Connect with us

Manyan Labarai

Sabuwar damfarar da ta fito a Kano

Published

on

Kwamandan ‘yan sinitir na Bigilante a karamar hukumar Birni, Idris Adamu Sharada, ya ja hankalin masu sana’ar sayar da Gawayi a karamar hukumar, da su yi taka tsantsan da wani sabon salon damfara da wadan su ba ta gari su ke yiwa masu sana’ar gawayin.

Idris Adamu Sharada ya yi jan hankalin ne, a lokacin da su ka samu nasarar kama daya daga cikin wadanda a ke zargi da irin wannan damfarar, ta hanyar zuwa da mota a loda musu gawayin da sunan za su sauke, su kuma dawo su kara sannan kuma su biya kudin gaba daya.

Ya kuma ce” Sun dade suna bibiyar mutanen sakamakon korafe-korafen da al’umma suke yi a kansu, inda a wannan lokacin suka samu nasarar kama daya daga cikin su. Mun samu rahoton cewa wanda a ke zargin ya karbi buhun Gawayin masu tarin yawa daga wurin mutane daban-daban”.

Wakilin mu Aminu Ahmad Abbas, ya rawaito cewa yanzu hakan  wanda ake zargin ya na hannun jami’an tsaro domin fadada buncike da kuma daukar mataki na gaba.

 

Labarai

Lokacin zaɓe: Rundunar ƴan sanda ta shirya daƙile tayar da tarzoma – SP Kiyawa

Published

on

Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta ce, ta shirya wajen samar da tsaro, tare da ɗaukar matakin da ya dace ga ɓata garin da suke shirin tayar da tarzoma.

Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ƴan sandan jihar Kano SP Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya bayyana hakan ga Wakilinmu Hassan Mamuda Ya’u a yau juma’a, yayin da yake tsokaci kan shirin da rundunar su ta yi kan zaɓe.

Continue Reading

Labarai

Al’umma da su dage da addu’a a lokacin da za su fita zaɓen gwamna da na ƴan majalisa – Malam Ali Ɗan Abba

Published

on

Gamayyar rukunin wasu Limamai da Malaman jihar Kano sun buƙaci al’umma da su dage da yin addu’a musamman ma a lokacin da zasu fita zaɓen gwamna da na ƴan majalisar jiha, domin hakan zai taimaka wajen yin zaɓen cikin kwanciyar hankali da lumana.

Shugaban magayyar limamai da malaman da suka fito daga Ɗariyar Tijjaniyya, Kaɗiriyya da Izala, da kuma Mahaddata Alƙur’ani mai girma na Kano Malam Ali Ɗan Abba ne ya bayyana hakan, yayin wani taron zaman lafiya da suka gudanar a ranar Alhamis.

Malam Ali Ɗan Abba, ya kuma shawarci al’umma da su gujewa tayar da tarzoma a yayin zaɓen, domin zama lafiya yafi komai mahimmanci a rayuwa.

Ya kuma ce kamata yayi suma malamai su ƙara dagewa da yin addu’in da suke yi, domin samun shugabanni na gari da za su yiwa al’umma adalci.

Continue Reading

Labarai

Hukumar KAROTA ta cafke mota ƙirar Tirela maƙare da Giya

Published

on

Hukumar Kula da Zirga-Zirga ababen hawa ta jihar Kano, KAROTA ta cafke mota ƙirar Tirela maƙare da Giya, a kan titin zuwa gidan Rediyon Kano, lokacin da Direban motar ke yunƙurin wucewa cikin Sabon gari, a daren Laraba.

Bayan da aka cafke motar, direban ya tsere tare da barin motar, wadda Jami’an hukumar KAROTA suka fuskanci barazana daga wasu jami’an sojoji waɗanda suka rako motar, domin tilasta musu sakin motar.

Daga bisani kuma suka ci gaba da lallabar jami’an da su rabu da motar tare da yi musu alƙawarin basu na-Goro

Hukumar ta KAROTA ta c,e zata miƙa Giyar ga Hukumar Hizba, domin ɗaukar mataki na gaba da zarar ta kammala bincike.

Continue Reading

Trending