Connect with us

Lafiya

Limamai sun magantu a kan cutar Lassa

Published

on

Limamain masallacin juma’a na masjudul Quba dake unguwar Tukuntawa a yankin karamar hukumar birni a jihar Kano, malam Ibrahim Abubakar Tofa ya bayyana cewa tuntuni addinin musulinci ya dade da bayyana muhimmancin tsafta da kuma kashe Beraye domin tsira da lafiya da kuma kaucewa kamuwa da cututtuka.

Malam Ibrahim Abubakar Tofa ya bayyana hakanne ta cikin hudubar juma’a daya gabatar yau a masallacin.

Ya kuma ce rashin kiyaye dokin musulinci ta hanyar yawaita ayyukan sabo da rashin tsafta wadda takan kawo Berayen na daga cikin abubuwan da suka kawo annobar cutar zazzabin Lassa da a ke fama da ita a halin yanzu.

Shima a hudubar sa ta yau Limamin masallaci juma’a a dake shelkwatar rundanar ‘yan sanda shiya ta daya wato zone one a jihar Kano, SP Muhammad Kabir Abubakar, ya ce” Ya zama dole jama’a su bi matakin kariya daga cututtuka musanman zazzabin Lassa da ya shigo jihar Kano. Cikin hanyoyin kubuta daga cutar lassa akwai wanke hannaye da kuma kula da abincin da mutin ya ke ci yazama, dole mutsaftace muzibin abincin mu sannan kuma abincin ya zama koda yau she ya na rufe”.

Limamin ya kuma ce al’umma su dai na tara shirgi da ysunmokara barkatai a cikin gida domin hakan na baiwa Berayen mafaka.

 

 

 

Lafiya

An ƙaddamar da aikin gwaje-gwajen lafiya da bayar da magani kyauta a Kano

Published

on

Ƙungiyar ma’aikatan lafiya da unguwar zoma ta ƙasa reshen asibitin Ƙashi na Dala a jihar Kano, ta ƙaddamar da aikin gwaje-gwajen lafiya da bayar da magani kyauta ga al’umma.

Shugaban ƙungiyar ma’aikatan lafiya na asibitin Ƙashi na Dala, Kwamared Abubakar Muhammad Isah, ne ya bayyana hakan a wani ɓangaren na tunawa da bikin ranar ma’aikatan jinya ta Duniya, wanda a nan Kano za’a shafe mako guda ana gudanar wa a jihar Kano.

Kwamared Abubakar Muhammad, ya kuma ce sun zaɓi gwaje-gwajen lafiya da bayar da magani kyauta, domin saukakawa al’umma.

A cewar sa, “Mutane ku rinƙa zuwa Asibiti ana gwada lafiyar ku ba sai baku da lafiya za ku je gwaji ba domin mai lafiya shine yake neman magani dan ya yi rigakafi, amma da zarar cuta ta ci karfin mutum to lamarin ya yi munin gaske, “in ji shi”.

Wakilinmu Yusuf Nadabo ya ruwaito cewar kungiyar za ta kwashe mako guda tana gudanar da taruka dan wayar da kan al’umma a kan batun lafiya.

Continue Reading

Lafiya

Ku rinƙa ziyartar Asibiti ana muku gwaje-gwajen fitsari da Jini domin sanin halin da ƙodar ku take ciki – Likita

Published

on

An shawarci al’umma da su rinƙa ziyartar Asibiti akai akai wajen duba lafiyar su, ta hanyar yin gwaje-gwajen fitsari da jini domin sanin halin da kodar su ke ciki.

Dakta Muhajid Sunusi Rabi’u ne ya bayyyana hakan yayin ganawarsa da Dala FM, lokacin da suke aikin gwaje-gwajen fitsari da jini, kyauta a ɗaya daga cikin makarantu masu zaman kan su a nan Kano.

Dakta Mujaheed ya kuma ce sun gudanar da aikin ne a wani ɓangare na bikin ranar ƙoda ta Duniya, wadda aka ware duk ranar Alhamis ta mako na biyu na kowanne watan Maris domin gudanar da bikin ranar.

Continue Reading

Lafiya

Za’a yiwa kusan yara miliyan 3 rigakafin cutar shan Inna a Kano

Published

on

Gwamnatin jihar Kano tace kusan Yara miliyan 3 za’ayiwa rigakafin cutar shan inna a kananan hukumomin jihar nan 44, duba da samun ɓurɓushinta da kaso 65, a jihar ta Kano.

Kwamishinan lafiya na jihar Kano Dakta Abubakar Labaran Yusuf ne ya bayyana hakan yayin ƙaddamar da rigakafin cutar shan innar a yau Alhamis, wanda za’a kwashe kwanaki 4 ana gudanarwa a Kano.

Dakta Abubakar Labaran ya ce duba da shigowar zafin akwai buƙatar al’umma su kula da alamomin cutar sankarau, duk da gwamnati ta yi shirin bayar da agajin gaggawa, kamar yadda tashar Dala FM Kano ta rawaito.

Ma’aikatar lafiyar ta jihar Kano dai ta ce za’a ci gaba da gudanar da sauran rigafin, domin bai wa yaran jihar Kano kariya daga cututtuka masu yaɗuwa.

Continue Reading

Trending