Connect with us

Daurin Boye

Shirin Daurin Boye na ranar 28/12/2019 tare da Muzammil Ibrahim Yakasai

Published

on

A yi sauraro lafiya

Download Now

Daurin Boye

EFCC ta kwace fasfo din tsohuwar ministar jin kai

Published

on

Hukumar Yaki da Masu yi wa Tattalin Arzikin Kasa Zagon Kasa (EFCC), ta kwace fasfo din tsohuwar Ministar aJin-kai, Betta Edu da magabaciyarta, Sadiya Umar-Farouq, kan binciken badakalar da ake yi a ma’aikatar.

 

Wata majiya mai tushe daga EFCC ta ce an kwace fasfo din Edu da da Sadiya ne domin hana su fita daga Najeriya yayin da ake ci gaba da binciken.

Hukumar ta kwace fasfo din tsofaffin ministocin biyu, Sadiya Umar-Farouq da Betta Edu.

“Mun kuma kwace fasfo din Halima Shehu har sai an kammala bincike. Hukumar ba ta son yin kasadar ganin ko daya daga cikinsu ya fice daga Najeriya alhalin ana bincike a kan su,” in ji majiyar.

Dangane da binciken Edu da Sadiya Umar-Farouq, EFCC ta gayyaci shugabannin bankunan Zenith, Providus da Jaiz ofishinta a ranar Talata.

Ita ma Halima Shehu, wacce aka dakatar daga hukumar kula da harkokin zuba jari ta kasa, EFCC na bincike a kan ta.

Continue Reading

Daurin Boye

Muna da wadataccen Mai – NNPCL

Published

on

Kamfanin man fetur na Najeriya, NNPCL, ya gargadi jama’ar kasar da su kiyayi sayen mai suna adanawa, don tsoron fuskantar karanci da karin farashin man.

 

Wannan gargadi ya biyo bayan karuwar jerin motoci ne a gidajen mai a sassan kasar a ‘yan kwanakin nan.

 

NNPC Limited, ya ce yin gargadin ya zama wajibi, bisa la’akari da yadda aka fara ganin layukan ababen hawa a gidajen mai a birnin Ikko, cibiyar kasuwancin kasar, da birnin tarayya Abuja da dai sauran wasu garuruwa na Najeriyar.

 

Wata sanarwa da kamfanin man ya fitar, ta ba wa ‘yan Najeriya tabbaci, cewa an gano bakin zaren dangane da abin da ya haddasa layukan ababen hawa a gidajen man.

 

NNPCL, ya ce abin da ya janyo wannan matsala shi ne raguwar dakon man daga ma’ajiyarsa da ke Apapa a birnin Ikko, wato Legas.

 

Amma yanzu haka akwai isasshen mai a adane, wanda aka yi amanna za a kwashe tsawon kwana talatin ana amfani da shi a kasar, kamar yadda sanarwar ta bayyana.

 

Saboda haka, kamfanin man na Najeriya ya yi gargadin cewa, jama’a su guji sayen man suna adanawa, bisa tsoron za a yi fama da karancinsa.

 

NNPCL, ya ce, nan da ‘yan kwanaki kadan komai zai daidaita game da safararsa zuwa sassan kasar.

 

Ana fatan wannan sanarwa da kamfanin man ya bayar, za ta kwantar wa jama’ar kasar hankali, ta kuma kawar da duk wata fargabar da ake yi, cewa mai yiwuwa an hau hanyar fama da karancin man, ko kuma an fara take-taken da za a kara farashinsa.

Continue Reading

Daurin Boye

Yar wasan Arsenal ta zama gwarzuwar shekara

Published

on

Yar wasan kwallon kafa ta kasar Netherland kuma yar wasan gaban kungiyar kwallon kafa ta Arsenal, Vivianne Miedema ta lashe yar wasan gwarzuwar shekara ta mata.

Vivianne mai shekaru 23 ta dai samu wannan kyautar ne yayin da kungiyar marubuta labarin wasanni ta mata ta karrama ta da lambar yabo.

Yar wasan ta doke yar wasan kungiyar Chelsea ta mata Bethany yar kasar Ingila a wannan shekarar.

Vivianne Miedema

A kakar 2019/20 Miedema ta zama ja gaba gasar mata ta Super League a matsayin wadda tafi zura kwallo 16 a kakar.

Sannan ta zama yar wasa da tafi zura kwallo a kasar ta wadda ta tallafa mata ta kai banten ta zuwa wasan karshe na gasar cin kofin duniya ta mata. Kuma it ace yar wasa ta uku da ta taba lashe kyautar bayan da Nikita Parris da kuma Fran Kirbysu ka lashe kyautar a shekarar 2018 da 2019.

 

Continue Reading

Trending