Labarai
Ba zamu lamunci tallata sirrin mu a duniya ba- Jami’ar Wudil

Kungiyar tsofaffin shugabanin kungyar dalibai jami’ar kimiyya da fasaha ta wudil K.U.S.T, sun bayyana rashin jindadin su kan yadda kungiyoyi a jami’ar su ke tallata sirrin ta a duniya maimakon bin hanyoyin da suka kamata na ciki domin warware matsalar.
Sanarwar mai dauke da sa hannun sakataren kungiyar, Kwamared Said Ibrahim, ta rawaito cewa kungiyar ta ce fitar da sirrin jami’ar, tun gabanin bin matakan cikin gida, abu ne da zai zubar da kimar makarantar a idon duniya, ta kuma ce darajar daliban ta a halin yanzu dama wadanda ta yaye baya.
Sanarawar ta kuma bukaci dukannin wasu kungiyoyin jami’ar da suka hadar da ta manyan malaman jami’ar (ASUU) da kuma ta dalibai harma da duka sauran kungiyoyin da suke da alaka da jami’ar da a koda a yaushe su fara da bin matakan cikin gida da domin warware kowacce irin matsala gabanin fitar da ita a kafafan yada labarai.

Labarai
Cutar mashako ta bulla a wasu sassan Jigawa

Akalla mutum goma ne suka mutu bayan ɓarkewar cutar mashaƙo a kananan hukumomi 14 na jihar Jigawa.
Ma’aikatar Lafiyar jihar ce ta sanar wa manema labarai haka a Dutse, a yau Lahadi. Ta ce ana kuma zargin cewa mutum 91 sun kamu da cutar.
Babban sakatare a ma’aikatar, Dr Salisu, Mu’azu, ya ce zuwa yanzu, an tabbatar da mutum biyu da suka kamu da cutar a kananan hukumomin Kazaure da Jahun yayin da aka Ɗauki jinin wasu zuwa Abuja domin yin gwaji da tantancewa.
Mu’azu ya ce ɓarkewar cutar abin damuwa ne musamman ma ganin cewa ta ɓulla a yankunan da ba su taɓa yin riga-kafin ta ba.
A cewarsa, tuni ma’aikatar ta fara bincike domin tattaro bayanai daga yankunan da abin ya shafa.
Ya ce gwamnatin jihar tuni ta fara shiri don yin riga-kafi a yankunan domin kaucewa yaɗuwar cutar.

Hangen Dala
Hukuncin kotu:- Zamu daukaka Kara – Abba Gida Gida

Gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf yace zasu ɗauki matakin ɗaukaka ƙara zuwa gaba domin tabbatar da adalci kan hukuncin da kotun sauraron korafe-korafen zabe ta yanke inda ta ayyana Alhaji Nasiru Yusuf Gawuna a matsayin wanda ya lashe zaben Gwamnan da aka gabatar a watan Maris din 2023.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayyana hakan ne yayin wani taron manema labarai da ya gudana a fadar gwamnatin Kano a daren laraba.
Gwamnan ya ƙara da cewa sun umarci lauyoyin su da su hanzarta wajen ɗaukaka ƙara ba tare da ɓata lokaci ba.
Ka zalika ya kuma ce wannan hukuncin bazai sanyar musu da gwiwa ba wajen ci gaba da gudanar da ayyukan da suka fara.
A ranar Laraba ne dai 20 ga watan Satumba 2023 kotun sauraron korafe-korafen zabe ta tabbatar da Nasiru Gawuna a matsayin Wanda ya lashe zaben Gwamnan Kano da aka gabatar a watan Maris. (more…)

Hangen Dala
Hukuncin zaben Kano:- An Kori ‘yan Jarida daga harabar kotu

Jami’an Ƴan Sanda sun hana ƴan Jarida shiga harabar Kotun Sauraron Ƙararrakin Zaɓe ta Kano.
Duk da asubanci da ƴan jarida suka yi, jami’an ƴan sanda sun yi ƙememe sun hana su shiga.
Ƴan sandan sun koro wakilan kafafen yaɗa labarai da dama zuwa can nesa da Kotun.
A yau ne dai za’a Yanke hukunci Kan karar da jam’iyyar APC ta shigar gaban kotun tana kalubalantar nasarar Gwamnan Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf.
Ƙarin bayani na tafe.

-
Nishadi4 years ago
Ina neman mijin aure – Rayya
-
Manyan Labarai4 years ago
KAROTA: An baiwa Baffa Babba wa’adin kwanaki bakwai
-
Labarai3 years ago
Hamisu Breaker ya kai kan sa wajen ‘yan sanda
-
Nishadi4 years ago
Mansura Isah ta yi kaca-kaca da Sadiya Haruna
-
Labarai4 years ago
Auren dan Panshekara da ba Amurkiya ya samu cikas
-
Lafiya1 year ago
Rahoto: An gano wani gida da ake gini da takardun Kur’ani da Alluna
-
Nishadi4 years ago
An gano daliban da Adam Zango ya dauki nauyin karatun su
-
Manyan Labarai4 years ago
Sabuwar damfarar da ta fito a Kano