Connect with us

Manyan Labarai

Hukuncin kisan da aka yankewa Maryam Sanda ya na karfafa shari’a- Human Right Watch

Published

on

Shugaban kungiyar kare hakkin dan Adam ta Human Right Watch Of Nigeria (HRWN), KaribuYahya Lawan Kabara, ya ce yankewa Maryam Sanda, hukuncin kisa bayan samun ta da laifin kashe mijinta ya nuna cigaban da harkokin Sahri’a ya samu a Nijeriya.

Karibu Yahya Lawan, ya bayyana hakan a ganawar sa da gidan redyiyon Dala Fm, lokacin da yake tsokaci kan hukuncin da kotun ta yankewa Maryam Sanda.

Ya kuma ce, “Hakika yanke matar hukuncin kisa ta hanyar rataya da kotun ta yi zai rage yawaitar kashe  aikata kisan kai tsakanin ma’aurata”.

Ya kuma kara dacewa,”Mu a bangaren mu na kungiyar kare hakkin dan Adam, hukuncin da kotun ta yankewa matar hakan yayi daidai, kuma zamu cigaba da sanya idanu musamman wajen ganin an zastarwa matar hukuncin kisa”. Inji Kabiru.

Wakilin mu Hassan Mamuda Ya’u yarawaito cewa, shugaban kungiyar Karibu Yahya Lawan Kabara,ya kuma shawarci ma’aurata da su kara sanya hakuri da tsoron Allah (S.W.T), a cikin zukatan su domin kaucewa fadawa halin da na sani.

 

 

 

 

Labarai

Rahoto: hukumar NDLEA na hukunta duk jami’in ta da ya yi laifi – Dakta Ibrahim Abdul

Published

on

Kwamandan hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi NDLEA, ta kasa reshen jihar Kano, Dakta Ibrahim Abdul ya ce, duk lokacin da ya samu daya daga cikin ma’aikatan su ya yi laifi, ya na hanzarin daukar matakin kora ko kuma hukuncin da ya dace.

Dakta Ibrahim Abdul ya bayyana hakan ne a zantawar sa da wakilin mu Abba Isah Muhammad, lokacin da yake mayar da martani a kan matasan da a ke zargin sun fada ruwan kududdufi lokacin da hukumar ta NDLEA ta kai simame yankin Dan Agundi da ke jihar Kano.

 

Domin jin cikakken rahoton saurari wannan

Continue Reading

Labarai

Rahoto: Matasa 2 sun gurfana a kotu kan zargin raunata jami’an KAROTA 3

Published

on

Kotu mai lamba 47, da ke rukunin kotunan majistret a unguwar Gyadi-gyadi, karkashin mai shari’a Huda Haruna Abdu, wasu matasa biyu Yunusa Sunusi da kuma Muhammad Babagana, sun gurfana a kotun da tuhumar a kan yi wa wasu jami’an hukumar KAROTA rotse, da suka hada da Usamatu Abdullahi da Sulaiman Musa da kuma Abdulkadir Isma’il.

Ana tuhumar matasan da laifuka guda uku, laifin hada baki da cin zarafi da kuma haddasa mummunan rauni, laifukan da suka saba da sashi na 93 da sashi na 264, sai kuma 247 na kundin laifuka, bayan kuma an karanta musu kunshin tuhumar zargin da a ke yi musu duk sun musanta.

 

Continue Reading

Labarai

Rahoto: Kotu ta fara sauraren shari’ar matar da a ke zargi da kazafin maita

Published

on

Wata mata ta gurfana a babbar kotun shari’ar musulunci da ke Kofar Kudu, karkashin mai shari’a Ibrahim Sarki Yola a kan zargin bin gari tana yada labarin cewa makwabciyarta da ‘ya’yanta duk mayu ne.

Tun da fari dai matar da a ke zargi da maitar, ta garzaya ofishin ‘yan sanda, tana karar makwabciyar tata, daga bisani kuma ‘yan sanda su ka tattara bayanai su ka mika su kotu domin fara sauraran shari’ar, bayan kuma karantawa matar mai yada labarin maita kunshin tuhumar ta musanta, inda kotu ta dage sauraren shari’ar.

Domin jin cikakken rahoton saurari wannan.

 

Continue Reading

Trending

error: Content is protected !!