarin mota.

Ministan zai dai kawo ziyara ne a gobe Asabar 25 ga watan da muke ciki domin jajantawa asibitin da kuma al’ummar jihar Kano dama gwamnati baki daya.

A cikin wata sanarwa wadda ta fito daga asibitin na AKTH, ta ce haka zalika wata cibiya ta lafiya da kimiyar kayayyakin aiki ta Nijeriya ta bada tallafin wata na’ura guda biyu ga asibitin wadda za ta ke kula da aukuwar yaduwar cututtuka a cikin asibitin.

Da yake bayar da tallafin na’urorin biyu, Alhaji Sani Abubakar, ya ce”na’urorin suna da matukar amfani kuma nan da nan suke bayyana alamar yanayin mutum nan take da zarar an sami wata cuta a jikin sa.

Ya kuma mika sakon ta’aziyar sa ga iyalan mamatan sannan ya kuma yi addu’ar samun lafiya ga wadanda a ke zargin cutar ta Lassa ta kama.

Da yake karbar na’urorin, shugaban asibitin na AKTH, Farfesa Abdurrahman Aabba Sheshe, ya godewa kamfanin bias wannan na’urar da ya baiwa asibitin gudunmawar sa sannan ya kuma tabbatar da cewa za a saka na’urorin a dakin bada kulawar gaggawa da hatsari da kuma dakin karbar haihuwa.

Sannan ya kuma bukaci al’umma da su daina yada jita-jita akan yaduwar cutar ta Lassa kamar yadda a ke kozanta ta kuma ya ce jita-jitar ta nuna cewa marasa lafiya sun daina ziyarta asibitin sakamakon barkewar cutar ta Lassa wanda hakan sam maganar bah aka ta ke ba.

 

Labarai

Ƴan kasuwa ku tsaftace magudanan ruwa bisa gabatowar Damuna – Ƙungiyar Amata ta kasuwar Singa

Published

on

An buƙaci ƴan kasuwa da su rinƙa tsaftace tare da gyara magudanan ruwa a cikin kasuwannin su, bisa yadda damuna ke ƙara gabatowa.

Shugaban ƙungiyar Amata reshen kasuwar Singa Alhaji Musa Ibrahim Ɗan gaske, ne ya bukacin hakan a zantawar sa da manema labarai, yayin kaddamar da tsaftace kasuwar da kuma gyara mugudanun ruwan kasuwar.

Alhaji Musa, ya kuma ce ta hanyar tsaftace magudanan ruwan ne za a gujewa kowacce irin ambaliyar ruwa a cikin kasuwanni.

Continue Reading

Hangen Dala

Yau za’a fara Shari’ar Ganduje da gwamnatin Kano

Published

on

A yau ne babbar kotun jaha mai lamba 4 zata fara sauraron wata sharia wadda gwamnatin kano ta ahigar.

 

Gwamnatin jahar kano dai ta shigar da karar tsohon gwamnan jahar kano Dr Abdullahi Umar Ganduje da mai dakinsa Hafsat Umar Ganduje da kuma dansu Umar Abdullahi Ganduje da kuma wani kamfani mai suna Lamash da kuma Dr Jibrilla Muhammad.

 

Gwamnatin jahar kano dai tana zargin Ganduje da wadanna mutane da laifin hada baki da barnatar da dukiyoyin gwamnati.

 

 

Cikin zarge-zargen da ake yiwa su Ganduje akwai batun sun sayar da wasu filotai ba bisa ka’ida ba.

 

 

Da kuma batun zargin da akewa Ganduje na badakalar karbar dala tun a shekarar 2019.

 

 

Yanzu haka an girke jami,an tsaro a harabar sakateriyar Audu Bako inda kuma daga yanzu zuwa kowane lokaci kotun zata fara sauraron korafin kamar yadda wakilinmu Yusuf Nadabo Ismail ya rawaito

Continue Reading

Labarai

Ku tallafawa mazauna gidajen gyaran halin dan rage musu raɗaɗin rayuwa – Mallam Ibrahim Bunkure

Published

on

Limamin masallacin Salafussaleh dake unguwar Ɗorayi ƙarama a jihar Kano, Mallam Ibrahim Abdullahi Bunkure, ya shawarci al’umma da su ƙara dagewa wajen tallafawa mazauna gidajen ajiya da gyaran hali, da masu buƙata ta musamman, domin rage musu wani raɗaɗin rayuwa na yau da kullum.

Mallam Ibrahim Abdullahi Bunkure, ya bayyana hakan ne yayin da suka tallafawa mazauna gidan gyaran hali na Goron Dutse, da kayayyakin Abinci, da kuma na gidan yara, a wani ɓangare na taya su bikin ƙaramar Sallah, wajen ganin sun samu farin ciki a bukukuwan ƙaramar sallar da aka gudanar.

Ya ce matuƙar masu hali za su rinƙa tallafawa mazauna gidan gyaran halin da abubuwan da suka sawwaƙa, babu makawa za’a rage musu wata damuwa ta yau da kullum.

Wakilinmu Yakubu Ibrahim Dogarai ya rawaito cewa, Mallam Ibrahim Abdullahi Bunkure, ya ce daga cikin kayan abincin da suka kai wa mazauna gidajen akwai Tuwon Sallah, da garin Kwakwaki, da kuma sinadarin Ɗanɗano, da Sukari, domin ragewa mazaunan gidajen wani raɗaɗin rayuwa.

Continue Reading

Trending