Connect with us

Manyan Labarai

Cin ‘ya’yan itatuwa na maganin cutar Kansa- Dakta Abdulmalik

Published

on

Wani likita dake Asibitin koyarwa na Malam Aminu Kano, Dakta Abdulmalik Yakubu ya ce, cutar Kansa cuta ce wacce ke shafar wasu bangarori na jiki da suka shafi Fata, Tantani da sauransu.

Dakta Abdulmalik, ya bayyana hakkan ne a zantawarsa da gidan rediyon Dala a yau Talata, a yayin bikin ranar cutar Kansa ta Duniya da majalisar Dinkin Duniya ta ware duk ranar 4 ga watan Fabrairun ko wacce Shekara.

Yana mai cewa, “Abubuwan da su ke kawo cutar Kansa sun hada da amfani da maganin Bature ba tare da shawarar masana ba, ko shan wata guba da kuma tarin shekaru.”              

Dakta Abdulmalik, ya kara da cewa, “Akwai hanyoyin da za’a bi dan kare kai daga kamuwa da cuta, da suka hadar da cin abinci mai inganci, da ‘ya’yan itatuwa.”                        

Wakilinmu Abdulkadir Muhammad Sani, ya rawaito cewa, likitan ya ce, masu dauke da cutar na iya warkewa matukar an bi tsarin da likitoci suka  zayyana.

 

 

Labarai

Marayu da marasa galihu na bukatar taimakon al’umma – Limami

Published

on

Wani malamin Addinin musulunci a jihar Kano ya bukaci al’umma da su dage wajen taimakawa marayu da marasa galihu dake cikin al’umma.

Limamin masallacin juma’a na Bilal Bn Rabah da ke garin Taura a Jihar Jigawa Dakta Isah Salisu Yaro ne ya bayyana haka jim kadan bayan kammala bude sabon masallacin juma’a na Shu’aibu Ali, dake Unguwar Ayagi a cikin karamar hukumar Dala a nan Kano.

Ya ce, “Taimakawa addini abu ne da al’ummar musulmi ya kamata su rinka a ko da yaushe”. Inji Dakta Isah Salihu.

A na sa jawabin limamin masallacin Ustaz Kabiru Sani Salihu, kira ya yi ga al’umma da su zama masu yawan godiya ga Allah (S.W.T) a kan ni’imar da ya yi wa bayin sa.

Continue Reading

Labarai

Rahoto: A guji amfani da matasa domin tayar da rigima a wajen zabe – Limami

Published

on

Limamin masallacin juma’a na Shelkwatar rundunar ‘yan sanda da ke Bompai SP Abdulkadir Haruna ya bukaci shugabanni da su guji amfani da matasa wajen tayar da hankalin al’umma a wajen zabe.

SP Abdulkadir Haruna ya bayyana hakan ne jim kadan bayan idar da sallar Juma’a, yayin da ya ke yiwa wakilin mu Abba Isah Muhammad Karin gaske akan abinda hudubar ta kunsa.

Domin jin cikakken rahoton saurari wannan.

Continue Reading

Labarai

Ya zama wajibi mu rinka yiwa tsofaffin sojoji addu’a – Ganduje

Published

on

Gwamnan Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje ya ce ya zama wajibi a rika yiwa tsoffin sojoji addu’a saboda  sadaukar da rayuwar su wajen tabbatar da ci gaban kasar su.

Gwamna Dr Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana hakan ne a ranar Juma’a yayin bikin tunawa da tsoffin sojojin da suka hidimtawa kasa.

Ya ce, “Da dama daga cikin tsoffin sojoji sun rasa rayuwar su ne wajen ganin kasar nan  ta zauna lafiya da kwantar da tarzoma adon haka ya zama lallai a rika tunawa dasu da Yi musu addu’a”. A cewar Ganduje.

Wakiliyar mu Zahrau Nasir ta rawaito cewa, an gudanar da faretin tunawa da tsoffin sojojin yayin taron.

Continue Reading

Trending

error: Content is protected !!